Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya gargadi cewa jam’iyyar PDP za ta fuskantanci hadarin tarwatsewa idan ta yi kokarin dawo da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi a cikin jikinta kafin zaben 2027.
A yayin wata tattaunawarsa tare da ‘yan jarida, Wike ya ce PDP ba ta dauki darasi ba game da kuskurenta na baya wadanda suka janyo mata rashin nasara a zaben 2023.
- An Shiga Damuwa Yayin Da Gwamnatin Nijeriya Ke Jinkiri Wajen Biyan ‘Yan Kwangila
- Gwamnatin Kaduna Ta Zargi El-Rufai Da Yunkurin Tayar Da Tarzoma A Jihar
Ya tunatar da cewa shi da sauran shugabannin jam’iyyar sun sake maimaita wanjen kuskuren na bari dan takarar shugaban kasa da shugaban jam’iyyar na kasa su fito daga yankin arewacin Nijeriya, wannan wani mataki ne na wanda ya saba da tsarin siyasar kasar nan.
“Tun daga ranar farko, na gaya wa abokan aikina da ke cikin jam’iyyar PDP cewa kuna daba wa cikinku wuka. Idan kuka bari abubuwan da ke faruwa su ci gaba a haka, za ji a jikinku. Kuma me na ce? Ba za ku iya fitar da dan takarar shugaban kasa da shugaban jam’iyya na kasa su fito a yankin guda ba,” in ji Wike.
Tsohon gwamnan Jihar Ribas ya zargi PDP da rashin yin adalci wajen rarraba mukamai da kuma watsi da kiraye-kirayen yin adalci da daidaito, a cewarsa, wannan mataki su ne makasudin rashin nasarar jam’iyyar a zaben bara.
“Yana da kyau tun yanzu a warwaren matsalar tikitin takarar shugaban kasa kuma na shugaban jam’iyyar na kasa n. A gani na hakan shi ya fi dacewa. Kuma shi ne adalci a siyasance. Ba na yin dana sani a kan haka,” ya bayyana.
Wike ya jaddada cewa dole ne shugabancin kasar nan ya sake komawa yankin kudu don tabbatar da adalci da daidaito a cikin harkokin siyasar Nijeriya.
A cewarsa, girman kai da kin sauraron gaskiya daga wasu shugabannin PDP sun sa jam’iyyar taraunata, sannan kuma ta samu rashin karfi tare rasa samun mulki.
Ya kuma musanta maganganun da suka shafi yiwuwar dawowar Obi cikin PDP, yana bayyana wannan mataki a matsayin mai tsananin hadari a cikin jam’iyyar.
“Ta wani dalili za ku dawo mana da Obi cikin wannan jam’iyyar? Kana son kashe jam’iyyar ne? Obi wanda yake zagin jam’iyyar, yana cewa ta lalace, yanzu kuma jam’iyyar ta zama mai kyau a gare shi ne? Burin mutum na iya sa mutane su kasance har zuwa gidan Shaidan,” in ji Wike.
Ministan ya kara jaddada cewa irin wannan hukunci zai kara lalata ingancin jam’iyyar kuma zai tarwatsa duk wata ginshikin da ya rage a cikin jam’iyyar a halin yanzu.
Ya ce, “Idan kana son tarwatsa jam’iyyar ne, to zai ka gaggauta shigo da Obi cikin jam’iyyar. Babu wata hanya da zai dawo saboda burinsa na kashin kai. Babu dabara da kuma ka’ida a wannan mataki,” ya kara bayyanawa.
Wike ya ci gaba da cewa yana tsaye kan matsayinsa cewa a yi adalci da gaskiya da kuma bin tsarin karba-karba domin ta wannan hanya ce kadai jam’iyyar PDP za ta sau damar dawo da tasirinta a kasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp