Kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ta musanta rahotannin da kafafen yada labarai suka yada cewa an kai wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP hari a garin Lokoja a Jihar Kogi.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na Kwankwaso, Barista Ladipo Johnson, a ranar Alhamis, ta ce rahotannin da ke nuna cewa an kai wa Kwankwaso harin “karya ne, sannan ba su da tushe kuma abin dariya ne.
- EFCC Ta Cafke Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ogun
- An Kashe ‘Yan Boko Haram 49 A Sansaninsu 3 Yayin Luguden Wuta Ta Sama
Johnson ya ce Kwankwaso bai fuskanci komai ba face soyayya daga mutanen Jihar Kogi a ziyarar da ya kai jihar.
Sanarwar ta ce, “An jawo hankalinmu ga rahotanni da dama da kafafen yada labarai suka rika yadawa, wadanda ke nuni da cewa an kai wa ayarin motocin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP hari a Jihar Kogi.
“Muna so mu bayyana a fili cewar wadannan labaran karya ne, sannan marasa tushe ne kuma abin dariya.
“Tun da ya isa jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bai samu komai ba face soyayya daga mutanen Jihar Kogi, a ranar Laraba ya ziyarci iyalan abokinsa tsohon gwamnan Jihar Kogi, marigayi Prince Abubakar Audu a wajen taron. Daga nan ne ya zarce zuwa tsakiyar birnin Lokoja domin kaddamar da sabuwar hedikwatar jam’iyyarsa ta jiha.
“Muna so mu bayyana cewa a tsakanin wadannan wurare guda biyu, ayarin motocin dan takarar shugaban kasa babu wani abu da ya same su.
“Bugu da kari, sabanin yadda kafafen yada labarai ke yadawa kan harin da aka ce an kai mana, muna tabbatar da cewa babu wani mai suna Musa Yunusa a cikin tawagar Kwankwaso, saboda haka wannan lamari bai faru ba.
“Kungiyar Kamfen din Kwankwaso na kokarin gurfanar da dan jarida da kuma kafar da suka yada wannan labari.
“Muna kuma kira gare su da suke tabbatar da duk wani labari da ya shafi Rabi’u Musa Kwankwaso, ta bakin masu magana da yawun yakin neman zabensa, su kuma daina yaudarar jama’a, musamman a irin wannan mawuyacin hali.