Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayar da umarni bude ofishin jam’iyyar NNPP da ke jihar ba tare da bata lokaci ba.
An ruwaito awaito cewa da yammacin Juma’a ne, gwamnan ya umarci Hukumar Raya Birane ta Jihar ta bude ofishin.
- Martanin Wike Ga Lamido: Ba Ka Da Sauran Wata Kima A Siyasa
- Anya, Guguwar Tsige Shugabannin Jam’iyya Ba Za Ta Ci Adamu Da Ayu Ba?
Hadimin gwamnan kan Kafafen Yada Labarai, Malam Isa Gusau, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da fitar a ranar Juma’a, inda ya ce bayan gwamnan ya samu labarin rufe ofishin ne ya bayar da umarnin sake bude shi.
Zulum, ya ce ko ma mene ne dalilin daukar matakin bai kamata a rufe ofishin a wannan lokaci ba.
Cikin sanarwar, Gusau, ya ce dama al’ummar jihar na da masaniya a kan cewa tun shekaru uku da suka wuce Hukumar Raya Birane jihar ke daukar matakan kawo gyara ciki har da rufewa wasu gine-gine na musamman wadanda ba a yi su bisa ka’ida ba.
Hukumar ta ce ta dauki matakin rufe ofishin ne saboda rashin bin ka’idar da ta dace wajen bude ofishin.
Zulum, ya ce sake bude ofishin abu ne da kowa zai so sannan kuma yana da kyau a ba wa kowacce jam’iyya dama gudanar da ayyukanta ba tare da wata matsala ba.
A a ranar ne dai Alhamis ne hukumar ta rufe ofishin jam’iyyar wanda ke hade da wasu ofisoshinta.
Bayan rufe ofishin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi Allah wadai da rufe ofishin jam’iyyar da aka yi.
A cikin wata sanarwa da Kwankwaso ya fitar a shafinsa a Twitter, ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankali da kuma bin doka da oda.
An rufe ofishin NNPP ne a yayin da Kwankwaso ke shirin zuwa jihar a karshen wannan makon.