• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: An Yi Kira Ga Masu Mulki Da Su Rungumi Tafarkin Inganta Rayuwar Al’umma

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
5 months ago
vector illustration of Nigeria flag and map

vector illustration of Nigeria flag and map

Masana sun ce maimakon su rika maida hankalinsu kan yadda Nijeriya za ta koma kan tafarkinta kamar yadda aka dade da saninta, mai tarkin jam’iyya daya, an yi kira da su ‘yan siyasa su maida hankalinsu kan yadda za su yi maganin matsananciyar fatara wadda take damun ‘yan Nijeriya.

Hakanan ma an yi kira da su maida hankalinsu yadda za ayi maganin matsalolin tsaro da sauran matsalolin wadanda suke damun Nijeriya.

  • Tottenham Ta Raba Gari Da Kocinta Ange Postecoglu
  • Dangote Ya Sanya Wa Hanya Sunan Tinubu, Zai Kashe Naira Biliyan 900 Don Gina Hanyoyi A Nijeriya

Wadannan shawarwarin sun fito ne daga manyan Lauyoyi na kasa da masana harkokin siyasa wadanda suka yi tunani kan damuwarsu ta yadda Nijeriya za ta kasance kasa mai amfani da tafarkin jam’iyyar siyasa daya, suka ce duk da abin ba wani aikata laifi bane sai dai halin da ake ciki yanzu yana da kamar wuya.

Sun ce yadda abubuwa suke tafiya da irin halin da su ‘yan siyasar suke zai sa lamarin tafarkin jam’iyya daya a matsayin abinda zai wahalar cimmawa,duk da yake dai tsarin mulki ya bada damar mu’amala da duk wata kungiya.

A wata ganawa ta musamman da Jaridar LEADERSHIP, ta ranar Lahadi,tayi dasu sun nuna damuwarsu akan irin kwamacalar siyasar da ake yi a Nijeriya,suka kara yin bayani cewa ai yanzu babu jajircewa da tsayawa kan lamarin da aka san mutum cikin jam’iyya,wanda ya kamata ace shi ne ake sa ran zai yi ma jam’iyya siyasa, Shugabannin majalisar yanzu abin babu ya dade da kwanta dama.

LABARAI MASU NASABA

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

Sun dora alhakin haka kan Shugabannin majalisar kasa wadanda sune suka yarda,da irin yadda lamuraran ke tafiya a majalisar.

Shugabnnin jam’iyyun adawa (PDP) da kuma (LP) sun zargi jam’iyya (APC) wadda take samar da matsala a jam’iyyun domin ta maida Nijeriya mai bin tafarkin jam’iyya daya.

Wannan ya bullo ne bayan da aka samu komawa ita jam’iyyar APC daga jam’iyyun adawa,ba domin komai ba sai saboda irin rigingimun cikin gida wadanda suka faru.

Wasu kafofin yada labarai sun bada rahoton cewa akwai ‘yan adawa fiye da 300 suka bar jam’iyyar PDP da sauran wasu jam’iyyun adawa zuwa APC tun dga shekarar 2023.

Yayin da dukkan sauya shekar siyasa abin ya faru ne a majalisun gwamnatin tarayya dana Jihohi, rushewar jam’yyar PDP da dukkannin abubuwanta zuwa APC a Jihar Delta,karkashin jagorancin gwamna Sheriff Oborebwori,wannan shi ne babban barin wata jam’iyyar siyasa zuwa wata wanda ana iya cewar ita ce ficewa daga jam’iyya da ta fi tayar da hankali.

Gwamann Jihar Akwa Ibom Umo Eno shi ma ana ta rade- raden cewar nan bada jimawa ba zai koma APC ,yayin dai lamarin ya kara kamari domin da akwai wsu manyan jiga- jigan da ake sa ran za su koma jam’iyya mai mulki.

Sai dai kuma maganganun da Shugaban jam’iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje’ sun jawo ma shi caccaka dangane da hakan.

Shi ma Shugaban kasa Bola Tinubu bada dadewa ba a wani taron jam’iyyar,yace tsarin jam’iyya daya bai da kyau ga mulkin farar hula;amma kuma ba hawan ba saukar a wani babin na shi yace ana maraba da dk wanda yake son dawowa jam’iyyar, saboda ai tsarin mulki ne ya bada damar ‘yancin yin hakan.

Halin da ake ciki yanzu Nijeriya tafiyar da mulkin farar hula mai jam’iyyun siyasa da aka yi wa rajista 18.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
Rahotonni

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

October 11, 2025
Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
Rahotonni

Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

October 11, 2025
Next Post
Sojojin Sama Sun Tarwatsa Maɓoyar Ƴan Ta’adda, Ya Daƙile Hari Ranar Idi A Borno

Sojojin Sama Sun Tarwatsa Maɓoyar Ƴan Ta’adda, Ya Daƙile Hari Ranar Idi A Borno

LABARAI MASU NASABA

Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya

Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya

October 21, 2025
An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba

An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba

October 21, 2025
Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

October 21, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC

Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC

October 21, 2025
NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 

NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 

October 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

’Yansanda Sun Kama Ɗan Fashi Sanye Da Kayan NYSC A Enugu

October 21, 2025
Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.