Gwamna Dauda Lawal ya sake tabbatar wa jama’ar jihar Zamfara cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa yin sulhu da ƴan bindiga masu addabar jihar ba. Gwamnan ya yi wannan furuci ne a ranar Alhamis yayin ziyarar jaje zuwa wasu ƙarin al’ummar da ƴan bindigar suka kai wa hari kwanan nan.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa wuraren da gwamnan ya ziyarta sun haɗa da Kagara, Ɗan Isa da Kasuwar Daji, dukkansu a cikin ƙaramar hukumar Kauran Namoda.
- Gwamna Lawal Ya Ziyarci Yankunan Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Hari A Zamfara
- ‘Yansanda Sun Kuɓutar Da ‘Yan Ghana 19 Da Aka Yaudare Su Zuwa Nijeriya
Gwamna Lawal ya ce tun daga farko ya sha bayyana cewa ba zai taɓa shiga tattaunawa da ƴan bindiga ba, domin ba su taɓa nuna gaskiya ba. Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da mai da hankali kan tsaro a matsayin babban fifiko, tare da gyara hanyoyin da suka lalace domin amfanin al’umman da abin ya shafa.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa tana kan shiri wajen tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi, tare da ba wa jama’a tabbacin cewa za a ci gaba da ɗaukar matakai masu tsauri domin murƙushe ƴan bindiga gaba daya a jihar Zamfa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp