• English
  • Business News
Friday, May 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hikimar Rabe Farkon Shekarar Musulunci Da Ranar Fara Aiken Manzancinsa (SAW)

by Sulaiman and Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
3 years ago
in Dausayin Musulunci
0
Saboda Girman Haihuwar Annabi (SAW) Aka Rabe Farkon Shekarar Musulunci Da Watan Haihuwarsa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Masu karatu har yanzu dai muna kan bayani game da abubuwan da suka sa Sahabbai ba su kafa tarihin kirgen shekarar musulunci ba da wasu manyan alherai na Musulunci, sai suka zabi Muharram ta zama farkon shekarar tare da lakaba mata shekarar Hijirah.

A makon da ya gabata mun yi bayani kan hikimar ware farkon shekarar daga watan Rabi’ul Auwal zuwa watan Muharram saboda girman haihuwar Manzon Allah (SAW). A yau kuma, za mu ci gaba da bayani a kan ware kirgen farkon shekarar daban da ranar da aka fara aiken Manzanci ga Annabi (SAW).

  • Mai Gadin Kabarin Manzon Allah SAW Ya Rasu

Tun ana sauran shekara uku Manzon Allah (SAW) ya cika shekara 40 da haihuwa, ya rika fita zuwa Halwa (kadaita) a wajen garin Makka a cikin Kogon Hira, mai nisan mil shida daga cikin garin na Makka.

Manzon Allah a lokacin ya bar gida, ya bar iyali, ya bar kowa domin ya kadaita da Ubangijinsa.
Wannan Kogon Hirar, lokacin da muka yi Hajji a 2004, mun ziyarci Kogon, muna yin Sallar Asuba muka fito amma ba mu kai ba sai wurin karfe takwas. Ga motoci na wucewa da komai amma kuma saboda dajin wurin ga birori ne suna ta tsalle-tsalle.

To, mai karatu ka yi tunani da kwakwalwarka, a 2004 ga wasu namun daji nan har yanzu a wurin, to ina ga in an koma sama da shekara dubu daya da dari biyar, yaya wajen nan ya kasance kenan? Amma haka Annabi (SAW) zai je wajen kuma idan ya tafi ba a kasan dutsen yake zama ba sai ya hau samansa, an bar gari, an bar iyali, an bar dangi, yanzu ma an bar kan kasa ma bakidaya.

Labarai Masu Nasaba

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa

Shi ma dutsen ba a zauna a sararinsa ba sai da aka shiga kogonsa, Subhanallah! In ka je hanyar shiga Kogon ma za ka ji kana hawaye saboda tafakurrin wadannan abubuwan na Manzon Allah (SAW).

Haka Annabi (SAW) yake zama a cikin Kogon, ya yi wata daya zuwa wata uku har sai abincinsa ya kare. Akwai ruwayar Sayyidina Aliyu (Karramallahu wajhahu) da ya ce idan abincin Manzon Allah ya kare shi yake kai masa.

Kuma ya ce tun a wannan lokacin yakan ji wani irin kamshi a wurin wanda babu irinsa a Makka. Haka Manzon Allah ya ci gaba da yi har Hakku ya yi masa tajalli fatahi ya samu.

Malaman Tafsiri kuma suka ce har Mala’ika Jibrilu ya zo masa. Ya ce masa “yi karatu”, Manzon Allah ya ce masa “ni ba mai karatu ba ne”, sai da aka yi haka sau uku kafin ayoyin nan na Suratu Ikra’a suka sauka masa (SAW). Daga nan fa sai Duniya ta yi wani irin numfashi, Manzon Allah (SAW) ya fara karantar da mu al’ummarsa da Larabci abubuwan da ya samu daga Ubanginjinsa tare da nuna mana kyawawan dabi’u.

A wannan lokacin da yake zuwa Halwa a Kogon Hira ibada ce ta Tafakkuri yake yi (Malamai sun ce da akwai wani abu da zai fi La’ilaha illallahu, zai zama Tafakkuri ne). Don haka babu wanda zai ce babu Halwa a Musulunci.

Idan dai mutum zai nemi sanin hukunce-hukuncen ibada ne, ya tafi wurin Malamai, ba zai samu wannan a Halwa ba. Amma idan zai nemi sanin wani abu mai zurfi ne na Imani to wannan sai da kebancewa (Halwa).

