Shugaban kungiyar tuntuba na masu ruwa da tsaki na Arewa, Ambasada Yerima Usman Shettima ya bayyana cewa ilimi shi ne mtakin nasarar rayuwar duniya da lahira.
Ya bayyana jin dadinsa game da hobbasar da Gidauniyar Abdullahi Maikudi ta yi wajen ganin ta tallafa wa dalibai da tallafin karatu a fanin lafiya.
Yerima, wanda shi ne babban bako na musamman a wurin taron kaddamar da ba da tallafin karatu ga dalibai 250, wanda ya gudana a filin makarantar firamare da ke Lakwaja a garin Rigasa da ke karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna.
Yerima ya bayyana cewa wannan mataki na daukar nauyin karatun dalibai a bangaren lafiya babban abin koyi ne, domin ilimi shi ne ginshikin ci gaban kowace al’umma.
Ya ce, “Ba za mu iya magance matsalolin al’umma ba sai da ilimi. Idan muka tallafa wa dalibanmu, musamman a fannin lafiya, muna tallafa wa rayuwar dubban mutane ne a nan gaba,”
Ya yaba da jajircewar Gidauniyar Abdullahi Maikudi, yana mai kira ga sauran masu kudi da kungiyoyi su yi koyi da wannan aiki na alheri. Ya kara da cewa a matsayinsa na dan arewa, ba zai daina fafutukar ganin matasa sun samu damar da za ta inganta rayuwarsu ba.
A yayin taron, daliban da aka dauki nauyin karatunsu sun bayyana farin ciki da godiya ga gidauniyar, inda suka yi alkawarin jajircewa a wurin karatunsu don su dawo su yi wa al’umma hidima. Taron ya kasance cike da nishadi, addu’o’i da kuma kira ga hadin kai wajen gina al’umma ta hanyar ilimi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp