Gwamnan Binuwe Na Sukar Shugaban ‘Yan sanda Ne Don Boye Tasa Gazawar Ne -Shettima

A cikin makon nan ne shugaban Kungiyar Tuntuba Ta Matasan Arewa (Arewa Youth Consultatibe Forum), ALHAJI YERIMA SHETTIMA, ya roki shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, da kada ya saurari gwamnan jihar Binuwe har ya hukunta babban sufeton ’yan sandan Nijeriya, Ibrahim Idris, kan zargin bijirewa umarnin shugaban kasar na tare wa a jihar tun bayan da kashe-kashen makiyaya da manoma ya tsananta.

Wannan ya biyo bayan kalaman shugaban kasar ne a lokacin da ya ziyarci jihar ta Binuwe na cewa bai san shugaban rundunar ’yan sandan bai zauna a jihar sama da awannin 24 ba. To, amma a wannan tattaunawar da Editan LEADERSHI A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, ya yi da shi, Yerima Shettima ya bayyana matukar shakkunsa kan wadannan kalaman na Shugaba Buhari, ya na mai cewa zai yi wuya a ce bai san halin da babban sufeton ke ciki ba. Ga dai yadda hirar tasu ta kasance:

A tsakiyar makon nan kun fitar da sanarwa da ke kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya hukunta babban sufeton ’yan sanda, IGP Ibrahim Idris, kan zargin bijirewa umarninsa na tare wa a jihar Binuwe. Shin mene ne dalilinku na tsoma baki a cikin batun?

Abinda ya sa mu ka yi wannan bayani shi ne, duk da ya ke Nijeriya tsinci kanta a wani hali na jarabta a fannin tsaro kuma ya kamata a dauki matakin da ya kamata, amma bai kamata a yi amfani da shi a siyasance wajen cutar da wani ba, sannan mu kuma mu zura idanu. Wannan abinda ya ke faruwa a jihar Binuwe mu na da masaniya kan abinda ya ke faruwa. Ba komai ba ne illa siyasa ce kan duk ta yadda za a yi a kuntata wa al’umma. Misali shi ne, ko kafin shugaban kasa ya bada umarni ga shugaban ’yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, kan ya wuce Binuwe, ga dukkan alamu shi kansa gwamnan jihar Binuwe ya nuna ya na da wani abu da ya ke yawo a kansa ko ya yiwa shugaban ’yan sandan sharri.

 

Saboda me?

Shi ne zai yi bayanin me ya sa ya ke hakan, saboda shi wannan bawan Allah (IGP Idris) ma’aikaci ne, ba dan siyasa ba ne.

 

Amma wadanne alamu ku ka gani da su ke nuna haka?

Lafazuzzukan da ya yi daga farko babu wanda ya bari a cikin lafazinsa. Na farko ya zargi ita kanta gwamnatin, wanda kuma babu yadda za a yi kala wa wata kabila kage ka kai labari a Nijeriya ba, saboda wannan harka harka ce ta ta’addanci na barayi. Shi a ke yi a Binuwe da sauran gurare. To, mu tun farko mun haramta, mun yi kira ga gwamnati da sauran jami’an tsaro da kuma wadanda su ke gwamnati da kada su kalli abin da fuska ta kabilanci cewa masu kiwo Fulani ne su ke yi. Wadannan abubuwa ne da idan za a yi maganinsu, to kada a danganta shi da wata kabila; a yi maganin abin a matsayin an sami barayi ko za a maganin barayi ko ’yan fashi ko ’yan ta’adda. To, ga dukkan alama wannan gwamnatin jihar Binuwe, musamman gwamnan jihar ya na danganta lamarin da kabilanci, saboda ka ga duk wanda ya san abinda ke faruwa a Binuwe ya san wannan tun da a ka zabe shi babu wani abu da ya yi wa al’ummarsa. Saboda haka wannan dama ce ya samu da zai nuna wa jama’arsa ya ja hankalin wadanda ya ke shugabanta ya raba mu su hankali ta hanyar kabilanci…

 

Wato ka na ganin gwamna na Binuwe ya na boye gazawarsa kan jagorancin jihar gaba ne?

Eh, gazawarsa ta shugabancin jihar, shi ne kawai abinda ya sa a gaba. Ya kawo shugaban kasa ya zuba a cikin makircinsa da sharrinsa, ya kawo dattawana Arewa ya zaga, ya zo saboda makirci, duk inda Arewa ta ke tun asali kowa ya san cewa ita Binuwe a cikin Arewa, amma ya nuna wa duniya cewa shi bai yi da Arewa; wani zama ya ke yi a matsayin kansa. Don haka ya gwammace ya samu dangantaka da mutanen Kudu. Wannan ba shi ne tarihin Arewa na asali ba. Kuma wannan rigima tsakanin makiyaya da manoma ta dade fiye da shekara 500 a na yin ta, kuma su na da lokacin da su ke yin abubuwansu su dawo su yi sulhu, amma wannan da ya fito karara, ka san cewa ba wannan rigimar ba ce. Mu na da bayanii da ya ke nuna cewa, shi ya yi amfani da wasu matasa ya ba su bindigogi a kan su je su wai su kare kansu. Ma’ana; su lahantar da mutane, su wulakanta mutane ’yan kasar nan wadanda su ke tafiya kiwo a yi ta harbin su, kuma ya yi hakan, ya samu biyan bukatarsa, daga baya sai ya juyo ya koma kan ’yan sanda, saboda ko da a ka tura ’yan sanda, shugaban ’yan sanda ya je Benuwe. Ya kasa bambance ina ne Benuwe ina ne Makurdi. Don mutum ya je kasar Benuwe bai kwana a Makurdi ba, wannan ba ya nufin cewa bai kwana a Benuwe ba, domin ba Makurdi ba ce kadai Benuwe. Kuma shugaban ’yan sandan tun kafin ya je Benuwe ka nuna cewa ba zai yi ma ka adalci ba, ka ga kenan babu mai yarda da kai, don ka riga ka nuna wa mutanenka wani tunani a kan wannan. Mu ka yi ta gargadi a kan lamarin nan. A sakamakon haka sai da mu ka yi kira cewa a yi kaddamar da dokar tabaci a jihar Benuwe da Taraba da Zamfara da Kaduna ma, amma Allah da ikonsa ka san irin gwamnatin da mu ke da ita ta karkashin wannan Janar Muhammadu Buhari ta na da wani al’amari na kusan tafiyar hawainiya da ta ke yi. A yayin da a ka kira hankalinsu cewa ga wani ta’addanci za a yi ko kuwa wani abu zai faru a na bukatar kafin a aikata wani ta’addanci ya zama gwamnati ta samu yadda za ta yi ta yi magani, ba a yi ba. Sai ta riga ta baci a ke yi. Mu tuntuni mu ka hango cewa, wannan bawan Allah gwamnan jihar Benuwe bai bukatar kasar nan ta zauna lafiya, saboda irin yanayinsa da lafazuzzukan da ya ke fada a bakinsa. To, daga baya da ya rasa inda zai yi, sai ya saka shugaban ’yan sanda a gaba, ya na nuna kabilanci, saboda shugaban ’yan sandan nan mutum ne wanda ya ke dan Arewa ne. ba wai da shi shugaban ’yan sandan ya ke ba; ya na so ne ya nuna cewa shugaban wannan gwamnati ai Bafulatani ne, ba ya so ya yi maganin wadannan masu kiwo da su ke cin zarafi. Kuma mu mun san cewa wannan rigima ba ma Fulani ba ne, a’a. barayi ne wadanda mafi yawa ma ba Fulanin ba ne… Kuma idan ka duba za ka ga ai an samu mutanen, amma ba Fulanin ba ne. Haka ita kanta Benuwe din ai an samu matasa da makamai. Sai su je su yi aika-aika, sai a ce Fulani ne.

 

To, amma an ce shi babban sufeton ’yan sanda ya ki ya tsaya a Benuwe ne ya tafi wajen bikin zagayowar ranar haihuwarsa a Nasarawa.

Wannan ba gaskiya ba ne. Ko a lokacin da a ka tura shi mun gani a talabijin ya je Benuwe din ya zauna da ’yan Benuwe, duk da ya ke ga cin zarafin da gwamnan ya nemi ya yi ma sa a cikin mutane. Mun ga bidiyon ai. Ya tashi kuma daga wurin; bai zauna a Makurdi ba, saboda rigimar da a ke yi ba a cikin Makurdi a ke yi ba, a kauyuka ne. kuma Nasarawan ma ai akwai rigimar a tsakanin iyakarta da Benuwe din. Nan ma a na zargin cewa ’yan ta’adda su na nan a wurin, kuma har shi gwamnan da kansa ya fada a taro. IGP Idris ya je gurin; mun gani. To, saboda haka haka a ke yin aiki, kawai ya na so ne ya zauna a gidan gwamnati tare da shi? Maganar tsaro a ke yi; shi ya san inda ya kamata ya je.

 

To, idan haka ne me ya sa shi babban sufeton ’yan sanda bai sanar da Shugaba Buhari cewa ba zai zauna a cikin Makurdi ko Benuwe tsawon lokaci ba, saboda yanayin aikin?

A’a, babu yadda za a yi a ce gwamnati ba ta san abinda ya ke faruwa ba. Magana ce ta tsaro; babu mamaki shugaban kasa ya yi wannan lafazi ne, don ya wanke kansa, saboda kar a zuba ma sa wani zargi, don da ma gwamnan ya na ta motse-motse, saboda Buhari Hausa/Fulani ne, to saboda haka sai ya je ya dauko wani mataki mai karfi a kan wadannan mutane saboda ya na ganin ’yan uwansa ne, saboda ka ga shi (Buhari) ne ainihin uban kungiyar Miyetti Allah (petron) ma na kasa. Amma babu yadda za a yi a ce IG ya na aikata wani abu ba tare da ya na mika wa shugaban kasa rahoto ba. Kada ka manta, kwana daya kafin Ranar Tunawa Da ’Yan Mazan Jiya ya je ya yiwa shugaban kasa bayanin ga abinda ya faru. Duk da ya ke ba da kwarewa ta aikin tsaro, amma a matsayinmu na shugabanni, ai mu na sa ido mu ga abubuwan da su ke faruwa a kasa kuma mu na duba inda ba a yi adalci ba.

