• English
  • Business News
Saturday, October 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: Zan Ware Dala Biliyan 10 Don Inganta Rayuwar Matasa —Atiku

by Sulaiman
3 years ago
Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin cewa idan ya yi nasara a zaɓen 2023, gwamnatin sa za ta ware dala biliyan 10 don bunƙasa rayuwar mata, samar da ayyuka, ƙanana da matsakaitan masana’antu da sana’o’i.

Ya ce waɗannan zunzurutun kuɗaɗen za su kuma yi amfani wajen tallafa wa mata da matasa kaiwa ga matakan nasarar da su ke ta hanƙoron ganin sun cimma burin kaiwa.

  • Tinubu Ya Bukaci Manyan Masu Kalubalantarsa Atiku Da Obi Da Su Janye Daga Takara

Atiku ya sha wannan alwashin a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, lokacin da ya je yaƙin neman zaɓe a can.

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

Atiku wanda ya yi mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007, ya ɗora laifin matsalar tsaro a kan gwamnatin APC.

Atiku

Ya ce gwamnatin Buhari ta gaza kuma ta yaudari ‘yan Najeriya a fannin tsaro da ayyukan gina ƙasa.

Da ya ke taya Jihar Kwara nuna damuwar sa kan matsalolin jihar, Atiku ya nuna takaicin duk da jihar Kwara ce mahaɗar Arewa da Kudu, amma ba ta da hanyoyi masu kyau.

Shi kuwa Shugaban PDP Iyorchia Ayu, cewa ya yi “jam’iyyar PDP babban gida ne wanda kawunan dukkan iyalan gidan a haɗe su ke. Mu na kan hanyar kaiwa ga nasara.

“PDP za ta dawo ta ceci Nijeriya, ta maida ta kan turbar bunƙasa da ceton kowane iyali.”

Atiku

“Kada ku bari wasu su yaudare ku, yunwar da ta yi mana katutu a yanzu ta nunka wadda mu ka sha a 2015. Kowa ya fito da katin zaɓen sa ku zaɓi PDP, ku zaɓi ɗan takarar ta Atiku Abubakar a zaɓen 2023,” inji Ayu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027
Siyasa

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

October 17, 2025
Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu
Siyasa

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

October 16, 2025
Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson
Manyan Labarai

Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson

October 16, 2025
Next Post
Babban Editan Jaridar LEADERSHIP, Azu Ishiekwene, ya Lashe Lambar Yabo Ta Zama Gwarzon Shekara

Babban Editan Jaridar LEADERSHIP, Azu Ishiekwene, Ya Lashe Kyautar Zama Gwarzon Shekara

LABARAI MASU NASABA

Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

October 18, 2025
Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

October 18, 2025
Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

October 18, 2025
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

October 18, 2025
Radda

Gwamnan Katsina Ya Bukaci Al’umma Su Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro

October 18, 2025
Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi

Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi

October 18, 2025
IMF

Fitar Da Kudi Ta Haramtacciyar Hanya Na Kara Dagula Matsalar Tattalin Arziki – IMF

October 18, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Gayyaci CBN Da Bankuna Kan Cire Wa Kwastomomi Kudi Ba Dalili

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.