Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja a ranar Litinin ta jingine hukuncin da babban kotun tarayya ta yi na amincewa da Shehu Sagagi a matsayin shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Kano.
Sagagi, wanda ke samun goyon bayan tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda tuni ya fice daga jam’iyyar tare da zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP a halin yanzu.
- Sojoji Sun Kashe Dan Ta’adda, Sun Kama Wasu 3 A Kaduna
- Yadda Bidiyon Tsiraicina Ya Karade Shafukan Sada Zumunta – Safara’u
Wasu mambobin jam’iyyar dai sun jima suna zargin Sagagi da magoya bayansa da yin aikin goyon bayan mai gidansu a siyasa, Kwankwaso tare da yin saddu domin muradinsa ya cika.
A ranar 29 ga watan Maris ne kwamitin uwar jam’iyyar PDP na kasa, ya rushe shugabancin jam’iyyar a Jihar Kano tare da nada wasu kwamitin riko na mutane shida da zai maye gurbin wadanda aka rushe.
A ranar 25 ga watan Mayu, alkalin babbar kotun tarayya a Kano, Taiwo Taiwo, ya ba da umarnin hana uwar jam’iyyar PDP daga cire Sagagi a matsayin shugaba har sai wa’adin mulkinsa ya kare a watan Disambar 2024.
Hukuncin kotun ya ce uwar jam’iyyar ba ta da ikon rushe shugabannin da suka zama shugabanni ta hanyar zabe.
Sai dai kuma kotun daukaka kara a ranar Litinin, ta rushe wannan hukuncin na babbar kotun tarayya, inda ta ce lamari ne na cikin gida don haka uwar jam’iyyar tana da cikakken ikon rushe shugabannin jam’iyyar a Jihar Kano.
Kotun daukaka karar ta zartar da hukuncin cewa uwar jam’iyyar ta kasa na da ikon rushe kwamitin shugabanni jam’iyyar na Jihar Kano.
Hukuncin da alkalan kotun daukaka karar su uku suka yanke, wanda ke karkashin jagorancin Peter Ige, ta ce matakin da uwar jam’iyyar ta dauka na rushe shugabannin jiha da na kananan hukumomin Jihar Kano tare da nada kwamitin riko bai dace a kalubalanci hakan a kotu ba domin ya saba wa dokar jam’iyyar PDP.
Kotun ta ce rushe da nada kwamitin riko da uwar jam’iyyar ta yi, ya gudana ne bisa amfani da sashen dokar 31 (2) (e) na jam’iyyar.
Hukuncin na kotun na zuwa ne daidai lokacin da tsohon gwamnan Jihar Kano Ibrahim Shekarau, ya sake komawa cikin jam’iyyar ta PDP, wanda ake kyautata zaton shi ne ma zai jagoranci jam’iyyar wajen tsare-tsaren zaben 2023 a jihar.
Kazalika, ana ganin wannan hukuncin zai kawo karshen rikicin cikin gida da ke faruwa a PDP a Kano kan waye dan takarar gwamna na jam’iyyar a tsakanin Muhammad Abacha, dan tsohon shugaban kasa, Sani Abacha da Sadiq Wali.
Shi dai Muhammad Abacha an zabe shi ne a karkashin jagorancin Sagagi yayin da shi kuma Sadiq Wali dan tsohon ministan harkokin kasashen waje, Aminu Wali uwar jam’iyyar ta zaba.