• English
  • Business News
Friday, August 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Gangamin ‘Yan Adawa Ya Sa APC Fafutukar Neman Mafita

by Idris Aliyu Daudawa and Sulaiman
3 weeks ago
in Manyan Labarai, Rahotonni
0
APC
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Yayin da ake ta shirye shiryen taron majalisar zartarwa na jam’iyyar APC da akwai shakkun da suke nuna har yanzu jam’iyyar bata yanke shawarar ko amincewa da daga wane bangare ne sabon Shugaban jam’iyyar na kasa,ya kamata ya fito.

Majaiya kwakkwara ta bayyanawa jaridar karshen mako ta Weekend Trust ta bayyana cewar jam’iyyar tana jira ta samu bayani daga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu akan daga wane sashe na Arewa yake son a zabi sabon Shugaban jam’iyyar,sai dai kuma masu ruwa da tsaki sun fi son,a maida mukamin Shugaban sashen Arewa ta tsakiya ko Arewa ta Yamma,saboda wasu dalilai.

  • Ko Kaɗan Bamu Ji Takaicin Ficewar Atiku Daga Jam’iyyar PDP Ba — Damagum
  • Wata Motar Tankar Mai Ta Kama Da Wuta Tare Da Kone Wasu Motoci A Ibadan, Jihar Oyo

Tun lokacin da tsohon gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje,ya sauka daga mukaminsa na Shugaban jam’iyyar, wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar suna kokarin sashen Arewa maso Yamma ya ci gaba da rike mukamin, koda kuwa a matsayin na riko,har sai zuwa lokacin da za a zabi Shugaban.

Dalilin hakan kamar yadda aka ji daga wata wata majiyar jam’’iyyar,shi ne saboda tsarin karba karba na jam’iyyar, saboda wasu abubuwan da suka taso bayan sauka daga mukamin wanda ya yi saboda a samu taushe wani abinda ka iya tasowa na rikicin cikin gida na jam’iyyar.

Wakilanmu sun bayyana cewa dalilan dsa suka sa, hakan sune a bar shi sashen na Arew a maso Yamma ya ci gaba da rike mukamin domin a rika yi ma lamarin kallon kamar ci gaba Shugabancin na Ganduje ne.

Labarai Masu Nasaba

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

Gwamnan Kano Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Gentle, Ya Bada Umarnin Zakulo Masu Laifin

Daya dacikin dalilan nasu shi ne yadda sashen yake da masu jefa kuri’a da yawa, wanda babu wani dan takarar Shugaban kasar da zai yiwa sashen rikon sakainat kashi.

Daya daga cikin majiyar ta nuna matakin ana son daukar shi ne domin kada aga kamar an an batama wasu mambobin jam’iyyar APC daga Arewa maso yamma,wadanda zasu iya ganin kamar an maido su Saniyar ware ne,idan an ki basu mukamin,hakanan kuma duk,a,lokaci daya,kada,a bata ma mabobin jam’iyyar daga Arewa ta tsakiya rai,wadanda kuma ake yi ma kallon babu wadanda suka fi dacewa da hakan kamar su saboda yadda lamarin karba-karba na jam’iyyar yake.

Kafin dai Ganduje ya sauka daga mukamin,ana kallon yawancin mambobin jam’iyyar,sun amince da tsarin da jam’iyyar ta yi cewar sashen Arewa maso yamma ya cigaba da rike mukamin Kujerar Shugaban jam’iyyar tun bayan da Sanata Abdullahi Adamu, amma kuma sai ga shi gurbin daya sauka daga mukamin da Ganduje yayi,yasa an dawo da sabuwar bukatar maganar son sashen ya ci gaba da rike mukamin.

Wata majiyar kuma ta bayyana cewa ana jiran a ji daga baki Shugaban kasa Bola Tinubu,wanda shi ne ke da alhakin wanda wanda yake ganin zai fi yi masa biyayya yayin da ake tunbkarar zaben shekara ta 2027.

Ana, iya da tunawa Ganduje ya sauka daga mukamin ne ranar 27 ga Yuni 2025 saboda lamarin daya shafi lafiyarsa,a wasikar daya aikawa Sakataren jam’iyyar na kasa,Ajibola Bashiru.

A wasikar,tsohon Shugaban ya bayyana yana bukatar lokacin ne domin ya lura da lafiyarsa.

Wata majiya kuma a cikin jam’iyyar ta nuna wata dabarar da ake kokarin yi daga jam’iyyar kafin zaben shekarar 2027.

Mataimakin Shugaban jam’iyyar na(Arewa),Ali Bukar Dalori, tuni shi ne yam aye gurbin Ganduje,a matsayin mai rikon mukamin Shugaban jam’iyyar.

Yayin manya d aga jam’iyyar suke ganin ba laifi bane a bar Dalori akan mukamin, yayin da wasu kuma suke kalon idan aka bar sassan Arewa ta tsakiya da yamma daga lamurra masu muhimmanci na jam’iyyar.

Jaridar Trust ta karshen mako ta bada rahoton mako biyu da suka gabata, bayan sauka daga mukamin wanda Ganduje ya yi,akwai sunayen manyan ‘yan jam’iyyar APC daga Arewa ta tsakiya da kuma Arewa maso yamma sun bayyana sha’awarsu ta neman Shugabancin jam’iyyar.

Zuwa yanzu dai masu neman mukamin yawancinsu daga sashen Arewa ta tsakiya ne, daya ne kawai daga Arewa maso yamma inda Ganduje ya fito.

Kamar dai yadda majiyar ta nuna, wadanda suke neman Shugabancin jam’iyyar daga Arewa tsakiya akwai tsohon gwamnan Jihar Nasarawa,Umaru Tanko Al-Makura; tsohon gwamnan Jihar Kogi ,Yahaya Bello; Sanata mai wakiltar mazabar Neja ta gabas, Sani Musa; tsohon gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye, Sanata Solomon Ewuga daga Jihar Nasarawa Nasarawa,da kuma Sanata Salihu Mustapha daga Jihar Kwara.

Duk wanikokarin da aka yi ta jin bakinsu ba a samu nasarar hakan ba.

Alal misali,an kira da kuma aikawa da sakonni zuwa ga Sanata Musa, Sanata Mustapha, Ewuga da Dariye, amma ba a amsa kiran ba, ko kuma bada amsar sakon.

Sai daiu kuma wata majiya dake kusa da su ‘yan takararar ta bayyana cewa kowane daga cikinsu yana jiran “wani bayani mai karfi daga wurin Shugaban kasa.”

Wata majiya ta nuna,“Maganar gaskiya, Shugabana shi ya dace ya yi hira da kai kamar yadda kaso amma kuma bai son ya bata wata alaka da yake da ita, daga wurin Shugaban kasa da kuma Shugabannin jam’iyya.

“Haka nake tunani daga suma sauran’yan takarar. Suna bukata ne wadanda suke da ruwa da tsaki suce su fito su yi takara, sabon Shugaban jam’iyyar zai kasance daga sashen Arew a ta tsakiya ko Arewa ta yamma kamar yadda ya furta,”.

Wani abu daban kuma shi ne Sanata Abu Ibrahin daga Jihar Katsina shi ne dantakara daya tilo daga Jihar Katsina wanda yake son a zabe shi sabon Shugaban jam’iyyar, daga sashen Arewa maso yamma.

Majiya mai tushe ta bayyana cewa Sanata Abu Ibrahim wanda ya yi sanata sau hudu kafin ya yi ritaya ta kashin kansa, shi ma na hannun damar Shugabn kasa Bola Tinubu ne,ana ganin shi zai maye gurbin Ganduje.

Sai dai kuma a wata ganawar da aka yi tashi Sanata Abu Ibrahim yace babu wanda ya tuntube shi dangane da hakan.

Sai yace, “Waccan magana (duk wani shaci- fadi ne na kasancewa Shugaba) abin ya bani mamaki ni ma. Da fako ban tattauna maganar da Shugaban kasa ba .Babu wanda ya tuntube ni.

“Ni a kashin kaina, Ina ganin na yi iyakar abinda zan iya yi a siyasa. Na fi son in tsaya domin na huta daga lamarin siyasa, saboda in ba matasa su kasance Shugabanni. Ni bukata ta ke nan.”

Ya kara bayanin cewa maganar da ake ta yadawa ne watakila wani abinda aka shirya ne.“Mutane suna tsammani ko zato suke zan iya tafiya da irin lamarin.Har yanzu, ni ban nuna sha’awa taba aka ita maganar da aka yadawa.”

An samu bayani Shugabannin jam’iyyar daga Arewa basu ji dadin basu dadin irin yadda Ganduje ya sauka daga mukamin ban a Shugaban jam’iyya na kasa,hakan shi yasa su suke son su ko a cigaba da rike mukamin Shugaban jam’iyyar.

Makon da ya wuce,Shugabannin jam’iyyar APC a Jihar Kano sun ki fitowa su yiwa su yi maraba mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima, wanda ya je Kano domin ya yi gaisuwar ta’aziyya ga iyalan marigayi babbab dan kasuwa Alhaji, Aminu Dantata, wanda baud ade da rasuwa ba.

Yayin da Shugabannin ko jami’an jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) suka yi maraba mataimakin Shugaban kasa, su kuwa jami’ai da Shugabannin APC basu je wurin daya tafi ba,wannan lamarin yasa aka fara tunanin cewa da walaki goro cikin miya.

Masu fashin baki kan lamarin siyasa sune an yi hakan ne da gangan domin a nuna lalle ba aji dadin yadda Ganduje, wada tsohon gwamna ne na Jihar Kano, wanda har yanzu yana da fada aji, kan lamarin siyasa a cikin Jihar.

Sai dai kuma Sakataren jam’iyya na Jihar APC, Ibrahim Zakari Sarina, yayi watsi da lamarin na kauce wa lamarin, yace dalilin da ya sa ba a samu zuwan Shugabannin jam’iyyar na Jiha lokacin ziyarar Shettima “domin lamarin saboda rashin tuntuba.”

Masu lura da lamurran siysa sun ceshi takun da aka fara yi shi ne na a dauki Sanata Abu Ibrahim a matsayin wanda zai maye Ganduje, domin a dadadawa masu fada aji na jam’iyyar APC, na sashen saboda yin la’akari da yadda yake muhimmanci kan lamurran siyasa. Ba ma kamar yadda yake da Jihohi bakwai da kuma mafiya yawan kuri’u idan aka zo maganar zabubbuka.

Jaridar Trust ta karshen mako ta bada rahoton Sanata Abu Ibrahim,wanda babban dan siyasa ne a Jihar Katsina ya taka muhimmiyar rawa ko babbar gudunmawa, a lamurran siya a shekarun 1990 tare da Bola Ahmed Tinubu. Kafin Ganduje, akwai Shugabanni biyar: Chief Bisi Akande (2013 zuwa 2014); Chief John Oyegun (2014 zuwa 2018); Komrade Adams Oshiomhole (2018 zuwa 2020); Mai Mala Buni (2020 zuwa22)da kuma Abdullahi Adamu (2022 zuwa 2023).


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Dalilin Da Ya Sa Dangote Ya Jinjina Wa Hukumar NPA

Next Post

Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa

Related

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara
Manyan Labarai

Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara

19 hours ago
Gwamnan Kano Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Gentle, Ya Bada Umarnin Zakulo Masu Laifin
Manyan Labarai

Gwamnan Kano Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Gentle, Ya Bada Umarnin Zakulo Masu Laifin

1 day ago
Masu Ƙwacen Waya Sun Kashe Ɗalibin BUK A Kano
Manyan Labarai

Masu Ƙwacen Waya Sun Kashe Ɗalibin BUK A Kano

1 day ago
Jami’an Tsaro Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara, Sun Ƙwato Bindigogi
Manyan Labarai

Jami’an Tsaro Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara, Sun Ƙwato Bindigogi

1 day ago
Yawancin ‘Yan Siyasar Nijeriya Ba Su Da Tarbiyya – Sarki Sanusi II
Manyan Labarai

Yawancin ‘Yan Siyasar Nijeriya Ba Su Da Tarbiyya – Sarki Sanusi II

1 day ago
Tinubu Ya Taya Nafisa, Rukayya, Hadiza Murnar Samun Nasarar Zama Gwanaye A Gasar Turanci Ta Duniya
Manyan Labarai

Tinubu Ya Taya Nafisa, Rukayya, Hadiza Murnar Samun Nasarar Zama Gwanaye A Gasar Turanci Ta Duniya

2 days ago
Next Post
Fyade

Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa

LABARAI MASU NASABA

Ba Gaskiya Ba Ne Rahoton Da Ke Cewa An Yi Sulhu Da Bello Turji – Guyawa Isa

Ba Gaskiya Ba Ne Rahoton Da Ke Cewa An Yi Sulhu Da Bello Turji – Guyawa Isa

August 8, 2025
Tashin Gurneti Ya Hallaka Yara Uku A Borno

Tashin Gurneti Ya Hallaka Yara Uku A Borno

August 8, 2025
Nijeriya Na Asarar Tiriliyan 3.2 Sanadiyyar Watsi Da Noma A Gandun Daji

Nijeriya Na Asarar Tiriliyan 3.2 Sanadiyyar Watsi Da Noma A Gandun Daji

August 8, 2025
GORON JUMA’A 8-8-2025

GORON JUMA’A 8-8-2025

August 8, 2025
Yara Uku Sun Gamu Da Ajalinsu A Wani Tafki A Borno

Yara Uku Sun Gamu Da Ajalinsu A Wani Tafki A Borno

August 8, 2025
Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)

Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)

August 8, 2025
Jirgin Shugaban Ƙasa Ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 Cikin Wata 18 Ƙarƙashin Tinubu

Jirgin Shugaban Ƙasa Ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 Cikin Wata 18 Ƙarƙashin Tinubu

August 8, 2025
Mamakon Ruwan Sama A Wasu Jihohi Na Barazana Ga Harkokin Yau Da Kullum

Mamakon Ruwan Sama A Wasu Jihohi Na Barazana Ga Harkokin Yau Da Kullum

August 8, 2025
Buƙatar Katange Iyakokin Nijeriya Don Tabbatar Da Tsaro 

Buƙatar Katange Iyakokin Nijeriya Don Tabbatar Da Tsaro 

August 8, 2025
Faɗace-Faɗacen Daba Da Ƙwacen Waya A Kano Ya Ɗauki Sabon Salo

Faɗace-Faɗacen Daba Da Ƙwacen Waya A Kano Ya Ɗauki Sabon Salo

August 8, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.