Dakarun rundunar Sojin saman Nijeriya (NAF) da ke ƙarƙashin Operation HADIN KAI sun kashe wasu fitattun kwamandojin ƙungiyar ISWAP da mayaƙansu a wani gagarumin harin sama da suka kai a Arina Woje, wani sansanin ISWAP da ke kudancin yankin Tumbuns a jihar Borno.
Mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana cewa harin wanda aka kai ranar 27 ga Yuli, 2025, ya biyo bayan binciken sirri da suka gudanar ta amfani da na’urorin leƙen asiri da suka tabbatar da dawowar ‘yan ta’adda bayan rikici tsakanin ƙungiyoyin su daban-daban.
- Yawan Ma’aikata Ne Ya Hana Borno Fara Biyan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi – Zulum
- Za A Gudanar Da Taron Davos Na Yanayin Zafi Na Bana A Birnin Tianjin
Binciken ya nuna ƙaruwar motsin mayaƙa da kuma motsi a ɓoyayyun cibiyoyin shugabanci da wuraren ajiya a cikin dazuka, lamarin da ya tabbatar da cewa yankin ya koma sansani mai hatsari.
Dakarun NAF sun kai hari kai tsaye bisa sahihin bayanan sirri, inda suka yi amfani da makamai masu linzami wajen kai farmaki, wanda ya haifar da mummunan ɓarna a sansanin ƴan ta’addan.
Rahoton farko na kimanta ɓarnar ya nuna cewa gine-ginen da ke ɗauke da manyan shugabannin ISWAP da wuraren ajiya sun rushe gaba ɗaya, lamarin da ya daƙile shirin aiyukansu da hanyoyin samun kayayyakin aiki. Wannan na daga cikin ƙoƙarin NAF na tabbatar da zaman lafiya da hana ƴan ta’adda sake samun mafaka a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp