Babbar jam’iyar adawa ta PDP ta ƙaddamar da kwamitin gudanar da taronta na ƙasa mai mambobi 119, insa shugabannin jam’iyyar suka yi gargaɗin cewa ba za su sake lamintar wani yunƙuri ya ruguza taron ba.
Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum da shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, Bala Mohammed da shugaban kwamitin amintattu da tsohon shugaban majalisar dattawa, Adolphus Wabara, sun tabbatar da cewa jam’iyyar ta shirya tunkarar gudanar da taronta na ƙasa ba gudu ba ja dawa.
- PDP Ta Zama Fanko, Ta Rasa Komai– Dele Momodu
- 2027: Idan Kana Son Tarwatsa PDP, To Ka Dawo Da Peter Obi – Wike
Sai dai kuma ɓangaren ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya fitar da sabbin sharuɗɗa kafin gudanar da babban taron jam’iyyar da zai gudana a ranar 15 da 16 ga Nuwamba, 2025, wanda aka tsara za a yi a garin Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo.
PDP ta tsinci kanta cikin rikici tun bayan gudanar da zaɓen fid da gwani na shugaban ƙasa a 2023, wanda ya fitar da tsohon mataimakin shugaba ƙasa, Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.
Bayan fitowar Atiku, wanda ya zo na biyu ya kasance gwamnan Jihar Ribas a lokacin, Nyesom Wike, ya samu goyon bayan wasu daga cikin gwamnonin abokansa, ciki har da Samuel Ortom (Benuwai), Seyi Makinde (Oyo), Ifeanyi Ugwuanyi (Inugu), da Okezie Ikpeazu (Abiya). Wanda suka kafa ƙungiyar G-5 don yin aiki tare wajen yaƙar Atiku.
Wike ya goyi bayan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a wani mataki da ya samu matsayin ministan Babban Birnin Tarayya Abuja.
Duk da yake har yanzu shi mamba ne na PDP, Wike ya kasance yana bayyana cewa zai ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar yayin da yake kuma yin aiki don sake zaɓen Tinubu, wani matsayin da yawancin mambobin PDP ba sa jin daɗinsa.
Kafin yanzu, jam’iyyar ta shiga cikin wata babbar matsala kan matsayin sakatare jam’iyyar na ƙasa, tsakanin Samuel Anyanwu, wanda Wike yake goyo baya, da Sunday Ude-Okoye, wanda yake samun goyon bayan Gwamnan Jihar Inugu, Peter Mbah.
Mafi yawancin shugabannin jam’iyyar sun yi tunanin cewa idan har Anyanwu ya dawo a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa zai kwantar da hankalin Wike. Amma kafin babban taron na Ibadan, ministan Abuja ya fito da sabbin sharuɗɗa.
Vangaren magoya bayan Wike sun gudanar da taro tare da shimfiɗa sabbin sharuɗɗa ta yadda za a iya gudanar da taron cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Cikin waɗanda suka halarci taron sun haɗa da tsofaffin gwamnonin, Samuel Ortom (Benuwai), Ifeanyi Ugwuanyi (Inugu), Ayo Fayose (Ekiti) da Okezie Ikpeazu (Abiya), da sakataren jam’iyyar na ƙasa, Anyanwu.
Vangaren ya kafa sharaɗin cewa dole ne shugaban jam’iyyar na ƙasa ya fito daga yankin arewa na tsakiya bisa ga tsarin rabon muƙamai na yankuna na taron 2021.
A cewar ɓangaren, rashin bin ƙa’idojin da aka ambata zai sa tsarin babban taron ya ruguze ya zama mara inganci, saboda za a samu rarrabuwan kawuna a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.
Sauran sharuɗɗan sun haɗa da yin kiran gaggawa ga kwamitin gudanarwa na ƙasa don gudanar da sabbin zaɓen shugabanni a jihohin Ebonyi da Anambra bisa ga hukuncin kotu da gudanar da sabon taron jam’iyyar na yankin kudu maso gabas da tabbatar da sakamakon taron kudu maso kudu da aka gudanar a Kalabar na Jihar Kuros Ribas, wanda kotu ta riga ta tabbatar da shi da kuma gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi na Jihar Ekiti cikin gaggawa bisa ga hukuncin kotu.
Amma yayin da yake magana a wajen ƙaddamar da kwamitin shirya taron mai mambobi 119 a hedkwatar PDP a Abuja, shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, Bala Mohammed ya bayyana cewa ba za su ci gaba da yin shiru ba suna barin wasu mutane suna lalata musu jam’iyyar.
Ya yaba da jagorancin Damagum da ingancin kwamitin taron, yana cewa, “Babu shakku kan ƙarfin wannan shugabancin. Sun yi hakan a baya, kuma muna ganin za su yi iya bakin ƙoƙarinsu. Gwamnonin PDP suna tare da sauran ‘ya’yan jam’iyyar nan wajen jagoran wannan kwamitin.
Da yake jawabi kan wannan dambarwar, masanin harkokin siyasa, Farfesa Kamilu Sani Fage ya gargaɗi cewa PDP na fuskantar wata matsala idan ba ta ɗauki matakan gaggawa wajen magance buƙatun Wike ba.
Ya ce Wike ya zama ƙarfan ƙafa a cikin jam’iyyar, domin yana iya bayar da umurni bisa irin gina mabiyansa, inda ya ce waɗannan sabbin sharuɗɗan da ya gindaya sun saɓa da tsarin dimokuraɗiyya.
Fage ya ƙara da cewa Wike yana ta yaƙar PDP tun daga 2023 ta hanyar tallata Tinubu, karɓar muƙamin minista a gwamnatin APC, da kuma raunana PDP a ƙasa da kuma a Jihar Ribas.
Ya gargaɗi cewa “Jam’iyyar tana buƙatar tabbatar da ladaftarwa. Babu wanda ya mallaki PDP. Idan suka bar Wike ya ci gaba, zai haifar da babbar matsala.”
A cewarsa, PDP na fuskantar haɗarin maimaita taron 2015, idan ba ta ɗauki mataki ba. “Idan tana son ta tsaya da ƙafarta, dole ne ta ɗauki matsaya mai ƙarfi. In ba haka ba, abin da ya faru a 2015 na iya maimaituwa a 2027.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp