An kama tsohon Firaministan Mali, Choguel Kokalla Maïga, bisa tuhumar cin hanci, rashawa da É“arnatar da kadarorin gwamnati.Â
Wannan na zuwa ne bayan rahoton wani bincike da ya gano wasu kashe-kashe na kuɗin gwamnati ba bisa ƙa’ida ba a lokacin da Maïga yake riƙe da ofishin Firaminista da kuma jagorantar Universal Access Fund (AGEFAU).
- Allah Zai Kunyata Masu Ɗaukar Nauyin ’Yan Ta’adda – Gwamnan Zamfara
- Rangwame: Tinubu Ya Bada Umarnin Sake Bitar Tsarin Yadda Ake KarÉ“ar HarajiÂ
Rahoton ya bayyana cewa an kashe kuÉ—aÉ—en ba tare da hujja ba, kamar kashe miliyan 15 na CFA a liyafar rana guda a garin Konobougou, alhali dokar kashe kuÉ—i ta iyakance irin wannan taro zuwa 75,000 CFA.
Haka kuma an gano wasu kuÉ—aÉ—e da aka fitar don balaguro da ayyuka ba tare da hujja mai karfi ba.
Bayan fitar rahoton, an gayyaci Maïga tare da wasu tsoffin mataimakansa da suka haɗa da Issiaka Ahmadou Singaré, tsohon shugaban ma’aikata, daraktan kuɗi da gudanarwa na ofishin Firaminista, da wasu manyan jami’an AGEFAU domin yin bayani.
Lauyan Maïga, Cheick Oumar Konaré, ya bayyana cewa kamun bai dace ba saboda Maïga ba shi da niyyar guduwa ko lalata shaidu, yana kuma zargin cewa wannan wani mataki ne na siyasa saboda tsohon Firaministan ya daɗe yana sukar gwamnatin soja tun bayan tsawaita mulkinsu ba tare da gudanar da zaɓe ba.
Maïga, ya hau kujerar Firaminista a watan Yulin 2021 bayan gwamnatin sojoji ta yi juyin mulki, inda ya goyi bayan dakatar da shirye-shiryen zaɓe don bai wa gwamnatin soja ƙarin lokaci.
Sai dai daga baya ya fara sukar wasu matakan gwamnati, musamman bayan an dakatar da shi daga kujerarsa a watan Nuwamban 2024.
Tun bayan juyin mulkin 2020 da na 2021, Mali ta kasance ƙarƙashin mulkin soja, kuma ana zargin gwamnati da take haƙƙin ɗan adam da murƙushe ‘yan adawa.
A kwanakin baya ma an kama wasu sojoji bisa zargin kitsa juyin mulki.
Kamun Maïga ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar, inda wasu ke ganin matakin a matsayin wani yunƙuri na yaƙi da cin hanci, yayin da wasu kuma ke kallonsa a matsayin dabarar murjushe ‘yan adawa, musamman a wannan lokaci da ake buƙatar haɗin kai don dawo da tsarin dimokuraɗiyya a Mali.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp