Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU), reshen Akure, ta gargaɗi gwamnatin tarayya da kada ta tilasta musu shiga yajin aiki sakamakon matsalolin jami’o’i ke fuskanta.
Da yake jawabi a taron manema labarai a Jami’ar Tarayya, Oye-Ekiti (FUOYE), Shugaban ASUU na jami’ar, Farfesa Adeola Egbedokun, ya ce malaman sun yi haƙuri sama da shekaru biyu ba tare da yin yajin aiki ba, suna jiran gwamnati ta cika musj alƙawura.
“Haƙurinmu ya kusa ƙarewa,” in ji shi, yana mai cewa malaman sun yi babbar sadaukarwa amma gwamnati ba ta yi abin da ya kamata ba.
Ya bayyana bukatun ASUU da suka haɗa da:
- Sake duba yarjejeniyar ASUU da Gwamnatin Tarayya ta 2009.
- Soke tsarin rancen ɗalibai na TISSF da ASUU ke ganin zai jefa ɗalibai cin bashi.
- Dakatar da kafa sababbin jami’o’i ba tare da tsari ba.
- Inganta fanshon malamai da sauran ma’aikata.
Egbedokun ya zargi gwamnati da ɓata lokaci da kuma yin alkawuran karya.
“Mun yi tattaunawar gaskiya, amma gwamnati tana yi mana wasa,” in ji shi.
Ya ce an yi watsi da rahotanni masu muhimmanci, an kafa manufofin da ke cutar da ilimi, sannan an jefa malaman da suka yi ritaya mummunan hali.
“Wannan gwamnati ta raina ilimi da malamai. Mun gaji,” in ji shi.
Shugaban ASUU ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta ƙi ɗaukar mataki, za ta ɗauki alhakin duk wata matsala da za ta biyo baya.
Ya kuma kira mambobin ASUU da su fito ƙwansu da kwarkwata wajen tarukan da za a gudanar a manyan jami’o’i a ranar Talata, 26 ga Agusta, 2025, yana mai cewa wannan shi ne mataki na farko da ƙungiyar za ta ɗauka don nuna rashin amincewa da halin da gwamnati ta shiga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp