Kungiyoyi da kuma sauran abokan arziki, ba ci gaba data taya Shugaban Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA Dakta Abubakar Dantsoho bisa zama Mataimakin Shugaban Kungiyar Tashoshin Jiragen Ruwa ta duniya wato IAPH.
Daya daga cikin su ita ce, Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa ta Kasa wato NSC wadda Sakatarenta kuma shugabanta Dakta Akutah Pius Ukeyima, ya bayyana cewa, zabar Dantsoho a mukamin hakan ya nuna salon shugabancinsa, na tafiyar da Hukumar ta NPA, musamman yadda ya mayar da hankali, wajen kara bunkasa fannin na sufurin kasar.
“Wannan nasarar da Dantsoho ya samu babban abin alfahari ne, ga kasar nan wanda kuma hakan ya nuna irin shugabanci na gari na Dantsoho ke ci gaba da yi ne, a bangaren Hukumar da kuma a bangren ruwa,” Inji Dakta Akutah.
Kazalika, Hukumar ta kuma jinjinawa Dakta Dantsoho kan samar da dabarun tsare-tsaren da suka kara saita fannin sufuri a kasar da kuma a fadin duniya.
Ya bayyana kwarin guiwarsa da cewa, shugabancin na Dantsoho, ya taimaka matuka wajen samar da damarmaki da dama a nahiyar Afirka, wanda hakan ya kuma kai Nijeriya ga wani babban mataki a bangaren sufurin Jiragen Ruwa a Afirka.
Ya kuma sanar da ci gaba da bai wa shugabancin Dakta Dantsoho goyon baya, musaman domin kara samar da sauye-sauyen da za su kara bunkasa hada-hadar zirga-zirga, da kuma a bangaren kara bunkasa kasuwancin tatalin azrki na Teku.
A nan kuma Kamfanin Rukunonin SIFAD, ya taya Dakta Dantsoho murnar zama Mataimakin Shugaban na kungiyar ta IAPH.
Hakan na kunshe ne, a cikin wata wasika da Shugaban Kamfanin Dakta Taiwo Afolabi CON ya fitar ta taya murnar, inda ya danganta zabar Dantsoho kan mukamanin a matsyin abinda ya dace, musamman duba irin salon shugabanci na gari na Dakta Dantsoho, wanda hakan ya sanya ya samar da gagarumar gudunmawa a bangaren sufurin Jiragen Ruwa na kasar.
Shugaban sashen samar da bayanai na Kamfanin Mista Olumuyiwa Akande, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.
“Wannan zaben na ka ya nuna irin kwarewar da kake da ita da kuma shekarun da ka shafe, kana yiwa Hukumar aiki wadda ta faro tun daga lokacin da ka yi aikin yiwa kasa hidima a Hukumar a shekarar 1992, inda a yanzu kuma ka kasance shugaban Hukumar ta NPA, “ A cewar Afolabi.
Ya kara da cewa, iya salon shugabanci na gari da kuma sauye-sayen da Dakta Dantsoho ya samar a hukumar, sun kara karfafa ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar.
A cewarsa, nasarorin da shugaban ya samar a Hukumar ba wai Hukumar ce kadai za ta amfana ba, har da daukacin fadin nahiyar Afirka
Kamfanin ya kuma bayyana kwarin airin Dakta Dantsoho zai yi amfani da sabbin dabarunsa na kara karfafa hadaka domin kai Afirka .
“Kamfanin na alfahari da nasarorin da ka samar da kuma ci gaba da kara ciyar da Hukumar gaba,”Inji Afolabi.
Kazalika, Kamfanin na SIFAD ya kuma kara jaddda goyon bayansa kan shiye-shiryen da Hukumar ke ci gaba da yin a kara ciyar da Hukumar gaba
Ya kuma ayyana ci gaba da yin hadaka da Hukumar ta NPA, musamman domin kara fadada gasa a bangaren sufurin Jiragen Ruwa na kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp