ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Masu Neman Takarar Shugaban Kasa A PDP Sun Kara Matsa Kaimi Bayan Ficewar Atiku

by Yusuf Shuaibu and Sulaiman
4 months ago
PDP

Gwagwarmayar neman takarar shugaban kasa a jam’yyar PDP a 2027 ta kara kaimi tun bayan da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar, wanda ta bude hanya ga gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, da sauran masu sha’awar neman takarar shugaban kasa da ke neman kalubalantar tazarcen Shugaban kasa Bola Tinubu.

Masu ruwa da tsaki na PDP, wadanda suka yi jawabi kan lamarin cikin sirri, sun tabbatar da cewa burin tsayawa takarar shugabancin kasar na Makinde da Bala ya kasance sanannen abu a tsakanin muhimman masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

  • Gwamnan Jigawa Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Dokar Tabbatar Da Hisbah
  • Matsalar Tsaro: Sarakuna Sun Bukaci Gwamnati Ta Canza Salo

Wata majiya mai tushe daga jam’iyyar ta bayyana cewa PDP ta bude kofa ga duk masu neman takarar shugaban kasa bisa bin dokokin jam’iyyar.

ADVERTISEMENT

Yayin da babban jigon jam’iyyar PDP, Cif Bode George, ya tabbatar a cikin wani tattaunawa ta musamman cewa, ana ci gaba da kokarin samun dan takarar shugaban kasa daga kudu, sauran mambobin kwamitin zartarwa na kasa sun bayyana ra’ayi daban-daban kan batun tsarin karba-karba na yankuna.

A daidai lokacin da PDP ke fama da rikicin cikin gida da suka hada da na shugabanci da batun tsarin karba-karba a tsakanin yankuna wanda jam’iyyar ke kokarin warwarewa kafin zaben 2027.

LABARAI MASU NASABA

ADC Ta Tsara Ka’idojin Da Shugabanninta Za Su Bi Don Tunkarar Zaben 2027

Rikicin PDP: Fiye Da Wakilai 3,000 Ne Za Su Raba Gardama A Babban Taron Jam’iyyar

Kwanan nan jam’iyyar PDP ta gudanar da taron kwamitin zartarwa karo na 100 da aka gudanar ranar 30 ga Yuni, PDP ta warware rikicin da ya dade yana ci mata tuwo a kwarya na batun mukamin sakataren jam’iyyar na kasa wanda ta tabbatar da Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar.

Duk da wannan warware batun, Atiku da wasu magoya bayansa sun fice daga jam’iyyar sakamakon rashin warware rikicin gida na jam’iyyar.

A ranar 1 ga Yuli, Atiku da Peter Obi da Rotimi Amaechi da Nasir El-Rufai, da wasu sun kulla hadaka a karkashin jam’iyyar ADC, sun ce sun yi wannan hadakar ne domin kalubalantar APC a zaben 2027.

A matsayin wani bangare na wannan yunkurin hadin gwiwa, sun nada tsohon shugaban majalisar dattawa, Dabid Mark a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa na wucin gadi da tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa na wucin gadi.

Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa Makinde da Bala Mohammed su ne manyan ‘yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar a yanzu haka, yayin da ake sa ran wasu jiga-jigan jam’iyyar za su biyo baya kafin zaben 2027.

Majiyar ta ce, “Ana tambayar game da wadanda suka nuna sha’awarsu na neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyya a halin yanzu. Duk da dai ba su fito fili sun bayyana ba, mun ji daga wurin shugabannin jam’iyyar, cewa Makinde da Bala Mohammed har ma da wasu tsoffin gwamnonin daga Kudu suna da sha’awar neman tikitin shugaban kasa jam’iyyar PDP a 2027.

“Amma a hakikanin gaskiya, a yanzu haka ba za mu iya sanin adadin wadanda suke sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a PDP, sai idan lokaci ya yi duk za a san su. Don haka, jam’iyyar PDP ta bude kofarta ga kowa, kuma ta kasance jam’iyyar da ke da karbuwa sosai a tsakanin ‘yan Nijeriya.”

Wani jigo a jam’iyyar wanda ya nemi a Sakaye sunansa don ba a shi izinin yin magana a hukumance ba, ya goyi bayan bude tikitin takarar shugaban kasa a PDP a 2027 ga dukkan ‘yan Nijeriya.

Shi kuwa, tsohon mataimakin shugaban PDP na yankin kudu maso yammaci, Eddy Olafeso, ya bayyana cewa shugabannin jam’iyyar sun dauki darashi ga abubuwan da suka faru a baya.

Yayin da tsohon sakataren jam’iyyar na kasa, Ibrahim Tsauri, ya shawarci mambobin jam’iyyar cewa su bar uwar jam’iyyar ta yanke hukunci, sannan kuma ya yi gargadi kan kauce wa bin tsarin karba-karba.

A nasa martanin, daraktan yada labarai na jam’iyyar APC, Bala Ibrahim ya ce Shugaban Tinubu zai kayar da Makinde, Bala Mohammed, ko wani dan takarar da PDP ta tsaida a 2027.

Ibrahim ya bayyana cewa, “Makinde da Bala Mohammed ba su da wata gogewa a matakin kasa na siyasar Nijeriya. Wadannan gwamnonin biyu ba za su iya jure fafatawar siyasar kasa nan ba. Ba su da gogewar da dan takararmu yake da shi.

“Mutane da ka ambata ba su da ikon doke shugaban kasa a kowanne fanni na siyasa. Wannan ba matsala ce da za ta ba mu ciwon kai ba. Koma dai wane yanki PDP zai fitar da dan takarar shugaban kasa ba zai yi nasara ba a 2027.”

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

ADC Ta Tsara Ka’idojin Da Shugabanninta Za Su Bi Don Tunkarar Zaben 2027
Tambarin Dimokuradiyya

ADC Ta Tsara Ka’idojin Da Shugabanninta Za Su Bi Don Tunkarar Zaben 2027

November 14, 2025
Tambarin Dimokuradiyya

Rikicin PDP: Fiye Da Wakilai 3,000 Ne Za Su Raba Gardama A Babban Taron Jam’iyyar

November 14, 2025
Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya
Tambarin Dimokuradiyya

Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

November 7, 2025
Next Post
Binciken Jin Raayoyi Na CGTN: Duniya Ta Saba Da “Kauracewar” Amurka

Binciken Jin Raayoyi Na CGTN: Duniya Ta Saba Da "Kauracewar" Amurka

LABARAI MASU NASABA

APOSUN Ta Jaddada Aniyarta Na Daƙile Hada-hadar Haramtattun Kuɗaɗe

APOSUN Ta Jaddada Aniyarta Na Daƙile Hada-hadar Haramtattun Kuɗaɗe

November 16, 2025
Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

November 16, 2025
Kwankwaso

NNPP Tana Da Ƙwarin Gwiwar Riƙe Kano Da Lashe Jihohin Arewa A Zaɓen 2027 – Ajuji

November 16, 2025
Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?

Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?

November 16, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

November 15, 2025
Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

November 15, 2025
Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

November 15, 2025
Za A Yi Gwanjon Rigunan Messi Na Gasar Kofin Duniya Ta 2022 Da Kudi Tsagwagwa

Ina Son Kasancewa Cikin Koshin Lafiya Kafin Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Messi

November 15, 2025
Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci

Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci

November 15, 2025
Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

November 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.