Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙaddamar da shirin RenewHER, wani shiri na musamman domin kare lafiyar mata da rage mace-mace a Nijeriya. Ya bayyana mutuwar uwa a matsayin “abin kunya ga ƙasa” da dole a kawo ƙarshenta.
A yayin bikin ƙaddamarwa a fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a daren Alhamis, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Tinubu, ya ce lafiyar mata ginshiƙi ce ga ci gaban Nijeriya. Ya bayyana RenewHER a matsayin ginshiƙin haɗin gwuiwa tsakanin gwamnatin tarayya, da gwamnoni, da kuma ƙungiyoyin mata da sauran masu ruwa da tsaki.
- Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi
- Ganawata Da Macron Ta Yi Amfani – Tinubu
Shirin zai kafa ofishi na musamman na Fadar Shugaban Ƙasa kan lafiyar mata, tare da kafa cibiyar National Women’s Health Digital Hub da ke amfani da fasahar AI wajen yaɗa bayanai kan lafiyar uwa, da matasa, da rigakafi da kuma haɗa kiwon lafiya da ci gaban tattalin arziƙi.
Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zama “katanga da kuma ƙarfafawa” ga duk wasu shirye-shirye har sai RenewHER ya samar da ingantaccen sakamako a faɗin Nijeriya. Ya ce: “Mun ɗauki alƙawarin ba kowace yarinya alƙawarin makoma mai kyau da tabbatar da rayuwa cikin ƙoshin lafiya.”
Shugabar ƙungiyar Matan Gwamnonin Nijeriya, Hajiya Olufolake AbdulRazaq, ta ce RenewHER hujja ce ta jajircewar gwamnati wajen inganta rayuwar mata. Ita da wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya kan harkokin mata a Nijeriya, Ms. Beatrice Eyong, sun yaba da shirin a matsayin sabon salo da ke bai wa lafiyar mata muhimmiyar gudummawa wajen haɓaka tattalin arzikin ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp