Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

by
4 years ago
in LABARAI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

SERAP Ta Bukaci Majalisar Dinkin Duniya Da Ta Ayyana Makiyayan Da Ke Kisa A Matsayin ‘Yan Ta’adda

Wata kungiya mai rajin kare hakkin bil adama, SERAP, ta aike da wata budaddiyar wasika zuwa ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, inda take neman majalisar da ta roki gwamnatin kasar nan da ta kawo karshen kashe-kashe da lalata dukiyoyin da wadanda ake zargin Makiyaya ne ke yi a sassan kasarnan daban-daban.

Kungiyar kuma ta bukaci wakilan majalisar Dinkin duniyar da su kawo ziyarar gani da ido a kasarnan.

Labarai Masu Nasaba

Mai Yuwa A Gaza Kawo Karshen Yaki Da Yunwa A Nijeriya Har Zuwa 2025 —Mata Manoma

Sojoji Sun Kashe 2 Tare Da Tarwatsa Sansanin Bayar Da Horo Na IPOB A Jihar Imo

Hakanan kungiyar ta roki majalisar da ta: “Ayyana Makiyayan da ke aikata wadannan munanan laifukan a matsayin ‘Yan ta’adda, kamar yadda majalisar ta yi amfani da sashen kundinta na 2349 (2017) wajen ayyana kungiyar Boko Haram a matsayin ‘yan ta’adda.

“Ayyana hare-haren na Makiyaya zai zaburar da gwamnati wajen daukan matakan da suka dace kan barazanar da Makiyayan ke yi, na aikata laifuka ga ‘yan Nijeriya da ma ‘yan adam bakidaya.

A cikin wasikar da kungiyar ta aika ranar 16 ga watan Maris 2018, wacce kuma mataimakin daraktan kungiyar ta SERAP, Timothy Adewale, ya sanyawa hannu, kungiyar ta bayyana matsanancin damuwarta kan yadda gwamnatin Shugaba Buhari ta kasa kawo karshen munanan ayyukan da Makiyayan ke aiwatarwa.

A wajen kungiyar ta SERAP, ci gaba da aiwatar da wadannan munanan ayyuka barazana ne ga zaman lafiyar yankin na Arewa da ma duniya bakidaya.

“Ya zama wajibi kwamitin na tsaro na Majalisar Dinkin Duniyar da ya yi hobbasan kare rayukan ‘yan Nijeriya da suka hada da mata da yara kanana, matukar dai ba kwamitin yana son a zarge shi ne da gazawa wajen kare mutanan Nijeriyan ba.”

SERAP din ta ce, “Hare-haren na Makiyayan ya yi sanadiyyar raba iyalai da yawa daga muhallin su, sun kuma yi barna mai yawa a cikin al’umma, inda suka hana masu hanyoyin neman abincin su, suka kuma lalata masu al’adun su. Wadannan hare-haren, suna barazana ga dalilin kafa ita kanta majalisar ta dinkin duniya. Matukar ba a tunkare su da hanzari ba, za su kai matsayin da za su kasance barazana ga zaman lafiyar duniyar ita kanta.

“Ya wajaba Majalisar ta Dinkin Duniya da wakilanta, su ayyana kowane irin aiki na ‘yan ta’adda, kamar misalin hare-haren da Makiyayan ke kaiwa a matsayin manyan laifukan yaki wadanda ba za a amince da su ba, ta kowane fanni.

ADVERTISEMENT

“Majalisar Dinkin Duniyan da wakilanta, su yi na’am, Da ayyana hare-haren na Makiyaya a matsayin ta’addanci, su kuma nemi taimakon sauran kasashen duniya ga Nijeriya wajen gamawa da masu kawo hare-haren, majalisar kuma ta tilasta wa Nijeriyan daukan matakan kawo karshen ayyukan ta’addancin na Makiyaya da ma sauran ayyukan ta’addancin da ke faruwa a kasarnan.

“Hakanan kuma, Majalisar ta Dinkin Duniya ta umurci babban Sakataren ta da ya kawo ziyarar gani da ido ta hadin gwiwa tare da babban shugaban kungiyoyin kare hakkin dan adam, na kasashen Afrika, da kuma kwamitin zaman lafiya na kungiyar hada kan Afrika domin su binciki zarge-zargen kashe-kashen da ake zargin Makiyayan da aikatawa, ta yadda za su fahimci ainihin tushen lamarin, su kuma tilasta wa Nijeriya da ta kawo karshen su.

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Gyara Sukurkutaccen Tsarin Tara Kudaden Shiga A Kasar Nan

Next Post

Shugabannin Da Suka Amfana Da Makarantun Gwamnati Sun Yi Watsi Da Su –el-Rufai

Labarai Masu Nasaba

Mai Yuwa A Gaza Kawo Karshen Yaki Da Yunwa A Nijeriya Har Zuwa 2025 —Mata Manoma

Mai Yuwa A Gaza Kawo Karshen Yaki Da Yunwa A Nijeriya Har Zuwa 2025 —Mata Manoma

by Abubakar Abba
6 hours ago
0

...

Sojoji Sun Kashe 2 Tare Da Tarwatsa Sansanin Bayar Da Horo Na IPOB A Jihar Imo

Sojoji Sun Kashe 2 Tare Da Tarwatsa Sansanin Bayar Da Horo Na IPOB A Jihar Imo

by Abubakar Abba
6 hours ago
0

...

CAN Ta Shirya Zanga-Zangar Yin Allah Wadai Da Kisan Deborah A Duk Jihohin Nijeriya

Batanci: CAN Ta Janye Gabatar Da Zanga-Zangar Da Ta Shirya Kan Kisan Deborah

by Leadership Hausa
10 hours ago
0

...

‘Yan Bindiga Sun Fille Kan Wani Dan Majalisa A Jihar Anambra

‘Yan Bindiga Sun Fille Kan Wani Dan Majalisa A Jihar Anambra

by Abubakar Abba
11 hours ago
0

...

Next Post
Mun Bar Masu Zagin Gwamnatin Kaduna Da Allah –Injiniya Namadi Musa

Shugabannin Da Suka Amfana Da Makarantun Gwamnati Sun Yi Watsi Da Su –el-Rufai

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: