Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirye-shiryen zuba hannun jari a bangaren aikin noma na kimanin dala biliyan 3.14.
An aiwatar da shirin ne a karkashin hukumar kula da abinci da ayyukan noma ta majalisar dinkin duniya (FAO), zuba hannun jairin zai mayar da hankali a fanonin noman tumatir, rogo, masara, madarar shanu da kuma kiwon kifi.
- Ana Fatan Majalisar Wakilan Amurka Za Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Raya Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
- Nazari Kan Littafin Baba Zube Na 5 (Gwamnati)
Babban Ministan Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya sanar da hakan ne a taron zuba hannun jari da ya gudana a Abuja.
Ya ce, gwamnatin tarayya za ta bayar da dauki na dala biliyan 1.75, inda kuma masu zaman kansu a fannin, za su bayar da dala biliyan 1.39.
“Za a gudanar da aikin ne da nufin tsamo miliyoyin ‘yan kasar nan daga talauci, samar da ayyukan yi, bunkasa samar da abinci mai gina jiki da sauran makamantansu,” in ji Kyari.
Har ila yau, ya kara da cewa; kudaden shigar da za a samu, za su karu zuwa dala 657, inda kuma za a kara samun sama da tan miliyan 1.2.
Ya ci gaba da cewa, albarkatun da Nijeriya ta ke da su, kashi 20 a cikin dari ne kacal na miliyoyin hektar noman da ake da su a wannan kasa ake nomawa, wanda kuma na hektar noman rani ta haura miliyan uku.
Ministan ya kuma sanar da cewa, bisa sauye-sauyen da ake ci gaba da samar wa bangaren shiyoyin sarrafa amfanin gona don samun riba, samar da kayan aiki da kudden aikin noma da bankin manoma ke yi da sauransu.
Kyari ya kuma bai wa masu son zuba hannun jarin tabbacin samar musu da kyakkyawan yanayi, domin samun cin nasarar abin da aka sanya a gaba.
Shi kuwa, wakilin FAO a kasar nan Hussein Gadain, ya yaba wa gwamnatin; kan kokarin da take ci gaba da yi a shirin muradan karni wato SDGs.
Ya kuma jinjina wa salon shugabanci na mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, wajen janyo masu zuba hannunn jari da samar da dabarun zamani.
Shi kuwa, jakadan tarayyar turai a kasar nan, Gautier Mignot, ya nanata ci gaba da bayar da goyon bayan Tarayyar Turai, wajen yin hadaka da kasar nan.
Ya ce, ko a kwanan baya, tarayyar turai, ta zuba hannun jarin da ya kai na Fam miliyan 80 a jihohi bakwai da ke kasar nan.
A cewarsa, wannan hadakar za ta taimaka wajen kara karfafa bunkasa fannin aikin noman wannan kasa baki-daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp