Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa tlTa’annati (EFCC), ta cafke shugaban majalisar dokokin Jihar Ogun, Olakunle Oluomo.
Jami’an EFCC sun kama shugaban majalisar ne ranar Alhamis da misalin karfe 9 na safe a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Jihar Legas.
- An Kashe ‘Yan Boko Haram 49 A Sansaninsu 3 Yayin Luguden Wuta Ta Sama
- 2023: Rashin Halartar Osibanjo, Lawan, Amaechi Ya Janyo Dakatar Da Zaman Sulhun APC
Rahotanni sun ruwaito cewa jami’an EFCC sun kama shugaban majalisar dokokin ne domin ya amsa wasu tambayoyi da ke da alaka da almundahanar kudade.
Shugabancin hukumar kawo yanzu ba su ce komai abkan lamarin ba, amma dai ana sa ran zabsu fitar da sanarwa nan babda jimawa ba.
Wata majiya dabke da alaka da hukumar EFCC ta bayyana cewa, hukumar ta gayyaci kakakin majalisar lokuta da dama amma ya gaza amsa kiranta.
Yanzu haka dai sun tafi da Oluomo zuwa ofisoshin hukumar EFCC da ke Legas domin yi masa wasu tambayoyi.
Yanzu haka dai majalisar dokokin Jihar Ogun hankali ya kwanta bayan da jami’an hukumar na EFCC suka kama jakakin majalisar.
Duk da al’amarin ya lafa, har yanzu dai kofar da ake shiga harabar majalisar na nan a rufe, yayin da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya wato Civil Defense suka yi wa kofar shiga tsinke.
Haka zalika, an hana shiga harabar majalisar yayin da masu ziyarar da ke ciki da wajen majalisar suka koma baya.