Hukumar kula da ayyukan ‘yansanda (PSC) ta ki amincewa da karin girma ga mataimakan Sufiritantandan ‘yansanda (ASPs) 179, saboda sun yi ritaya, ko mutuwa, ko kuma sam karin girman bai dace da su ba.
A cewar wata sanarwa a ranar Laraba da kakakin hukumar ta PSC, Ikechuckwu Ani ya fitar, ta tabbatar da cewa, 176 daga cikin jami’an da abin ya shafa sun riga sun yi ritaya, yayin da sauran ukun kuma tuni sun riga mu zuwa gidan gaskiya.
- Xi: Wajibi Ne A Aiwatar Da Dabarun JKS Wajen Mulkin Yankin Xizang Na Sin A Sabon Zamani
- An Tsare Tsohon Firaministan Mali Bisa Zargin Cin Hanci Da Rashawa
Ani ya kara da cewa, amma an samu nasarar karawa jami’an ASP 952 karin girma zuwa mukamin mataimakan sufiritandan ‘yansanda (DSPs).
“Hukumar ‘yansanda ta amince da karin girma ga mataimakan Sufiritantandan ‘yansanda (ASP) 952 zuwa matsayi na gaba na DSP. Hukumar ta kuma ki amincewa da karin girma ga jami’an ASP 176 da aka samu sun yi ritaya daga aiki da kuma wasu uku da sun riga sun mutu,” inji sanarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp