• English
  • Business News
Friday, September 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnonin Arewa Sun Amince Da Kafa Ƴansandan Jihohi: Ko Hakan Zai Yi Tasiri Ga Sha’anin Tsaro?

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
6 hours ago
in Uwargida Sarautar Mata
0
Gwamnonin Arewa Sun Amince Da Kafa Ƴansandan Jihohi: Ko Hakan Zai Yi Tasiri Ga Sha’anin Tsaro?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Batun kafa Rundunar Ƴansanda mallakar gwamnatocin jihohi ya jima yana ɗaukar hankalin al’umma waɗanda ke tafka muhawarar a yi ko kar a yi da alfanu da rashin alfanun ƙiriƙiro da jami’an da manufar taimakawa wajen kawar da matsalolin tsaro da suka kasa ƙarewa.

Masu ruwa da tsaki sun buƙaci kafa ƴansandan jihohi ne saboda yadda taɓarɓarewar sha’anin tsaro a yankin Arewa ya kai ƙololuwar mataki ta yadda ‘yan ta’adda ke cin karen su ba babbaka ta hanyar yi wa al’umma kisan ƙare dangi, garkuwa da mutane, ƙone garuruwa, sanya dubun- dubatar al’umma gudun hijira da hanawa ɗimbin jama’a noma albarkatun gona.

A bisa ga rahoton ƙididdigar 2024- 2025 Rundunar Ƴansanda a Nijeriya ta na da jami’ai dubu 370, 000 tare da alwashin ɗaukar jami’ai dubu 30, 000 a kowace shekara zuwa shekaru shida a ƙoƙarin samar da ƴansanda 650, 000 a faɗin ƙasa.

  • Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi
  • Tinubu Ya Bayar Da Umarni Karya Farashin Kayan Abinci A Nijeriya

Sai dai adadin yawan ƴansanda a Nijeriya ya saɓawa shawarar Majalisar Ɗinkin Duniya na aƙalla ko wane ɗan sanda ɗaya ya riƙa bayar da kariya ga mutane 450.

Masu fashin baƙin lamurran harkokin tsaro na ganin idan har al’ummar ƙasa za su riƙa ƙorafin masu riƙe da madafun iko da yin amfani da hukumomin tsaro domin biyan buƙatun kan su, to kai tsaye gwamnoni za su yi amfani da ƴansandan jihohi da ke ƙarƙashin ikon su wajen muzgunawa abokan adawa.

Labarai Masu Nasaba

Ko Kin San… Matsalolin Mahaifa Da Suke Hana Haihuwa 

Ki Bar Auna Yadda Mijinki Yake Miki Da Yadda Wani Yake Wa Matarsa

Buƙatar Gwamnatin Tarayya ta kafa Ƴansandan Jihohi ta na ƙara samun goyon baya a bisa ga yadda mafi yawan masu ruwa da tsaki suka aminta da buƙatar domin shawo kan ƙalubalen tsaro.

Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya riga ya bayyana matsayar gwamnatinsa na cewar kafa ƴansandan jihohi ba zaɓi ba ne wajibi ne a ƙoƙarin da gwamnati ke yi na ganin ta samu nasarar ceto rayukan al’umma da dukiyoyonsu daga hannun makasa.

A kwanan nan Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta tabbatar da cikakken goyon bayan ta wajen kafa Rundunar Ƴansanda a jihohi a matsayin ɗaya daga cikin matakan kawo ƙarshen gawurtacciyar matsalar tsaro da ta dabaibaye yankin Arewa da ƙasa bakiɗaya.

Isma’il Uba Wakili, kakakin shugaban ƙungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya wanda ya bayyana hakan ya ce Gwamnonin sun riga sun cimma matsaya kan kafa ƴansandan jihohi.

Ya ce Gwamnonin Arewa 19 sun riga sun bayyana matsayarsu a lokacin da suka gudanar da taro da sarakunan gargajiya a Kaduna cewar bakiɗaya sun aminta da a kafa ƴansandan jihohi domin su shiga cikin sauran hukumomin tsaro wajen kawar da matsalolin tsaron ƙasa.

Haka ma Gwamnonin na Arewacin Ƙasa sun buƙaci Majalisar Ƙasa da ta gaggauta ɗaukar mataki kan aikin dokokin da za su ba da damar assasa sabuwar rundunar ƴansandan jihohi.

Matsayar Gwamnonin ta biyo bayan kiraye- kirayen da manyan ƙungiyoyi da dama a yankin Arewa suka yi cewar an riga an kai Arewa a bango don haka wajibi ne ta kare kan ta, daga ciki akwai ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) da ƙungiyar Dattawan Arewa. 

A kwanan nan ne ƙungiyar Dattawan Arewa ta buƙaci shugaba Tinubu da ya kafa dokar ɗaukin gaggawa kan sha’anin tsaro a Arewa a bisa ga yadda matsalar ta kasa ƙarewa.

Kwana ɗaya gabani, Gwamnonin jihohi shida na Arewa- Maso- Gabas da suka haɗa da Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe suka tattauna da Shugaba Tinubu a Abuja a inda suka yi masa ƙorafin ƙara taɓarɓarewar matsalar tsaro a yankin tare da buƙatar sake ɗaukar ƙwararan matakai.

Masu fashin baƙin lamurran yau da kullum sun bayyana cewar yunƙurin ya nuna damuwar da shugabannin Arewa ke da ita kan yadda ayyukan ta’addanci da rikicin ƙabilanci ke ci- gaba da ta’azzara a yankin tare da cin rayukan ɗimbin al’umma.

A cewar ƙungiyar Dattawan Arewa wajibi ne a bi dukkanin matakan doka wajen kafa ƴansandan jihohi kuma tilas ne ta kowace irin fuska ka da Gwamnoni su yi amfani da su ga abokan adawar siyasar su.

Da yake magana da jaridar LEADERSHIP a ranar Juma’a, Kakakin ƙungiyar Farfesa T. A  Muhammad- Baba ya bayyana cewar abin yabawa ne idan har ƴansandan jihohi za su bayar da gudunmuwa wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar al’umma. Ya ce ƙungiyar ba ta riga ta fitar da bayanai a hukumance ba, amma wajibi ne a bi dukkanin matakan da doka ta tsara.

“Batun kafa ƴansandan jihohi ya jima, amma mene ne matakan kafa ƴansandan jihohi? Ya batun kuɗin gudanarwa? Ku na ganin yadda wasu jihohi suke samun matsaloli wajen biyan albashin ma’aikata? Wane irin shiri jihohi suka yi wajen biyan ƴansandan jihohi? Mene ne zai faru idan kamar ma’aikatan jiha ba a biya ƴansandan da ke riƙe da makamai ba?”

Farfesa Tukur Baba ya ce mutane da dama sun nuna damuwa kan wasu Gwamnonin jihohi za su yi amfani da su wajen muzgunawa abokan adawa da waɗanda ke sukar su don haka ya ce wane tabbaci ake da shi cewar Gwamnoni ba za su yi amfani da su wajen biyan buƙatun su ba.

Ƙungiyar ta ce domin idan shugaban ƙasa zai ƙirƙiro ƴansandan jihohi wajibi ne domin bin dukkanin ƙa’idoji a gudanar da gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin ƙasa ta hanyar Majalisar Ƙasa.

Tun dai a watan Yuni a taron majalisar sarakunan gargajiya da gwamnonin Arewa a Kaduna suka buƙaci gwamnatin tarayya da gaggauta ɗaukar matakin tsarin dokokin da za a yi amfani da su wajen kafa ƴansandan jihohi

Shugabannin na Arewa sun aminta da cewar gagarumar matsalar tsaro da ta mamaye Arewa ta kai ƙarshen taɓarɓarewa don haka ta na buƙatar ɗaukar matakin gaggawa tare da cewar kafa ƴansandan jihohi mataki ne da bai kamata a yi watsi da shi ba.

Tuni Shugaba Tinubu ya bayyana cewar ƙirƙiro da rudunar ƴansandan jihohi ba abu ne da za a kaucewa ba a matakin da Gwamnatin Tarayya ke bi domin yaƙi da matsalar tsaron da ta zama ruwan dare, ya ce ba zaɓi ba ne wajibi ne.

Kalaman shugaban ƙasar sun biyo baya ne a yayin da ƙungiyar Dattawan Arewa suka roƙe shi da ya kafa dokar ɗaukin gaggawa kan matsalar tsaro a Arewa a bisa ga ƙaruwar ayyukan ta’addanci a yankin wanda ya durƙusar da tattalin arziki da ci- gaban Arewa.

A kwanan nan ne dai Sanata Ali Ndume ya bayyana cewar mayaƙan Boko- Haram da suka kassara Arewa Maso Gabas ba ruwan su da addini, domin su kan kai hare- haren ta’addanci ga Musulmi da Kirista da kuma waɗanda ba su yadda da duka addinan biyu ba.

Kalaman Tinubu sun faranta zukatan masu ruwa da tsaki a siyasar ƙasar nan musamman mabambantan ƙungiyoyin yankuna da ke kan gaba wajen kiran gwamnatin tarayya ta tabbatar da kafuwar ƴansandan jihohi.

Ƙungiyoyi kama daga ƙungiyar Dattawan Arewa, ƙungiyar Yarbawa ta Afenifere da ƙungiyar al’ummar Arewa ta Tsakiya duka sun bayyana buƙatar su a fili.

Da yake jawabi a fadar mulki a Abuja a yayin da tawagar ‘yan asalin jihar Katsina suka ziyarce shi a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Raɗɗa, Tinubu ya ce gwamnatin tarayya ta himmatu wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Shugaban ya jaddada kalamansa a yayin da ya tattauna da Gwamnonin Arewa- Maso- Gabas kwana ɗaya gabani a inda ya bayyana cewar akwai buƙatar tattaunawa da shugabannin majalisar ƙasa kan batun.

Shugaban ya tunatar da mahalarta taron cewar tun a watan Fabrairu 2024, Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin da zai yi nazarin abubuwan da suka kamata domin kafa ƴansandan jihohi.

A wata hira da tsohon Sufeto Janar na ƴansanda Mike Okiro ya yi da gidan talabijin na Arise ya bayyana cewar kafa ƴansandan jihohi ba shine mafitar magance matsalolin tsaro ba, ya ce ba a baiwa ƴansandan tarayya kuɗin da ya kamata.

A kan wannan Okiro ya yi gargaɗin yayatawa da amannar da aka yi cewar assasa ƴansandan jihohi zai magance ƙalubalen tsaro a Nijeriya, ya ce babbar matsalar da sha’anin tsaro a Nijeriya ke fuskanta shine rashin isassun kuɗi.

Okiro ya yi bayanin ne a yayin da Gwamnonin Arewa suka buƙaci assasa ƴansandan jihohi domin shawo kan matsalar tsaro a yankin. Ya ce ƴansandan jihohi ba shine mafitar ba.

Ya ce matsalar tsaro abu ne da ke faruwa kullum, ba wai domin ƴansanda suna a ƙarƙashin gwamnatin tarayya ba ne, sai dai domin ba a baiwa ƴansanda wadatattun kuɗaɗe, ya ce suna kuma da ƙarancin ma’aikata kuma babu kayan aiki.

A cewarsa duk da yana sane da damuwar Gwamnonin Arewa kan matsalar tsaron yankin, amma ya ce Nijeriya ba za ta iya kafa wata rundunar ƴansandan jihohi 36 a yanzu ba sai dai zuwa gaba, a mamakon hakan tsohon shugaban Yan sandan ya bayyana cewar zai fi zama maslaha a kafa ƴansandan yanki a yankuna shida na ƙasa a maimakon kafa ƴansandan jihohi.

A ɓangaren sa tsohon ɗan majalisar dattawa daga jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewar waɗanda ke yunƙurin ganin an kafa ƴansandan jihohi su shiriya fuskantar ƙalubalen samun matsalar buƙatar su.

Sanatan wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook ya bayyana cewar waɗanda ke yunƙurin kafa ƴansandan jihohi da sukar rundunar ƴansanda ta tarayya, idan har shugaban ƙasa ya aminta da buƙatar, za su gano bambancin ƴansandan tarayya da na jihohi.

Haka shi ma tsohon sakataren ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa, Anthony Sani ya nuna rashin goyon bayan sa ga kafa ƴansandan jihohi yana cewar Gwamnoni za su yi yadda suke so da jami’an a kan abokan hamayyar su.

Anthony Sani ya bayyana cewar idan har ba a baiwa ƴansandan jihohin ingantaccen horo ba, wadatattun kuɗi, kayan aiki da ƙarfafa masu ba za su yi wani abin a zo a gani ba, ya ce idan har ba a yi hakan ba babu wani ƙalubalen tsaro da za su iya magancewa.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: ArewaBuhari TinubuPoliceƳansanda
ShareTweetSendShare
Previous Post

Nijeriya Na Shirin Samun Jarin Dala Biliyan 60 A Fannin Gas – Shugaban NNPCL

Next Post

Ba Lallai Ne FIFA Ta Cirewa Afrika Ta Kudu Maki 3 Ba – Rayond Hack

Related

aure
Uwargida Sarautar Mata

Ko Kin San… Matsalolin Mahaifa Da Suke Hana Haihuwa 

2 months ago
Ki Bar Auna Yadda Mijinki Yake Miki Da Yadda Wani Yake Wa Matarsa
Uwargida Sarautar Mata

Ki Bar Auna Yadda Mijinki Yake Miki Da Yadda Wani Yake Wa Matarsa

2 months ago
Ko Kin San… Yadda Ake Magance Cutar Sanyi Ga Ma’aurata (Infection)
Uwargida Sarautar Mata

Ko Kin San… Yadda Ake Magance Cutar Sanyi Ga Ma’aurata (Infection)

2 months ago
Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)
Uwargida Sarautar Mata

Kula Da Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi

3 months ago
aure
Uwargida Sarautar Mata

Kar Ki Bari Naman Sallah Ya Kashe Miki Aure Yar’uwa

3 months ago
Arewa
Uwargida Sarautar Mata

Hanyoyi Goma Sha Daya Da Mace Za Ta Bi Domin Janyo Hankalin Mijinta

6 months ago
Next Post
Ba Lallai Ne FIFA Ta Cirewa Afrika Ta Kudu Maki 3 Ba – Rayond Hack

Ba Lallai Ne FIFA Ta Cirewa Afrika Ta Kudu Maki 3 Ba – Rayond Hack

LABARAI MASU NASABA

Gwamnan Abba Ya Gabatar Da Ƙudurin Haramta Auran Jinsi A Kano

Gwamnan Abba Ya Gabatar Da Ƙudurin Haramta Auran Jinsi A Kano

September 12, 2025
Tinubu Ya Ƙaddamar Da Shirin RenewHER, Don Magance Mutuwar Mata

Tinubu Ya Ƙaddamar Da Shirin RenewHER, Don Magance Mutuwar Mata

September 12, 2025
Ahlul Faidhati Mai Diwani Group

Yadda Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Suka Yi Maulidin Cikar Annabi (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa 

September 12, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 14 Ta Janye Sabon Harajin Man Fetur

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Ba Gwamnati Wa’adin Kwana 14 Ta Janye Sabon Harajin Man Fetur

September 12, 2025
Likitoci Masu Neman Ƙwarewa Sun Fara Yajin Aikin Ƙasa A Nijeriya

Likitoci Masu Neman Ƙwarewa Sun Fara Yajin Aikin Ƙasa A Nijeriya

September 12, 2025
Ba Lallai Ne FIFA Ta Cirewa Afrika Ta Kudu Maki 3 Ba – Rayond Hack

Ba Lallai Ne FIFA Ta Cirewa Afrika Ta Kudu Maki 3 Ba – Rayond Hack

September 12, 2025
Gwamnonin Arewa Sun Amince Da Kafa Ƴansandan Jihohi: Ko Hakan Zai Yi Tasiri Ga Sha’anin Tsaro?

Gwamnonin Arewa Sun Amince Da Kafa Ƴansandan Jihohi: Ko Hakan Zai Yi Tasiri Ga Sha’anin Tsaro?

September 12, 2025
Nijeriya Na Shirin Samun Jarin Dala Biliyan 60 A Fannin Gas – Shugaban NNPCL

Nijeriya Na Shirin Samun Jarin Dala Biliyan 60 A Fannin Gas – Shugaban NNPCL

September 12, 2025
Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi

Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi

September 12, 2025
Rashin Wutar Lantarki: Masana Sun Nuna Damuwa Kan Asarar Dala Biliyan 29 Da Ƙananan Masana’antu Ke Yi

Rashin Wutar Lantarki: Masana Sun Nuna Damuwa Kan Asarar Dala Biliyan 29 Da Ƙananan Masana’antu Ke Yi

September 12, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.