Majalisar Shura ta Jihar Kano ta sanar da cewa za ta fara bincike kan zargin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da aka yi wa shahararren malamin addini, Malam Lawan Shuaibu Abubakar Triumph, bayan karɓar ƙorafe-ƙorafe daga gwamnatin jihar.
Sakataren Majalisar Shura, Shehu Wada Sagagi, ya bayyana haka a taron manema labarai ranar Juma’a cewa kwamitin da Waliyan Kano ke jagoranta zai gayyaci masu ƙorafe-ƙorafe da kuma Malam Triumph domin sauraron bayanansu. Ya ce matakin zai baiwa kowanne ɓangare dama kuma za a bi ƙa’idojin shari’ar Musulunci wajen gudanar da binciken.
- NECO 2025: Gwamnan Kano Ya Bayyana Bayanai Ba Daidai Ba
- Trump Ya Haramta Wa Jami’an Nijeriya Masu Cin Hanci Da Rashawa Shiga Amurka
Masu ƙorafin sun zargi malamin da yin kalaman da ba su dace ba kan Annabi Muhammad (SAW), ciki har da maganganu kan yanayin jikinsa, da haihuwarsa, da kuma batutuwa da suka shafi iyayensa. Sai dai Sagagi ya jaddada cewa a halin yanzu waɗannan duka zargi ne kawai, kuma bincike zai fayyace gaskiya.
“Za mu gayyaci masu ƙorafin su yi ƙarin bayani, sannan Malam Triumph ma zai sami damar kare kansa. Kwamitin zai bi tsari bisa ga shari’ar Musulunci,” in ji Sagagi.
Ya ƙara da cewa duk da rahotannin da ke cewa wasu na shirin kai ƙara kotu, Majalisar Shura za ta tsaya ne kan aikinta na shari’a. Ya kuma yaba wa gwamnatin Kano bisa kawo al’amarin gaban majalisar, wadda ya ce ta ƙunshi fitattun malamai masu zurfin ilimin shari’ar Musulunci.
Sagagi ya roƙi jama’a da su zauna cikin kwanciyar hankali, tare da jaddada muhimmancin kiyaye zaman lafiya da Kano ta shahara da shi a Arewa maso Yamma. Ya tabbatar da cewa majalisar za ta yi bincike da tattaunawa kafin ta baiwa gwamnati shawara kan matakin da ya dace bisa ga ƙa’idar shari’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp