Tsohon mai ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin siyasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa babu wani dan takara da zai iya lashe kujerar shugaban kasa a 2027 ba tare da goyon bayan arewa ba.
Ya dai bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a Kaduna a karshen mako, Baba-Ahmed, wanda ya kasance tare da tsohon sakataren hukumar inshorar kiwon lafiya ta kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya jaddada cewa nan ba da dadewa ba arewa za ta ayyana matsayarta na siyasa.
- ‘Yan Sama Jannati 3 Na Kumbon Shenzhou-20 Na Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniyar Sin Cikin Nasara
- Idan Kana Son Barin PDP, Yanzu Ne Lokacin – Bukola Saraki
Ya ce, “A cikin watanni shida masu zuwa, arewa za ta yanke shawarar kan matsayarta na siyasa. Idan sauran yankuna suna so su shiga tare da mu, babu matsala kan haka. Idan ba haka ba kuma, sai mu bi hanyarmu ta daban. Abu daya da yake a bayyane shi ne, babu wanda zai iya zama shugaban Nijeriya ba tare da goyon bayan arewa ba.”
Ya koka kan halin da kasar ke ciki, kuma ya bukaci ‘yan arewa da su yi taka-tsantsan da ‘yan siyasa masu rarraba kawunan mutane da yaudara, gabanin babban zabe mai zuwa.
“Muna son gwamnati da za ta fahimci matsalolinmu kuma ta magance su. Bayan shekaru takwas na mulkin Muhammadu Buhari, mun dauki darasi.
”Yanzu haka muna cikin wata gwamnati, kuma har yanzu muna kuka. Kuka kadai ne muka san yadda za mu yi?” Baba-Ahmed ya tambaya.
Baba-Ahmed ya ce arewa ta sha wahala sosai a lokacin Boko Haram, wanda ya shafi dukkan kungiyoyi, ciki har da Musulmi da Kiristoci da Fulani da Baju, da sauransu, yana mai jaddada bukatar hadin kai.
“Kafin Buhari ya zama shugaban kasa, Boko Haram na kai hari kan masallatai, coci-coci, Abuja da Legas. Wannan shi ne lokacin da ‘yan arewa suka hada kai.”
Ya yi gargadi game rashin girmama yankin arewa, yana mai cewa ci gaba da rashin girmama yankin zai haifar da mummunan sakamako.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp