A ranar 26 ga watan Agustan 2023, kungiyar Zauren Hausa ta Nijeriya ta jagoranci gudanar da taron Ranar Hausa ta Duniya a Jihar Kano. Taron ya gudana ne a zauren taro na Hassan da ke cikin Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a (CAS), da ke Jihar Kano.
Taron, wanda ya gudana karkashin jagorancin Farfesa Maryam Mansur Yola, mataimakiyar shugabar Kungiyar Zauren Hausa ta Kasa, ya tabo abubuwa da dama da suka shafi rayuwar Bahaushe da al’adunsa da kuma yanayin yadda yake a da da yanzu.
- An Bude Bikin Nune-Nune Na Masana’antar Manyan Bayanai Ta Big Data A Kudu Maso Yammacin Sin
- Firaministan Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Bunkasa Cinikayyar Ayyukan Hidimomi Masu Inganci
Kafin a fara gudanar da taron, Malam Abdullahi Baba Dantse ya gabatar da wasannin zaurance ga mahalarta taron, sannan ya kara bayani kan muhimmancin zaurance a harshen Hausa.
Yana mai cewa: “Da yawa yanzu an manta zaurance ko ba a yi, saboda yanayin yadda zamani yake. Amma a da, musamman ma idan ka je wajen da ka ga sun iya Hausa kuma su ba Hausawa ba ne, za ka iya juya harshe ta amfani da zaurance wajen canza yaren ba tare da wanda ka ke tare da shi ya fahimci me kake faa ba.”
Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a (CAS), Dakta Sunusi Yakubu Ahmed, ya bayyana jin dadinsa matuka bisa zabar kwalejin don gudanar da wannan taron.
Dakta Sunusi ya ce: “Tun lokacin da na ga an yi irin wannan taron a Jami’ar Northwest, na bukaci nima ina da burin ace an kawo irin wannan taron wannan kwalejin. Kuma masu shirya wannan taron sun aminta tare da kawo wannan taron nan.”
Dakta Sunusi ya kara da cewa, Hausa harshe ne wanda ya bunkasa matukar gaske ta hanyar da ya yi nisan da ba za a iya cewa ga inda harshen ya tsaya ba.
Ya ci gaba da cewa ire-iren wadannan tarukan ne ke kara fito da muhimmancin harshen a idon duniya, da kuma ga wadanda suke ganin kamar harshen ba shi da amfani.
Ita kuwa Farfesa Maryam Mansur Yola jaddada muhimmancin wannan rana ta yi ga duk wani mai amfani da harshen Hausa.
Farfesa ta ce kamar yadda aka fara bikin jiya ta hanyar bayar da horo ga wadanda suke amfani da harshen musamman a ayyukansu, kamar ‘yan jarida da masu fassara da malaman makaranta, yau kuma za a gudanar da wassanni da kuma nuna wasu daga cikin al’adun Bahaushe.
Farfesa Maryam ta bayyana dalilin da ya sa aka zabi wannan rana don mayar da ita Ranar Hausa ta Duniya, sakamakon ranar ce da aka kirkiri haruffa masu lankwasa da suka hada da ‘d, ‘b, ‘k, da sauransu, wadanda ke matukar dada wa harshen armashi.
Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi a wajen taron, akwai Hon. Sulaiman Mukhtar Ishak, dan Majalisar Jiha mai wakiltar Karamar Hukumar Madobi, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Kula da Ilimi na Majalisar Dokoki ta Jihar Kano. Ya jaddada tare da nuna muhimmancin wannan harshe.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Alhaji Sama’ila Ammani Mai Zare da Alhaji Garba Gasash, da Shugabannin Sashen Koyar da Harshen Hausa na manyan makarantun gaba da sikandire na Jihar Kano, da dalibai da malamai daga ciki da wajen jihar.
Masu wake-wake da makada sun nishadantar da mahalarta taron tare da baje basirar da Allah ya ba su ta hanyar amfani da harshen don isar da sako ko kuma bunkasa harshen.
Daga karshen taron an gudanar da wasannin dambe da langa da kuma nuna wasu daga cikin sana’o’in da Malam Bahaushe ke alfahari da su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp