An ƙiyasata cewa, Nijeriya na yin asarar kimanin dala biliyan 10.5, na samun kuɗaɗen shiga daga fitar da kashin dabbobi zuwa kasuwannin duniya, musamman saboda rashin samar da kyakkyawan tsari na ƙasa da kuma kayan aiki.
‘Nagar kimiyya ta Science Direct’ ta bayyana cewa; kashin dabbobi na ɗauke da wasu sinadarai kamar na ‘nitrogen, phosphorus da kuma na potassium’.
Kazalika, ƙungiyar ‘Trendset Ɓisionaries’ ta ayyana matsayin kashin dabbobin, wanda ya kai dala biliyan 10.5; har ila yau kuma ta ƙara da cewa; zai iya zarcewa zuwa dala biliyan 18.3 a shekarar 2030.
Sai dai, an bar Nijeriya a baya wajen kai kashin dabbobin zuwa kasuwannin duniya, musamman duba da cewa; ƙasashe a nahiyar Asiya da tarayyar Turai da Ƙasar Amurka, tuni suka yi nisa, wajen sarrafa kashin dabbobin zuwa takin zamani da sauransu.
- Shettima Ya Bada Umarnin Gaggauta Raba Lamunin Naira Biliyan 250 Ga Ƙananan Manoma
- Nazari Kan Bukatar Manoma Su Rika Yi Wa Mangwaro Ban-ruwa
Haka nan, Ƙasar China a faɗin duniya, ita ce kan gaba wajen sarrafa kashin dabbobin zuwa takin zamani, inda rahotanni suka bayyana cewa; ƙasar ta China na samar da aƙalla a duk shekara tan biliyan 3.8 na takin zamani da ta samar daga Kashin dabbobi da kuma na kashin kaji.
Duk da cewa, Nijeriya ce kan gaba wajen kiwon dabbobi a nahiyar Afirka, amma har yanzu, mahukunta a ƙasar sun gaza gudanar da wani kyakkyawan tsari da kuma samar da kayan aiki wajen samar da kashin na dabbobi, inda rashin hakan ke ci gaba da haifar da damuwa ga waɗanda ke fannin a faɗin ƙasar.
“Nijeriya za ta iya samun daloli masu yawa a kasuwar ta duniya”, a cewar Chuka Mordi Babban Jamie’s kamafanin Ellah Lakes kuma wanda ya kasance ɗaya daga cikin masu goyon bayan ganin ana fitar da kashin dabbobin zuwa kasuwannin duniya, domin yin hada- hadar kasuwancinsa.
“Kashin dabbobin ya kasance ɗaya daga cikin hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga, musamman wajen sarrafa kashin dabbobin zuwa takin zamani, domin ƙara inganta ƙasar yin noma da kuma amfanin gonar da aka shuka,” in ji Chuka.
Mordi ya ci gaba da cewa, rashin cin gajiyar da ba a yi na kashin dabbobin a ƙasar nan, hakan na ci gaba da haifar da giɓi ga fannin.
“Akwai buƙatar sassan koyar da darussan aikin noma da ke jami’oin ƙasar nan, su sanya darasin koyar da muhimmancin yin amfani da kashin dabbobin a cikin manhajarsu, domin a bunƙasa fannnin”, a cewar Mordi. Kazalika, ya yi kira ga gwamnati da ta samar da wasu shirye-shirye, musamman domin a ilimantar da manya da ƙananan manoma da kuma ƴ an kasuwa, kan albarkar da ke tattare da kashin na dabbobin.
“Ga ƙasa kamar irin Nijeriya da ke ƙoƙarin ganin ta rage yin dogaro daga fannin man fetur, idan ta mayar da hankali, za ta iya amfana da wannan fannin,” Inji Mordi.
Bugu da ƙari bisa wasu alƙaluma da hukumar kula da ƙididdiga ta ƙasa wato NBS ta fitar sun bayyana cewa, a Afirka ta Yamma, Nijeriya ce, kan gaba da ke da Shanu masu ɗimbin yawa, inda a ƙasar ake kiwata Shanun da yawansu ya kai miliyan 20.79.
Kazalika, ƙasar na da sauran dabbobi dasuka haɗa da, Tumaki da Akuyoyi da sauarsu.
Sai dai, duk irin waɗannan ɗimbin dabbobin da ƙasar ke da su, da kuma kasancewar ƙasar kan gaba wajen albarkatun dabbobi a Afirka ta Yamma, amma mahukuntan ƙasar, sun gaza samar da wani kyakaywan tsari na cin gajiyar da ke tattare da Kashin na dabbobin.
Albarkatun da ke cikin ƙashin dabbobi da Jininsu da kuma kashin nasu, za a iya juwa su zuwa wasu sinadarai da dama.
A cewar hukumar NBS, a kullum a Jihar Legas kaɗai, ana yanka Shanu da yawansu ya kai daga 3,000 zuwa 5,000.
Wannan adadin, ba su daga cikin dubban da aka yankawa, ba tare da yarjewar mahukunatan jihar ba, amma duk da hakan, ba a cin gajiyar alfanun da ke tattare da Kashin na dabbobin.
Sunny Omokaro, shugaban ƙungiyar ma’aikatan mahauta na ƙasa, ya sanar da cewa, wannnan rashin ci gajiyar ta Kashin dabbobin, ya sanya Nijeriya rashin samun damarmaki masu yawa.
“Sarrafa kashin dabbobin, zai taimaka wajen ƙara samar da ayyukan yi da samar da kuɗaɗen shiga“ Sunny ya shaida wa jaridar BusinessDay hakan.
Ya buga misali da ƙashin dabbobin, wanda ya ce; za a iya sarrafa shi zuwa abincin dabbobin da sauransu.
Ya sanar da cewa, rashin samar da kayan aikin sarrafa kashin dabbobin zuwa wasu nau’ika, na ƙara haifar wa fannin wani sabon ƙalubale.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp