Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa hukumar ta karbi wasikun kungiyoyi 110 da ke neman rajista a matsayin jam’iyyu siyasa kafin zaben 2027.
Yakubu ya bayyana hakan a yayin taron INEC tare da manyan jami’an kafafen watsa labarai da aka gudanar a Abuja.
- Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 1,191, Sun Ceto 543 Cikin Watanni Uku
- Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 50 A Benue
Shugaban INEC ya bayyana cewa tun ranar 23 ga Yuni, hukumar ta karbi wasikun kuma tana gudanar da aiki a kansu bisa doka da ka’idojin zabe.
“Tun a ranar Litinin, 23 ga Yuni 2025, hukumar ta karbi wasikun kungiyoyi 110 da suke son rajista a matsayin jam’iyyu na siyasa. Muna aiki tukuru wajen sarrafa bukatun tare da bin tsarin da aka gindaya a cikin doka da kuma ka’idojinmu na zabe.
“Mun amince da duk bukatun ban da guda shida da aka karba kwanan nan wadanda za a kammala aikinsu kafin karshen mako,” ya bayyana.
Yakubu ya jaddada kokarin hukuma wajen yin adalci.
“Za mu duba dukkan bukatun cikin adalci ba tare da la’akari da matsayin wadanda suka kawo su ba, lallai hukumar zabe ba za ta taba karya ka’idojinta ba.”
Shugaban INEC ya musanta zarginsu cewa hukumar kokarin hada kai da wasu domin saba ka’ida wajen yin ragisara, ya tunawa da irin wannan zargin da ba tare da hujja ba da aka yi a shekarar 2013.
Ya bayyana cewa hukumar ta amince da dukkan wasikun da aka karba illa guda shida, wadanda za a yi aiki a kai kafin karshen mako. Haka nan ya lura cewa dokoki da ka’idojin zabe ta 2022 kan jam’iyyun siyasa yana nan a shafin intanet na hukumar.
Yakubu ya kara da cewa za a fitar da cikakken jerin kungiyoyi 110, ciki har da sunayensu da yadda ake takaitawa da adireshi, da sunayen shugabanninsu da sakatarensu, nan ba da jumawa ba za a wallafa su a shafin intanet na INEC da kafofin sada zumunta don tabbatar da gaskiyar lamari ga jama’a.
Daya daga cikin kungiyoyin masu neman zama jam’iyyun siyasa, ADA ana zargin cewa ta samu goyon bayan ne da hadakar wasu shahararrun mutane masu tasiri a siyasa, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da kuma tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi.
Wata kungiyar kuma wanda ake tsammanin tana samun goyon baya daga magoya bayan tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ta gabatar da bukatar rajista karkashin suna mai kama da na LP, wanda ke nuna damuwa game da yiwuwar maimaitawar sunan LP.
INEC ta ce akwai kura-kurai mai yawan gaske a cikin wasu takardun da aka gabatar. Wasu daga cikin kungiyoyin sun yi amfani da suna iri daya, wanda hakan ya sab awa ka’idodin INEC.
Kazalika, INEC ta gano cewa akwai kungiyar da ta gabatar da bukatar yin rajistar guda biyu, kowanne tare da shugabanci da adireshi daban.
INEC ta bayyana cewa za ta tantance dukkan bukatun bisa ga tsarin doka da ka’idojin aikinta kafin ta yi rajista ko ta ki.
Bugu da kari, INEC ta ce akwai bukatar da aka shigar mata na neman yin rajista daban-daban har guda biyu a karkashin sunan ‘Obidient Peoples Party’.
A cewarta, wasu ana takaita sunayenu sun yi kama da na jam’iyyun da aka soke rajistarsu a baya, kuma an shigar da wasu takardu ba tare da sa sunayen shugabannin jam’iyyar ba, wanda haka ya saba wa ka’idojin INEC.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp