Shugaban Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA Dakta Abubakar Dantsoho ya bayyana cewa, a rabin farkon zangon na shekarar 2025, Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar, sun bayar da gudanwar wajen samun karuwar da ta kai kaso 19.6 a bangaren fitar da kayan da ba su shafi fannin Mai ba.
Kazalika, Dakta Dantsoho ya sanar da cewa, Hukumar ta NPA na kan kokarin ganin cewa, ta samar da tsarin gudanar da yin gasa ta kasa da kasa, musamman domin a kara karfafa gudanar da hada-hadar kasuwanci tare da janyo ‘yan kasuwa daga ketare, da za su zuba hannun jari na kai tsaye da kuma kara karfafa masu guiwa domin dorewar tattalin arzikin kasar, a nan gaba.
- Manyan Jami’an Kasashen Afirka Suna Fatan Fadada Hadin Gwiwa Da Kasar Sin
- Xi Ya Taya Jami’ar Tianjin Murnar Cika Shekaru 130 Da Kafuwa
Dantsoho ya bayyana hakan ne, a kasidar da ya gabatar a taron Majalisar Dikin Duniya da ake ci gaba da gudanarwa a yanzu a kasar Amurka.
Taken kasidar shi ne, ‘ Kula da Kayan Aikin Hukumar Domin a kara Habaka Hada-Hadar Sufurin Jiragen Ruwa da kuma Karfafa Gasa Fadin Duniya.’
Dantsoho ya kara da cewa, a zangon farko na shekarar 2026, Hukumar ta NPA, za ta ci gaba da wanzar da tsarin na Tashar Jiragen Ruwa wato PCS.
“Muna tabbatar da inganta tsarin na PCS domin a kara tabbatar da karfafa gasa a fadin diniya a fannin na sufurin Jiragen Ruwa na NPA wanda hakan zai kuma kara samar da damar janyo masu zuba hannun jari daga waje na kai tsaye da kuma kara karfafa tattalin arzikin kasar, a nan gaba,”.
A cewarsa, za mu ci gaba da kulla hadaka domin mu cimma burin da aka sanya a gaba, na kara inganta ayyukan Hukumar ta NPA.
Ya ci gaba da cewa, a rabin zangon farko na shekarar 2025, ingancin da aka samar a bangarorin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar sun bayar da gudunmawar da ta karu, zuwa kaso 19.6 a fannin fitar da kaya waje, da ba su shafi fannin mai ba.
Kazalika, Dantsoho ya bayyana cewa, Hukumar ta NPA, na kan wanzar da tsarin haadaka na fasahar zamani wanda zai sada ya da sauran masu zuba hannun jari da gudanar da hada-hada.
A cewarsa, bisa samar da wannan tsarin na yin amfani da fasar ta zamani, hakan ya taimaka wajen gudanar da hada-hadar a cikin sauki da kuma rage yin asara.
Kazalika, Dantsoho ya bayyana cewa, Hukumar na kuma yin amfani da na’aurar zamani a daukacin harabar ginin na Tashar Jiragen Ruwan da ke a jihar Legas, musamman domin a kara rage cunkoso a Tashar.
“An sanya tsari a cikin yin amfani da na’urar zamani ta ECS wanda hakan ke bayar da damar kula da kayan da ake jigarsu a cikin Jiragen Ruwa zuwa Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar kuma a kan lokaci,” Inji Dantsoho.
Ya bayyana cewa, Hukumar ta NPA, na gudanar da ayyukanta ne, a zamanance, ba tare da yin amfani da takardun rubutu ba wanda hakan ya taimaka, wajen ragewa Hukumar, yin asara.
Shugaban ya kara da cewa, Hukumar ta NPA, na tabbatar da cewa, ta na ci gaba da kara inganta ayyukanta, inda ya jaddada mahimmancin yin amfani da fasahar zamani domin rage yawan yin dogaro da yin amfani da manyan motocin da ke bin musamman manyan hanyoyin kasar, domin rage fitar da yaki.
Da yake ci gaba da yin tsokaci kan kokarin Hukumar na rage yawan fitar da hayakin na manyan motocin da yeke yin safarar kayan Dantsoho ya sanar da cewa, Hukumar ta ci gaba da kasancewa a gaba wajen gudanar da gangamin ganin an rage yawan hayakin, inda gangamin, ya faro tun daga Tashar Jiragen Ruwa ta Lekki.
“Hukumar ta NPA ta ci gaba da kasancewa a gaba wajen gudanar da gangamin ganin an rage yawan hayakin, inda gangamin, ya faro tun daga Tashar Jiragen Ruwa ta Lekki, “ Inji Dantsoho.
Kazalika, ya bayyana cewa, Hukumar ta kuma himmatu, wajen ganin tana kara zamanantar da ayyuakan da take ci gaba da gudanawar, a daukacin Tashishin Jiragen Ruwa na kasar tare da yin ayyuan, da kayan aiki na zamani, musamman domin a samar da gudanar da yin ayyukan a cikin sauki.
“Wannan babbar Tashar ta Jiragen Ruwa ta Lekki ta hanyar hadaka da NPA da kuma sauran abokan hadaka, da ke a fannin na sufurin Jiragen Ruwa,” Acewar Shugaban.
Shugaban ya ci gaba da cewa, karfin da Tashar ke da shi, ya kai ga har za ta iya tabbatar da gudanar da gasar gudanar da hada-hadar kasuwanci, musamman duba da irin manyan Jiragen Ruwan da ke sauka a Tashar.
“Mun samu damar kaddamarwa da wasu kayan aiki a Tashar ta Lekki ,” Inji Dantsoho.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp