Jam’iyyar ADC a Jihar Kebbi ta dakatar da shugabanta, Injiniya Sufiyanu Bala, mataimakinsa Junaidu Muhammed Mudi, da sakatariyar jam’iyyar, Hauwa Muhammed.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Jamilu Muhammed ne, ya shaida wa ’yan jarida a Birnin Kebbi cewa an dakatar da shugabannin ne sabodarashin tuntuɓar sauran shugabannin jam’iyyar.
- ‘Yansanda Sun Fara Bincike Kan Rasuwar Wani Dan NYSC A Bauchi
- Babu Neman Afuwa Kan Nuna Goyan Bayan Tinubu Da Na Yi – Soludo
Haka kuma, ya zarge su da bai wa ’yan siyasa daga Abuja damar ƙwace ragamar jam’iyyar.
“Mun sha wahala wajen gina wannan jam’iyya, ba za mu bari wasu daga Abuja su mamaye ta ba,” in ji Jamilu.
An yanke wannan hukunci ne bayan wani taron gaggawa da aka yi tare da tsofaffin mambobi da jiga-jigan jam’iyyar.
Jam’iyyar ta naɗa Abdulrazaq Abubakar Isah Iko a matsayin shugaban riƙon ƙwarya, da Adamu Aliyu a matsayin sakataren riƙon ƙwarya har sai an gudanar da sabon zaɓe.
ADC ta gargaɗi shugabannin da aka dakatar kada su ci gaba da kiran kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar ko gudanar da harkokinta.
Haka kuma ta soke tarukan siyasa da suka shirya, tana mai cewa hakan ya saɓa wa dokar zaɓe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp