2023: Yayin Da Gwamnonin APC Suka Yi Fatali Da Tsarin Karba-karba…

Eid-el-kabir

kungiyar gwamnoni karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki ta yi watsi da tsarin karba-karba wajen tsayawa takara a cikin jam’iyyar a zaban shekarar 2023.

Sakamakon kara karatowar babban zabe mai zuwa, kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC ta bayyana cewa, kowa zai iya tsayawa takarar kowani matsayi na siyasa a karkashin jam’iyyar a cikin kasar nan, bisa la’akari da dokokin jam’iyya da kuma tsarin mulki ta shekarar 1999 na Tarayyar Nijeriya wanda aka yi wa garanbawul.

Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC kuma gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu shi ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi game da canza shekar gwamnan Jihar Kuros Ribas, Ben Ayade daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Ya bayyana cewa, jam’iyyar mai mulki a bude take gudanar da al’amuranta, sannan kuma za ta ci gaba da gudanar da tsaftataccen siyasa wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari yake kokari a kai bisa bin tsarin shugabannin jam’iyyar.

“Shugaban ruko na jam’iyyar na kasa yana aiki tukuru wajen dawo da tsarin siyasa jam’iyyar APC a matsayinta na jam’iyya mai karfi take gina dimokaradiyya a Nijeriya. Za mu ci gaba da mara wa shugaban jam’iyyar na kasa baya wajen gudanar da wannan kokarin da yake yi a wannan babbar jam’iyya namu. Shigar Mista Ayade cikin wannan jam’iyyar tamu ya nuna irin ci gaban da ‘yan Nijeriya ke samu, wanda zai kara wa jam’iyyar karfi.

“Jam’iyyar APC na ‘yan Nijeriya ne gabaki daya. Kowani mutum da ke kowacce bangare yana iya tsayawa takaran a karkashin jam’iyyar, kamar yadda dokokin jam’iyyar da tsarin mulkin tarayyar Nijeriya na shekarar 1999 wanda aka yi wa garanbawul suka tanada. Tsarin manufofin jam’iyyar ya ta’allaka ne bisa tattalin arziki da zamantakewa da bunkasa siyasar Nijeriya.

“Jam’iyyarmu za ta ci gaba da habaka. Za mu ci gaba da samun shigar mutane masu mahimmanci cikin ma’iyyarmu ta APC,” in ji shi.

Wasu magoya bayan jam’iyyar suna ganin wannan kalamai ya ci karo da abin da shugabannin jam’iyyar suka kulla na bai wa yankin Kudancin kasar nan takara a zaben shekarar 2023.

Da yake zantawa da manema labarai, tsohon shugaban jam’iyyar APC, Cif John Odigie-Oye ya bayyana cewa, tsarin karba-karba ba shi ba ne matsala, matsalar dai ita ce tun daga lokacin da aka fara gudanar da siyasa ba ana bin tsarin karba-karba ko da kuwa a kananan hukumomi ko a gundumonin da mutane da yaruka iri daya da addini daya.

“Ba a iya kauce wa tsarin karba-karba saboda akwai yankuna daban-daban a gundumomi ko a kananan hukumomi da ke da mabambantan ra’ayoyi da bukatu, wanda mulki ba zai iya zama a wuri daya ba ko da kuwa akwai mutanen da suka fi cancanta.

“Domin haka, tsarin karba-karba ba abu ba ne da za a yi watsi da shi, domin yana nan a ko’ina a duniya. A wasu yankunan ya yi karanci, amma dai yana nan.”
Shi ma wani jigon jam’iyyar a Jihar Inugu, Osita Okechukwu ya bayyana cewa, “ina murna da cewa gwamnonin jam’iyyarmu sun yi magana da murya daya, wannan ba karamin ci gaba ba ne. Mun ji abin da kungiyar gwamnominmu suka fadi wanda zai bai wa duk wani dan jam’iyyar damar tsayawa takarar shugabancin kasa.

“Wannan shi ne tsarin dokokin jam’iyyarmu mai girma. A zaban fidda gwani na shugaban kasa da ya gudana a shekarar 2020, an samu matsaloli masu yawa game da tsarin karba-karba, musamman a yankin Kudu.”
Gwamnonin jam’iyyar APC sun yaba da hukuncin da gwamna Ayade ya dauka bisa irin shugabancin da shugaban jam’iyyar na kasa kuma gwamnan Jihar Yobe, Mallam Mai Mala Buni da kuma Muhammadu Buhari suke gudanarwa zai kara bai wa ‘yan Nijeriya masu yawa sha’awar shiga cikin jam’iyyar.

“kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC ta yi maraba da shigowar mai girma gwamnan Jihar Kurus Ribas, Mista Ben Ayade zuwa cikin jam’iyyar APC. Dukkan shugabannin jam’iyyar da mambobi suna yi maka barka da shiga cikin wannan jam’iyyar tamu. Shawarar da Mista Ayade ya yanke na shiga cikin jam’iyyar APC ya nuna irin ayyukan da jam’iyyar ke gudanarwa wajen hada kan dukkan ‘yan Nijeriya kamar yadda magabata suka daura jam’iyyar a kai. Shigowar Mista Ayade cikin jam’iyyar APC hanya ce da za a kara samun mambobi da shugabanni a cikin jam’iyyar a kowani mataki.

“Muna taya murna ga shugabanninmu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari wadanda suka yi tsayin daka wajen tallata jam’iyyar a wajen ‘yan Nijeriya. Shugaban kasa mutum ne da bai nuna bambamci wanda ya daga darajar jam’iyyarmu a matsayin hanyar da ya sa aka zabi jam’iyyar. A matsayinmu na gwamnoni jam’iyyar APC za mu ci gaba da bai wa shugaban kasa goyar baya wajen gina jam’iyyarmu ta APC, domin ta ci gaba da kara karfi a cikin kasar nan.

“Haka kuma muna jinjina wa shugaban ruko na jam’iyyar APC na kasa, Mai Mala Buni wajen kokarinsa na samar da nasarori a cikin jam’iyyar, domin bisa kokarin da ya yi ne har ya sa gwamna Ben Ayade shiga cikin jam’iyyar APC.
“Muna wa Mista Ben Ayade maraba na yanke hukuncin barin jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC. Wannan ba karamin ci gaba zai kawowa jam’iyyar APC ba na sake kara bunkasa kasar nan.

“Bisa irin nasarorin da Mista Ayade ya samu a cikin Jihar Kurus Ribas ya zo gidan da ya dace da shi. Jam’iyyar APC za ta samar masa mutane a dukkan fadin Nijeriya da zai samu nasarar cimma burikansa na siyasa ta hanyar tattaunawa da su. Tare da Mista Ayade da dukkan shugabannin jam’iyyar APC, jam’iyyar za ta hada hannu da dukkan ‘yan Nijeriya wajen samar da wakilai nagari a cikin kasar nan.”
Sai dai kuma, a yayin da ra’ayoyi suka bambanta a cikin jam’iyyar game da tsarin karba-karba a 2023, ke nan ina hankali zai fi karkata ne a jam’iyyar?

Exit mobile version