 

To, ka na so ka ce shi Shugaba Buhari ya san shi babban sufeton ’yan sanda ba ya Binuwe din, illa dai ya fada ne don ya kare kansa?

To, ai a matsayinsa na shugaban rundunar ’yan sanda na kasa, idan a ka yi la’akari da irin abubuwan da su ke faruwa a kasa; ko’ina yanzu ba zaman lafiya, babu yadda za a yi a ce a matsayisa na IG a ce a na son ganin sa a Binuwe, a ce kuma a na son a gan shi a Taraba, a ce a na son a ji shi a Abuja, a na so a ji shi a Zamfara, duk a ce wannan bawan Allah a lokaci guda zai yi hakan, ba zai yiwu ba; shi ma shugaban kasar ya san haka. Kuma ga shi ma mu na da labarin cewa, ya yi saka wakilcin aikin ga mukaddashinsa (DIG) mai kula da ayyukan yau da kullum (Operation) ya zauna a Binuwe din a kan ya tabbatar da abinda ya ke faruwa, shi kuma ya na zagawa kasar gabadaya ya na ta aiki. To, wannan shi ne aiki, amma ba yadda za a yi a ce ya je ya nade kafa ya zauna a Binuwe kadai. Ko da shugaban kasa ya tura sojoji ya ce su tare a koma Maiduguri, ka na so ka ce min su Burutai da shugaban sojojin sama da na ruwa duka sun koma sun tare a Maiduguri ne? Ai yawo su ke yi! Amma su na samun bayanin kullum abinda a ke ciki. To, shi ma babban sufeton ’yan sandan hakan ya yi; ba wani abu ya yi daban ba. Wannan tsari ne na aiki. Idan ka ba wa mutum aiki, sai ka sa ma sa ido ka gani, ya ya zai yi nasara ko kuwa ba ya yi? Kuma a na yi; kowa ya san a na yi. Wannan shugaban ’yan sandan babu irin abinda ba ya yi. Duka idan ka duba yawan ’yan sandan na Nijeriya a na bukatar su kare rayuka da dukiyar al’umma kusan miliyan 200, amma ’yan sandan gabakidaya guda na wa su ke? Ba su wuce 300,000 da wani abu ba, kuma amma a hakan su na kokari tunda ko ta ina rigima a ke yi a kasar kuma dole ya yi yawo ya duba ya ga abinda ya ke faruwa kan rayuwa da dukiyar al’umma kafin sojoji su shigo.

 

To, amma ku kungiyar Matasan Tuntuba Ta Arewa (AYCF) ba ku tsammanin za a yi zargin ko shi babban sufeton ’yan sanda sayen ku ya yi, shi ya sa ku ke kare shi?

A’a, shi zargi da ma ai wani abu ne wanda shi da ma dan adam ya na da shi, amma duk abinda za ka yi, idan za ka yi don Allah, ba ka tunanin abinda zai biyo baya na zargi. Ai wani lokacin ba ba ma sukar ’yan sandan ba ne, saboda wasu abubuwan da su ke yi, amma a kan wannan batun babu wata maganar siyasa a ciki ko sayen mu. Ni ka ga ban taba ganin shi sufeton ’yan sandan a rayuwata ba ko lokacin da mu ka yi wadannan abubuwa, ni ban taba ganin sa ba, amma magana ce ta Allah da annabi idan za a yi ta a yi don Allah kawai. Kar mu kawo son rai cikin al’amarin nan. Harkar tsaro kada mu danganta shi da maganar siyasa. To, dole mu ba su dama, mu yi mu su uzuri, mu karfafa mu su gwiwa. Ka na nan ka na munshari su na can su na tsayawa a kan hanya su na kula da kai, don ka samu ka yi barci. Su ma fa rai ne da su. Idan babu tsaron, za mu samu mu zauna lafiya kamar yadda yanayin kasar nan ya ke ne? Ya kamata mu gode mu su wani lokacin, amma ba za mu zauna mu ce suka kawai za mu dinga yi ba, babu wata shawara ko wani taimako daga gare mu ba. Ba zai yiwu ba. Ya kamata mu gane cewa, duk yadda ’yan sanda da soja su ka kai da kokarinsu a Binuwe, idan ba ’yan Binuwe ne su ka ba su hadin kai ba, babu inda za su yi nasara kan abubuwan nan.

 

To, shugaba mun gode.

Yauwa, madalla na gode, Nasiru.

 

Exit mobile version