Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Nijeriya (NCAA) ta umarci dukkanin fasinjoji da su kashe wayoyinsu gaba ɗaya bayan sun shiga jirgin sama.
Darakta Janar na NCAA, Chris Najomo, ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Talata, 19 ga watan Agusta 2025.
- An Gano Karin Gawarwaki 3 Da Jirgin Ruwa Ya Kife Da Fasinjoji 26 A Sokoto
- Kasar Sin Ta Zama Jagora Mai Haskawa Duniya Sabuwar Hanyar Samun Zaman Lafiya Da Ci Gaba Ba Tare Da Nuna Fin Karfi Ba
Ya ce wannan doka ta shafi dukkanin filayen jiragen sama da kamfanonin jirgin sama a Nijeriya.
Umarnin ya biyo bayan wani rikici da ya biyo baya, tsakanin wata fasinja mai suna Comfort Emmanson da wata ma’aikaciyar kamfanin jirgin Ibom Air.
Najomo ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin kauce wa rikice-rikice da rashin fahimta a tsakanin fasinjoji da kamfanonin jirgin sama.
“A yanzu dole ne a kashe waya gaba ɗaya yayin da jirgi ke tashi ko sauka. Ba za a amince da amfani da tsarin ‘flight mode’ kawai ba. Kamfanonin jirgin sama za su canza dokokinsu kuma su gabatar da su ga NCAA don amincewa,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp