Dakarun runduna ta daya ta sojojin Nijeriya da ke karkashin jagorancin babban kwamandan rundunar ta daya Manjo Janar Taoreed Lagbaja, sun kashe dan ta’adda guda daya tare da kama wasu uku a Jihar Kaduna.
Daraktan yada labarai na rundunar, Birigediya Janar Onyema Nwachukwu, ne ya bayyana hakan, ya ce GOC tare da rakiyar tawagar kwamandoji da jami’an tsaro a ranar Litinin, 29 ga watan Agusta, 2022, sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda a yankunan Buruku, Udawa, Manini, Birnin Gwari, Doka, Maganda, Kuyello da Dogon Dawa a Jihar Kaduna.
- Yadda Bidiyon Tsiraicina Ya Karade Shafukan Sada Zumunta – Safara’u
- Za A Sake Jera Kwana Hudu Ana Zabga Ruwan Sama A Jihohin Arewa Biyar – NiMet
Ya ce tawagar sun yi arangama da ‘yan bindigar, inda suka fatattake su har suka yi galaba a kan ‘yan ta’addar “da karfin tsiya an yi nasarar kashe daya daga cikinsu, yayin da aka kama wasu uku da ransu, yayin da wasu daga cikin ‘yan ta’addar suka tsere da harbin bindiga.
Dakarun sun kuma kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, harsashi mai nauyin dangi 7.62 da kuma babura 18.
Don haka kakakin rundunar sojin ya ja kunnen jama’a musamman cibiyoyin kiwon lafiya da ma’aikatan lafiya da su rika lura da mutanen da za su iya zuwa neman magani sakamakon harbin bindiga da kuma kai rahoto ga hukumomin tsaro da abin ya shafa.