Tawagar ƴan wasa mata ta Nijeriya ita ce tawagar ƙwallon ƙafa da masoya ƙwallon ƙafa a ƙasar nan suke farin ciki da ita a ko da yaushe domin a lokuta da dama tana sharewa ƴan Nijeriya hawaya a duk lokacin da suke wakiltar ƙasar nan a gasanni daban-daban na nahiyar Afirka da ma na duniya baki daya wanda hakan kuma babbar nasara ce ga harkokin ƙwallon ƙafa musamman ga matan da suke sha’awar ƙwallon ƙafa a ƙasar nan.
Nijeriya ta lashe kofin ƙwallon Afirka na mata karo na 10 bayan ta doke mai masaukin baƙi ƙasar Morocco a wasan ƙarshe da aka buga na gasar ta shekara ta 2024, wadda aka jinkirta har ta shigo wannan shekara ta 2025.
Wasan ya tashi ne Nijeriya tana da ci uku ya yin da Morocco ke da biyu bayan an kai ruwa rana a wasan da aka fafata a ƙarshen satin da ya gabata.
- Girgizar Ƙasa: Mutum 1,700 Sun Rasu, 3,400 Sun Jikkata A Myanmar
- Shekaru 15, Wasanni 535, Yaushe Kane Zai Lashe Kofi A Ƙwallon Ƙafa?
Morocco ce ta fara shiga gaba a wasan inda ta zura ƙwallo biyu tun kafin a je hutun rabin lokaci ta ƙafar ƴan wasanta Ghizlane Chebbak da kuma Sanaa Mssoudy. Sai dai bayan komawa daga hutun rabin lokaci Nijeriya ta farke ƙwallon farko ta ƙafar ƴar wasa Esther Okoronkwo kafin dagabisani Folashade Ijamilusi ta zura ƙwallo ta biyu. Kuma wannan ya nuna cewa Nijeriya ta ci gaba da riƙe kambunta a matsayin wadda ta fi nuna bajinta a tarihin gasar.
Karawar ƙarshen ta wakana ne a filin wasa na Olympic Stadium mai cin ƴan kallo dubu 21, 000 da ke birnin Rabat, a shekara ta 2022, Morocco ta zo ta biyu a gasar a wannan filin bayan ta sha kashi a hannun Afirka ta kudu. Tawagar Morocco da ke ƙarƙashin jagorancin mai horaswa Jorge ɓilda, ta so ta dauki kofin a karon farko a tarihi, sai dai hakan bai yiwu ba.
Nijeriya, wadda take ta daya a jerin ƙasashen da suka fi iya ƙwallon mata a Afirka, ta zura ƙwallon da ta ba ta nasara ne a gab da tashi wasa a karawarta da Afirka ta Kudu a wasan kusa da na ƙarshe. A yanzu za a iya cewa Nijeriya ta cimma burinta na ‘Mission ɗ’, wato lashe kofin a karo na 10 a tarihi kuma ta ci gaba da jan zarenta na tawagar mata wadda babu kamarta a wannan nahiyar.
Nijeriya ta ƙara kafa wani tarihin kasancewar ita ce ta farko da ta lashe sabon kofin na gasar bayan sauya shi da aka yi daga wanda aka saba amfani da shi a baya. A ƙarshen wasan Rasheedat Ajibade ta Nijeriya ce ta lashe kyautar ƴar wasa mafi ƙwazo a gasar ta 2024 sai yar wasan Morocco Ghizlane Chebbak, wadda ta zama wadda ta fi kowa zura ƙwallo a gasar, inda ta zura ƙwallaye biyar.
Mai tsaron raga ta Nijeriya Chiamaka Nnadozie ce ta karɓi kyautar mai tsaron raga mafi ƙwazo, inda aka zura ƙwallo a ragarta sau uku kacal tun bayan fara gasar ta wannan shekara. Ita kuwa Esther Okoronkwo ta zama gwarzuwar karawar, wannan ba abin mamaki ba ne ganin irin gudumawar da ta bayar wajen samun nasara Nijeriya. Ta zura ƙwallo daya sannan ta taimaka aka ci sauran biyun.
Baya ga kofin, Nijeriya za ta koma gida da ladan kuɗi dala miliyan daya kamar yadda hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka CAF, ta yi alƙawarin bawa duk tawagar da ta samu nasara.
Jerin ƴan Wasan Nijeriya Mata da Babu Kamarsu
Abu na farko da mutum zai fara ji game da tawagar ƙwallon ƙafa ta matan Nijeriya shi ne ta lashe kofin ƙasashen Afirka sau 10, mafi yawa kenan a tarihin gasar ga kowace ƙasa. Hakan ta sa dole ake cewa tawagar ta Super Falcons ce mafi hazaƙa a nahiyar Afirka saboda sauran nasarori da ta samu tun daga kafa ta a shekarun 1990. Gabanin gasar kofin Afirka ta 2024 a Morocco, Super Falcons ta samu gurbi ne da gagarumar nasara gida da waje a kan Cape ɓerde da ci 5-0 da kuma 2-1.
ƴanmatan na Nijeriya sun lashe kofin Afirka na Wafcon karon farko a 1998, kuma karo na ƙarshe da suka yi hakan shi ne a 2018 – kafin su lashe na ranar Asabar. Hakan na nufin sun lashe gasar sau 10 cikin 13 da suka halarta kuma babu wata ƙasa a tarihin nahiyar Afirka da ta taɓa lashe kofin nahiyar Afirka sau goma a tarihin fara kofin.
Mun yi duba a ƙasan wasu ƴan wasan Nijeriya mata da suka taka rawar gani a baya:
Perpetua Nkwocha
ƴar wasa Perpetua Ijeoma Nkwocha ƴarwasan tsakiya ce da ta yi ritaya daga tawagar ta Super Falcons a 2012. Ita ce kan gaba a ci wa tawagar Nijeriya ƙwallaye inda ta zura ƙwallaye 80 da ta zira a raga cikin wasanni 99 da ta buga. An haife ta a shekarar 1976 kuma ta ci wa Nijeriya ƙwallo huɗu a wasan ƙarshe na gasar kofin Afirka ta mata ta
2004, inda suka doke Kamaru.
Ta lashe kyautar gwarzuwar ƴarƙwallon Afirka har sau huɗu: a 2004, da 2005, da 2010, da kuma 2011. daga cikin ƙungiyoyin da ta bugawa wasa akwai Sunnanå SK ta Sweden, da kuma Clemensnäs IF inda a yanzu take horar da ƴanwasan ƙungiyar bayan ta yi ritaya.
Asisat Oshoala
ƴarƙwallon da ake yi wa kallon daya daga cikin mafiya hazaƙa a tarihin Afirka, Oshoala ta lashe kyautar gwarzuwar Afirka sau shida. ƴarwasan gaban mai shekara 30 ta fara buga wa Nijeriya wasa a watan Satumban 2013. Ta ci kofin Afirka na mata a 2014, da 2016, da 2018. A 2014, ta zama gwarzuwar gasar kofin duniya ta ƴan ƙasa da shekara 20 kuma wadda ta fi zira ƙwallaye a gasar.
Ta buga wasa a ƙungiyoyi da dama, wadanda suka hada da Liɓerpool da Arsenal da Barcelona, da dalian ƙuanjian. Yanzu tana buga wa ƙungiyar Bay FC ta Amurka. daga cikin kyautukan da ta ci akwai gwarzuwar ƴarƙwallon Afirka a shekarun 2014, 2016, 2017, 2019, 2022, 2023.
Rasheedat Ajibade
ƴar ƙwallon da ke bugawa ƙungiyar Atletico Madrid ta Sifaniya wasa, Rasheedat Ajibade ce kyaftin ɗin tawagar Nijeriya yanzu haka. ƴar wasan mai shekara 25 tana da ƙwarewar buga lambobi da dama, ciki har da gefen hagu ko dama ko kuma tsakiya. Ta wakilci Nijeriya a tawagar matasa ta ƴan ƙasa da shekara 17, da 20, kuma ta ci kofin ƙasashen Afirka na mata a 2018. An zaɓe ta matashiyar ƴarwasa mafi hazaƙa a Nijeriya a 2018.
Mercy Akide
Mercy Joy Akide Udoh tsohuwar ƴarwasa ce da ta fara bugawa Nijeriya wasa ne a shekarar 1994, yanzu tana da shekara 49, ƴarwasan tsakiya ce da ta samu nasarar lashe kofin ƙasashen Afirka karo uku a 1998, da 2000, da kuma 2002. Haka nan, ta lashe kyautar gwarzuwar ƴarƙwallon Afirka a 2004.
Francisca Ordega
Francisca Ordega mai shekara 31 na buga wasa a ƙungiyar Al-Ittihad ta Saudiyya a matsayin ƴarwasan gaba. Ta bugawa Nijeriya wasa a dukkan tawagogi tun daga ƴan ƙasa da shekara 17, inda ta buga kofin duniya a tawagar manya a 2011, da 2015, da 2019 sannan tana cikin tawagar Super Falcons da ta lashe kofin Afirka na 2010 da 2014.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp