Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal na jihar Zamfara ya sayo kayan koyo da koyarwa har guda 408,137 domin rabawa ga makarantun gwamnati a faɗin jihar.
An gudanar da bikin rabon ne a ranar Juma’a a Cibiyar Horar da Malamai ta TTDC da ke hanyar Bypass a Gusau.
- Tinubu Bai Shirya Yin Gaskiya A Zaɓen 2027 —Buba Galadima
- Ko Me Ya Sa Jihar Xinjiang Ta Kasar Sin Ke Kara Janyo Hankalin Al’ummun Duniya?
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa rabon bai tsaya ga littattafai kaɗai ba; an shi ne domin tabbatar da Zamfara ta hau kan turbar farfaɗowa, sabuntawa, da ci gaba ta hanyar ilimi.
Sanarwar ta ƙara da cewa, an bayar da ƙarin kayayyakin da za a raba a matsayin tallafin ne daga Hukumar Kula da Ilimi ta Duniya (UBEC) da UNICEF.
A jawabinsa a wajen taron, Gwamna Lawal ya sake nanata cewa gwamnatinsa ta zo ne da aikin ceto da sake gina jihar.
Ya ce: “Tun da farko mun gane cewa hanya mafi inganci wajen dawo da Zamfara kan turba ita ce saka hannun jari a zukatan al’ummarmu.
“A yau, a cikin wannan alƙawari, na yi farin cikin sanar da raba kayayyakin koyo da koyarwa 408,137 da gwamnatin jihar Zamfara ta sayo kai-tsaye.
“Wannan shi ne ɗaya daga cikin mafi girma na zuba jari a cikin albarkatun koyarwa da jiharmu ta taba gani. Ya nuna imanin mu cewa malamai ba za su iya yin nasara ba tare da kayan aikin da suka dace ba, kuma yara ba za su iya koyo ba tare da isassun kayan karatu ba.
“Amma wannan ƙoƙarin ba namu kaɗai ba ne, muna godiya tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Ilimin Bai-ɗaya (UBEC), wadda ta samar da kayayyakin koyo da koyarwa 77,609 domin ƙara wa shirin gwamnatin jiharmu.
“Gudunmawar da suke bayarwa ta nuna cewa ana samun ci gaba mai kyau idan gwamnatoci a matakai daban-daban suka yi aiki tare, tare da haɗin kan jama’a.
“Muna gode wa abokan aikinmu na ci gaba, musamman UNICEF, da suka samar da littattafai masu muhimmanci 5,000. Waɗannan litattafan za su ba yaranmu ilimi mai muhimmanci na muhalli da kuma ilimin tattalin arziki, tare ba su ƙarin haske kan yadda duniya take da canjin yanayi.
“Kowanne daga cikin waɗannan kayan da jihar ta sayo, da gudunmawar UBEC, da tallafin UNICEF, na da ma’anarsa. Amma tare, sun ba da labari ɗaya mai ƙarfi, Zamfara ta zabi hanyar ilimi a matsayin ginshiƙin sake gina al’umma.”
Gwamna Lawal ya kuma yaba wa malaman Zamfara bisa sadaukarwar da suke yi a fannin ilimi.
“Dole ne na ɗauki lokaci don yaba wa malamanmu, babu wani abin da zai iya maye gurbin sadaukarwar malamin da ke zaburar da ɗalibai a kullum. Waɗannan albarkatun da muke rarrabawa za su kasance masu ma’ana ne kawai idan an yi amfani da su sosai ta hanyar masu sha’awar ilmantarwa.
“Ga iyaye, don Allah ku gane muhimmiyar rawar da ku ke takawa a ilimin yaranku. Littafi shi kaɗai ba ya isa ba tare da ƙarfafawa a gida ba. Ilimi yana farawa ne daga gida, tarbiyya da jagoranci ke kafa tushen nasara. Ina roƙon ku da ku bai wa makaranta muhimmanci, kula da ayyukan ilimi, kuma ku tunatar da yaranku cewa makomarsu ta dogara ne akan sadaukarwarsu wajen koyon karatu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp