Hukumar yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya ICPC za ta hada hannu da Kungiyar Masu Tsaftace Sana’ar hada-hadar kudi wato (APOSUN), domin ganin ta dakile masu aikata cin hanci da rashawa da kuma zamba da kuma almundahana ta na’urar POS a fadin Nijeriya baki daya.
Daraktan Dake Kula Da Sashen Ilimantarwa Da Bin Diddigi Ayyukan Huhumar ICPC, Mista Abia Udofia ne ya bayyana haka a lokacin da ya wakilci Shuagaban hukumar ta ICPC Farfesa Bolagi Owasanya, yayin da kungiyar ta APOSUN ta kai masa ziyara a shelkwatar hukumar dake Abuja babban birnin Nijeriya.
Da yake yin maraba ga jagororin kungiyar na masu sana’ar POS mai inkiya da APOSUN, Darakatan Dake Kula Da Sashen Ilimantarwa da Bin Diddigi Dangane da Ayyukan Hukumar, Mista Abia Udofia, ya ce a shirye hukumar take wajen ganin ta yi aiki da duk wata harkalla da ake yi a sana’ar, tare da taimaka wa kungiyar ta yadda za ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin hukumomin gwamnati da ma cibiyoyi masu zaman kansu a Nijeriya.
Ya yi marhaban da lale tarea da nuna farin ciki ziyarar ta su inda ya kara da cewa, wannan tunani da ya kamata a yi la’akari da shi duba da irin yadda ake dada samun karuwar mazambata da maha’inta a kowacce fuska ta hada-hadar kudi.
A karshe ya yi wa ‘yan kungiyar fatan alheri da addu’ar samun nasara kan ayyukan da kungiyar ta sa gaba.
A nasa bangaren, Shugaban Kwamitin Amintattu Na Kungiyar ta APSUN Barasta Abdullahi Gurin, ya bayyana gamsuwarsa bisa yadda Hukumar ta Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa ICPC ta karbe su hannu bibiyu, ya kuma bayar da tabbacin ba da gagarumar gudummwa ga hukumar a kokarinta na ganin ta dakile kuruciyar bera a tsakanin al’umar kasar.
Barristan ya ci gaba da cewa, mun yunkura kan rage ayyukan ma’aikata na sace-sacen kudn gwamnati, wannan sana’ a ta POS za ta taimaka matuka wajen rage wadannan sace-sace, domin idan ma’aikaci ya zo da wata hulda da ya saci kudaden gwamnati, za mu iya ba da bayanai ko kuma mu nuna hakan ba zai yiwu ba.
“A yanzu haka dai kungiyar ta APOSUN na cigaba da kai ziyara ga masu ruwa da tsaki a fadin Nijeriya a yunkurin da take yi wajen ganin ta tsaftace sana’ar POS, nan ba da jimawa bane kuma kungiyar ta APOSUN za ta gudanar babban taronta na kasa a Nijeriya wanda zai ba ta daman gudunar ayyukanta babu kakkautawa.