Yanzu mutum ya yi tunani, kafin Manzon Allah (SAW) ya kawo mana addinin nan, sai da ya bar iyali, ya bar gari, ya bar kowa ya tafi kogon dutse ya yi Halwa ta shekara uku, to wani ya zo da rana tsaka ya yi shigar burtu ya ce mana ya san komai na addinin, abin da ya ga dama shi ne mai kyau, wanda bai ga dama ba haramun ne, yaushe hankali zai kama wannan ballantana imani? Ba don Rahamar Manzon Allah da ya ce ya bar mu a hanya mai sauki ba, yaushe addinin zai samu mana. Kuma dai duk da saukin addinin yana da hawa-hawa, Islam, Iman da Ihsan.

Don haka ba komai na addini za ka ce ka sani ba, dole akwai iya gejinka na Islam, haka nan a Iman sannan ga kuma Ihsan ba adadi. Wani ma ya ce ba ilimin badini a cikin addini, yanzu Manzon Allah ya zauna ne a gida a gaban mata da yara addinin ya sauka? Ai sai da ya bar gida ya shiga Kogon Dutse ya yi Halwa. Kuma ba Manzon Allah shi kadai ba, sauran Annabawa ma haka ne.

Har gara Kogon Hira ma a kusa yake idan aka kwatanta da Dutsen Duri Sina’a, wurin da Annabi Musa (AS) ya yi magana da Allah. Cikin dajin da mutum mai tsoro ba zai iya zuwa ba, ko a yanzu dubi yadda wurin yake balle a wancan lokacin nasu.

Dubi Annabi Ibrahim, daga Isra’ila ya dauko mace da danta zai musu gida kawai amma sai da ya shafe wurin mil dubu hudu ya kawosu Makka ya ajiye. Don haka abubuwa na Annabawa da bin hanyarsu ba a sa dan karamin hankalinka a ciki.

Daga wannan Halwar ce Manzon Allah (SAW) ya zo mana da duk alheran da duniya ta sauyu da su. Larabawan da ba su iya karatu da rubutu ba suka zama Malamai.

Daulolin da suka zama suna mulkar Larabawan duk suka juya suka zama a karkashinsu, sun samu yalwa na abinci maimakon gurasa da busasshen nama kawai da suke ci a da. Ko a baya-bayan nan ma, shugaban Hadaddiyar Daular Laraba (marigayi) Bin Zayed, ya roki Shehu Ibrahim Inyass (RA) ya yi musu addu’a saboda kasarsu ba ta da komai na arziki, Shehu ya ba shi Darikar Tijjaniyya ya yi masa addu’a ya ce komai zai zo muku. Su manyan kasar sun san haka kuma wasu har yau suna rike da alkawari.

A shekarar da aka aiko Manzon Allah (SAW), shekarar giwa tana da 40, shekarar haihuwar Annabi Isah kuma tana da 611. Allah ya ba Manzon Allah Alkur’ani wanda sai dai mu dan tsakuri abin da za mu iya a cikinsa, mu dauki zahirinsa da ya yi mana magana a kan hukunce-hukuncen ibadu da sauran mu’amaloli, sai dai mu yi wanka a bakin koginsa kawai, amma fa a Kogon Hira aka debo shi, shekara uku ana Halwa dominsa duk da karfin annabta.

Allah ya ce, wannan Alkur’anin “Littafi ne da aka saukar a gare ka (SAW) don ka fitar da mutane daga cikin duffai (mai yawa), ka shigar da su haske (guda daya) da izinin Ubangijinka (abin ba zai yiwu ba in ba izinin Ubangiji) izuwa tafarkin Mabuwayi abin godiya. Shi ne Allah mai mallakar komai da komai da ke cikin sammai da kasa”.

Wannan aya sirrin aiken Manzon Allah (SAW) yana cikinta.
Wannan Alkur’ani shi ne tsarin mulkin da ya shafe kowane irin tsarin mulki duka, shi ne ya tsere wa dukkan sauran littafan da suka zo daga Allah.

Ya shafe duk wani tunani na masu falsafa irinsu Aristotle, Karl Mad, da su Bictor Couzen da Khalidr Ruhi, Nepolion, William John, duk Alkur’ani ya shafe su.

Haka nan duk wanda ba a cikin Alkur’anin ne zai yi tafakkuri ya fito da abubuwa ba, Alkur’ani ya shafe shi daga nan har tashin kiyama. Don haka mu so Allah, mai rahama ne, mai jinkai ne komai nasa mai sauki ne. Sannan duk mai son komai nasa ya yi dai-dai, ya debo a cikin Alkur’ani.

To duk da wadannan alherai na sirrin aike, Sahabbai sun ajiye kirgen shekarar musulunci ne da Hijirah saboda hikima.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Sarkin Musulmi Ya Bukaci Jama’a Da Su Fara Neman Jinjirin Watan Safar A Yau Asabar

Next Post

DA DUMI-DUMI: Rundunar Sojin Nijeriya Ta Kori Sojojin Da Ake Zargi Da Kashe Sheikh Aisami

Related

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci
Dausayin Musulunci

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

6 hours ago
Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa
Dausayin Musulunci

Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa

2 weeks ago
Ramadan
Dausayin Musulunci

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (4)

3 weeks ago
Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (3): Shari’ar Manzon Allah (SAW) Ta Zo Da Wayewa A Kowane Fanni
Dausayin Musulunci

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (3): Shari’ar Manzon Allah (SAW) Ta Zo Da Wayewa A Kowane Fanni

4 weeks ago
Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (2): Kyawawan Dabi’u Ke Fayyace Tsoron Allah A Musulunci
Dausayin Musulunci

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (2): Kyawawan Dabi’u Ke Fayyace Tsoron Allah A Musulunci

1 month ago
Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (1)
Dausayin Musulunci

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (1)

1 month ago
Next Post
Kisan Gilla: Abin Da Sheikh Aisami Ya Tambaye Ni Kafin In Ja Kunamar Bindiga Na Harbe Shi

DA DUMI-DUMI: Rundunar Sojin Nijeriya Ta Kori Sojojin Da Ake Zargi Da Kashe Sheikh Aisami

LABARAI MASU NASABA

GORON JUMA’A 16/05/2025

GORON JUMA’A 16/05/2025

May 16, 2025
Zargin Cin Zarafi: Gaskiyar Halin Da Ake Ciki A Gidan Yarin Goron Dutse

Zargin Cin Zarafi: Gaskiyar Halin Da Ake Ciki A Gidan Yarin Goron Dutse

May 16, 2025
Nijeriya Na Bukatar Dala Biliyan 10 Kowace Shekara Domin Samun Ingantacciyar Wutar Lantarki — Minista

Nijeriya Na Bukatar Dala Biliyan 10 Kowace Shekara Domin Samun Ingantacciyar Wutar Lantarki — Minista

May 16, 2025
Masu Garkuwa Sun Nemi Miliyan ₦30 Don Sako Shugaban APC A Ondo

Masu Garkuwa Sun Nemi Miliyan ₦30 Don Sako Shugaban APC A Ondo

May 16, 2025
Dalilin Tsame Daya Cikin Uku Na Ma’aikatan Ƙasar Nan A Tsarin Sauye-sauyen Biyan Haraji – Czar

Dalilin Tsame Daya Cikin Uku Na Ma’aikatan Ƙasar Nan A Tsarin Sauye-sauyen Biyan Haraji – Czar

May 16, 2025
Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

May 16, 2025
Tinubu Ya Kira Taron Manyan Kafafen Yada Labarai Kan Samar Da Wadataccen Abinci

Tinubu Ya Kira Taron Manyan Kafafen Yada Labarai Kan Samar Da Wadataccen Abinci

May 16, 2025
Abin  Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (1)

Abin  Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (1)

May 16, 2025
Rashin Tsaro Da Raba Wa Manoma Kayan Aiki Kan Lokaci Na Baraza Ga Wadata Kasa Da Abinci

Rashin Tsaro Da Raba Wa Manoma Kayan Aiki Kan Lokaci Na Baraza Ga Wadata Kasa Da Abinci

May 16, 2025
Kasar Sin Ta Yanke Shawarar Hana Taiwan Halartar Babban Taron WHO Na Bana

Kasar Sin Ta Yanke Shawarar Hana Taiwan Halartar Babban Taron WHO Na Bana

May 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.