Dan takarar shugaban kkasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Mista Peter Obi, ya tabbatar da cewa takarar shugaban kasa zai yi a zaben 2027, ya musanta jita-jitar da ake yi cewa yana son zama mataimakin shugaban kasa.
Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya bayyana hakan ne yayin shirin siyasa na gidan talabijin na Channels da ke Abuja.
- Sojoji Sun Kai Hari Maɓoyar Boko Haram A Borno, Sun Kashe Wasu ‘Yan Ta’adda
- Shiri Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Tabbatar Da Ci Gaban Kasar Sin
Ya kuma yi alkawarin gudanar da wa’adi guda daya kacal idan an zabe a matsayin shugaban kasa, yana mai jaddada cewa ba zai ci amana ba a kan wannan lamari.
“Ba na bukatar karin kwana daya kan shekaru hudu. Zan gudanar da kyakkyawan shugabanci. A cikin shekaru biyu, an lalata kasar nan. Zan iya sauya babuwa cikin shekaru biyu. Mutane na bukatar samun shugaba wanda ke kulawa tare da nuna tausayin su,” in ji shi.
Obi ya kasance cikin muhimmin mambobi a hadakar jam’iyyun adawa ta ADC da aka kaddamar makon da ya gabata.
An dai yi ta tsokaci kan cewa ko Obi zai amince da mukamin mataimakin shugaban kasa tare da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, kamar yadda ya yi a 2019.
Obi ya ce, “Takarar shugaban kasan Nijeriya zan yi a 2027, kuma na tabbatar da cancanta.”
A kan ko zai hakura ya zama mataimakin takarar Atiku a 2027, Obi ya bayyana cewa, “Wannan abun wasa ba ne, babu wanta ya tattauna hakan. Mutane ne kawai yin irin wannan tunani. Amma a zahirin gaskiya babu wanda ya bayyana hakan.”
Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya kuma jaddada cewa har yanzu yana shi mamba ne a jam’iyyar LP.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa Obi yana daga cikin shahararrun mutane a cikin hadakar ADC da ‘yan adawar masu kokarin karbe mulki a wurin Shugaban kasa Bola Tinubu na jam’iyyar APC, wanda ke neman zarcewa a wa’adi na biyu a zaben 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp