• English
  • Business News
Friday, September 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar Nan (6)

Fadakarwa:

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
1 month ago
in Dausayin Musulunci
0
Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar Nan (6)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Muna kira ga daukacin al’ummar Musulmi kowa ya yi tanadi na musamman kar ya bari a bar shi a baya, a bana idan Allah ya kai mu watan Rabi’ul Auwal maulidin da za a yi shi ne zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa.

Yadda abin yake shi ne, idan ka dauki shekarun haihuwar Manzon Allah (SAW) 40 kafin a fara aiko masa da manzanci ka hada da shekarun da ya yi a Makkah guda 13 bayan fara saukar da manzanci zai ba ka shekaru 53. To, idan ka hada shekaru 53 da shekarar Hijira 1446 a bara, lissafin zai ba ka cewa a baran Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1499 da haihuwa. A bana kuma zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa kenan.

  • Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)
  • Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447 Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa

Hatta wadanda ba su yin maulidi ya kamata a bana su yi kokari su yi wani abu ko yaya kar a bar su a baya, saboda yanzu idan Allah ya ja da rayuwarmu muka ga watan Rabi’ul Auwal mai zuwa lokacin da Manzon Allah zai cika shekara 1,500 da haihuwa, to zai yi wahala mu ga lokacin da zai cika shekara 2,000 kuma. Domin da wahala a samu wani daga cikin mutanen da ke rayuwa a doron kasa yanzu ya kara wasu shekaru 500 a raye.

A lokacin da Annabi Isah (AS) ya cika shekaru 2,000 da haihuwa an ga yadda duk duniya ta dauki murna, to mu ma ya kamata Musulmi mu girgiza duniya da bukukuwa na murnar mu ma Annabinmu (SAW) ya cika shekaru 1,500 a duniya. Wannan babban alheri ne da tarihi a rayuwarmu. Allah ya hore mana dukkan abun da za mu yi hidima da shi Albarkar Annabi (SAW).

 

Labarai Masu Nasaba

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

Muna Murna Da Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (1)

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Tsara Gina Birnin Madina Bayan Hijira

Masu karatu Assalamu warahmtullahi ta’ala wa barkatuh. A makon da ya gabata, mun ji irin alherai da ke cikin Hijira na daga ‘yanci da kafa kasa da gina kasa duk da sunan ‘yan kasa, da sunan Musulunci yadda Manzon Allah (SAW) da Sahabbai suka samun ‘yancinsu suka kafa kasa, suka kafa bukukuwansu irin su sallolin idi da sauransu.

A farkon dawowa Madina, akwai ‘yan kasa da aka samu wadanda ba musulmi ba, wasu Yahudawa ne, wasu Nasara, wasu Maguzawa, amma sai Annabi (SAW) ya yi tsarin zama na kasa da bai wa kowa ‘yanci don a zauna lafiya. Daga baya, daga Allah, Yahudawan suka warware alkawari, aka kori Banud Nadir da Kainuka’a, aka kashe Kuraizata saboda sun yi ha’inci, sun ha’inci kasa a lokacin yaki. Duk wanda ya yi wannan kuma, ya ha’inci Allah, ya ha’inci Manzon Allah (SAW).

Kasar da wasu ke ganin ba komai ba ce, Manzon Allah ya ce duk wanda ya ci kasar makocinsa kamu daya, ya ci har kasan bakwai, kuma za a yi wa mutum rawani da ita a jefa shi a wuta ranar tashin kiyama. Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda aka kasheshi a fagen yakin kare kasarsa Shahidi ne, ba za a ce mutum ya mutu a banza ba saboda ya mutu a kan kare kasa.

Haka nan duk wanda ya ha’inci Musulunci a matakin Islam, ko Darika a matakin Iman da Faila a matakin Ihsan, ya ba da kofa aka yi sharri, maimakon ya kare sai ma ya rika ruruta abin, to ya ha’inci Allah da Manzon Allah (SAW).

Manzon Allah ya koyar da mutane yin ado da kwalliya, akalla a yi wanka sau daya a sati kamar yadda ya nunar a ranar Juma’a. Hatta kasuwanni sai da Manzon Allah ya kakkafa cikin tsari. Wannan duk yana daga cikin albarkar Hijira saboda ‘yancin da aka samu. Sannan da rarraba aiki, masu hali su taimaki marasa shi, su kuma marasa hali kar su yi girman kai su girmama masu hali su taimake su cikin aikinsu. Manzon Allah ya zo ya tarar da ‘Yan Madina a kasarsu, da gonakinsu, sannan ga wadanda suka zo daga Makka su kuma, wadansu sun zo da wani abu (na dukiya) wasu kuma ba su zo da shi ba, sannan ga wasu ‘Yan Madina an samu sashinsu yana gaba da wani sashi. Manzon Allah sai ya cire sunan gaba a tsakanin mutanen da ke gaba da juna na Madina (Ausi, Khazraju da sauransu) bakidaya, ya sa musu sunan ‘Ansaru’ (Mataimaka), ya cire sunan ‘Yasriba’ ga kasar ya sa mata ‘Madina’. Kuma duk abin da yake jawo gaba Manzon Allah ya cire. Haka nan ya koyar da yadda za a zauna lafiya tare da wadanda ba musulmi ba a kasar. Shi ya sa duk in ka ga musulmi ya shiga wani rikici ya kauce wa karantarwar Manzon Allah (SAW), to wannan kuma sai a ce ‘La haula wa la kuwwata illa billah…’

Hadarin da ake ciki yanzu shi ne akwai wadanda suke koya wa yara sabanin abin da Manzon Allah ya koyar na zamantakewa, suna ganin koyarwar tasa (SAW) kamar sakaci ne, sai su ne za su koyar da kishin islama da fushi da zage-zage, wato a ganinsu wancan na Annabi ba kishi ba ne. Ga shi har an kai abin da aka kai yau, Allah ya gyara mana.

Mutanen Madina suka ce za su raba dukiyoyinsu biyu su ba Muhajirai, su kuma suka ce a’a, ku rike dukiyoyinku, suka zabi su yi aiki tare da su a cikin dukiyoyin suna raba ribar abin da aka samu a tsakaninsu, da haka suka iya kasuwanci kuma dama wasunsu sun iya kasuwancin tun a Makka. Sayyidina Abdurrahman bin Auf an hada shi da wani mai kudin Madina, ya ce masa zai raba dukiyarsa biyu ya ba shi rabi, ya shiga ya duba a cikin matansa ya zabi wacce ta yi masa zai saketa shi ya aureta (irin wannan sai a wurin Almajiran Manzon Allah ake gani ko Kalifansa Sahibul Faidhati). Abdurrahman ya ce masa Allah ya yi wa dukiyarka albarka, Allah ya yi wa matanka albarka (ka rike) ni dai nuna mun kasuwa kawai. Shikenan ba a dade ba bayan ya fara kasuwanci sai ga shi ya zo gaban Manzon Allah da kunshi a hannu, har ya yi kudi ya yi sabon aure.

Lallai talaka ya girmama mai shi, domin Manzon Allah ya ce talaka mai girman kai ba zai shiga Aljanna ba (ana jin kamshin Aljanna kimanin tafiyar shekara 500, amma shi ba zai ji ba, ga talauci ga girman kai ai kuma duk bala’i ya faru).

To haka ya kasance, su masu kudin ba su da rowa, su kuma talakawan ba su da girman kai da nuna butulci. Yana daga abin da Manzon Allah ya yaka; rowa, bare kuma zalunci da ba da bashi da ruwa da danniya ga talakawan kasa kullum a take su a kasa, duk Manzon Allah ya yaki wannan.

Ya ci girman Almajiran Manzon Allah (SAW) wannan Haidisin da muke ta karantawa, mu gaya wa Turawa da duk wani ma da yake alfahari da kansa. Hadisin nan da Talakawa suka zo wurin Manzon Allah (SAW) suka ce Ya Rasulallahi, masu kudi sun tafi da lada, suna sallah kamar yadda muke yi, kuma mafificin kudin nasu shi suke ba mu (sadaka). Ma’ana talakawan sun kawo kara kan cewa masu kudin suna da wani abu da suka fi su da shi a wurin Allah. Suna ibada iri daya yadda suke yi, sannan sun dara musu da sadaka. Manzon Allah sai ya ce wa talakwan ku je ku yi ta Zikiri da yawa shi ma sadaka ne, Manzon Allah ya lakana musu ‘Subhanallah…’, ai da masu kudin suka ji su ma sai suka kama yi, talakawan suka kara komawa wurin Manzon Allah suka ce abin da ka ba mu su ma masu kudin sun kama suna yi. Sai Manzon Allah ya ce “wannan falala ce da Allah yake ba wanda ya so”.

Alhamdu lillah, irin haka ‘Yan Faila Almajiran Shehu Ibrahim na gaskiya suke. Duk ibadu na Allah da talakawan ke yi su ma masu kudin suna yi. Kuma sai dai talakawan cikinsu su yi kishin darajarsu a wurin Allah (ba hassada ba). Duba dai irinsu Alhaji Maigemu Gusau, Alhaji Uba Ringim da Khalifanmu Shehu Isyaka Rabi’u, tun daga cikin kasar nan har zuwa waje za ka ji ana labarin irin alkharain da ‘Yan Failan suka yi. Dubi irin su Shehu Salisu Mu’azu da Shehu Lawal Bara’u, ga Shehu Audu Kwangila a Kaduna. Allah ya dawo da masu kudin nan a cikinmu Albarkar Annabi (SAW). Wannan duk tunatarwa ce, saboda kowa yana jin tarihin alkhairan da magatansa suka yi zai ji dadi.

Manzon Allah (SAW) ya yi hijira ba tare da ko kobo ba, haka kuma ya shiga gaba wurin aiwatar da duk tsare-tsaren gina kasa da yake shimfidawa, Daula ta ginu, Duniya ta canju. A cikin tsarin ne Manzon Allah ya gina Masallacinsa, kuma dama duk inda Musulmi yake Masallaci ne kan gaba a wurinsa. Masallacin Manzon Allah ya kasance nan ne wajen aike (na manzanci), nan ne wajen shawara, nan ne wajen haduwa da baki da sauran harkoki. Daga nan sai kuma Manzon Allah ya gina ‘yan’uwantaka wanda shi ne babban ginshikin bayan hijirar, da Muhajirai da Ansaru suka zama ‘yan’uwan juna, kuma tun daga nan abin ya game, Musulmi ya zama dan’uwan Musulmi har tashin duniya. Manzon Allah ya yi wannan domin ya tafiyar da jahiliyya da kabilanci da bambancin launin fata, ya zama babu wani abu da zai daukaka mutum ko ya kaskanta shi sai tsoron Allah. Rashin tsoron Allah shi zai kaskantar da mutum ya sa ya yi baya.

Sannan Manzon Allah ya kafa dokokin da suka kiyaye barna, suka kiyaye jinin al’umma. Haka Manzon Allah ya tafiyar da al’umma cikin tsari tare da karantar da su da Alkur’ani da Zikirai da sauran abubuwa na shiriya har Allah ya kawo zamanin Faila aka ga Zamanin Manzon Allah (SAW) a sarari. Mutanen kudancin duniya, da arewaci, da yammaci da gabashi suka narke cikin ‘yan’uwantaka na Allah. Idan mutum yana neman gaskiyar wannan ya dau Goran Faila ya karanta (idan ba ya jin Larabci sai Hausa), idan kuma yana jin Larabci ya dau Mir’wakul Ishak wanda Bayin Allah da suka riski zamanin suka rubuta. Ba su ne kadai ba akwai su da dama, amma dai wadannan su ne jagorori. Ka tsaya ka karance su da kyau zuciyarka a bude komai zai fito maka a sarari in dai ba hayaniya kake so ba. Alhamdu lillah, komai a sarari yake.

Haka nan Shehu Ibrahim littafan da ya rubuta irinsu Kashiful Ilbas da sauran hudubobinsa duk saboda tausayinsa ya saukaka bayanai ta yadda manya da kanana kowa zai gane. Ga kuma yanzu Khalifa Shehu Tijjani Inyass ya nemi Larabawa su fito da abubuwa na Shehu da ke wurinsu saboda masu tasowa da muradinsu shi ne Allah. Kuma Alhamdu lillah, ga Muhammadu Abdullahi dan Shehu Jejiba nan ya dukufa, ko zuwa yanzu ya fitar da littafan kayan Shehu sun fi 20.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Manzon Allah
ShareTweetSendShare
Previous Post

GORON JUMA’A

Next Post

An Biya Falcons Duk Kuɗin Alawus, Kyautar $100,000 Da Gidaje Ga Super Falcons

Related

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)
Dausayin Musulunci

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

8 hours ago
Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Muna Murna Da Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (1)

3 weeks ago
Kyawawan Abubuwa Da Allah Ya Yi Wa Manzon Allah (SAW) Na Girmamawa
Dausayin Musulunci

Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah

4 weeks ago
Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar Nan (7)
Dausayin Musulunci

Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar Nan (7)

1 month ago
Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)
Dausayin Musulunci

Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)

2 months ago
Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447 Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa
Dausayin Musulunci

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447 Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa

2 months ago
Next Post
An Biya Falcons Duk Kuɗin Alawus, Kyautar $100,000 Da Gidaje Ga Super Falcons

An Biya Falcons Duk Kuɗin Alawus, Kyautar $100,000 Da Gidaje Ga Super Falcons

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Na Farin Cikin Ganin Kamfanoni Suna Gudanar Da Shawarwarin Kasuwanci Da Kyau Bisa Ka’idojin Kasuwa

Kasar Sin Na Farin Cikin Ganin Kamfanoni Suna Gudanar Da Shawarwarin Kasuwanci Da Kyau Bisa Ka’idojin Kasuwa

September 26, 2025
An Gano Cututtuka Uku Da Suka Ta Da Hankalin Hukumomin Lafiya A Nijeriya

An Gano Cututtuka Uku Da Suka Ta Da Hankalin Hukumomin Lafiya A Nijeriya

September 26, 2025
Kasar Sin Ta Yi Alkawarin Bayar Da Sabuwar Gudummawa Dangane Da Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya

Kasar Sin Ta Yi Alkawarin Bayar Da Sabuwar Gudummawa Dangane Da Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya

September 26, 2025
Membobin Tawagar Koli Ta Sin Sun Ziyarci Jami’ai Da Gidajen Al’umma A Yankunan Jihar Xinjiang

Membobin Tawagar Koli Ta Sin Sun Ziyarci Jami’ai Da Gidajen Al’umma A Yankunan Jihar Xinjiang

September 26, 2025
Akwai Bukatar Sin Da Amurka Su Lalubo Hanya Mafi Dacewa Ta Tafiya Tare A Sabon Zamani

Akwai Bukatar Sin Da Amurka Su Lalubo Hanya Mafi Dacewa Ta Tafiya Tare A Sabon Zamani

September 26, 2025
Mazauna Kuyello A Jihar Kaduna Na Cikin Zullumin Bayyanar ‘Yan Ta’addar Ansaru

Gwamnati Ta Kafa Kwamitin Bincike A Kan Fashewar Wani Abu A Kaduna

September 26, 2025
An Samu Manyan Sauye-Sauye Na Zamani A Jihar Xinjiang Cikin Shekaru 70

An Samu Manyan Sauye-Sauye Na Zamani A Jihar Xinjiang Cikin Shekaru 70

September 26, 2025
Trump Ya Haramta Wa Jami’an Nijeriya Masu Cin Hanci Da Rashawa Shiga Amurka

Trump Ya Haramta Wa Jami’an Nijeriya Masu Cin Hanci Da Rashawa Shiga Amurka

September 26, 2025
Gwamnatin Kogi Ta Yi Haɗin Gwuiwa Don Fara Fitar Da Amfanin Gona

Gwamnatin Kogi Ta Yi Haɗin Gwuiwa Don Fara Fitar Da Amfanin Gona

September 26, 2025
Me Ake Nufi Da Ado? 

Me Ake Nufi Da Ado? 

September 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.