Al’ummomi a sassan Nijeriya na fama da mummunan tasirin ambaliyar ruwa da ta lalata gadaje da hanyoyi, ta hana zirga-zirgar mutane da kaya, tare da haifar da ƙarin wahalhalu ga jama’a. Binciken Jaridar Daily Trust ya gano cewa yawancin waɗannan gadoji da hanyoyi sun daɗewa ba tare da kulawa ko gyara ba kafin su rushe.
Gadar Kufai Ta Filato Ta Rushe
A Jihar Filato, rushewar Gadar Kufai dake kusa da ƙauyen Yelwa a ƙaramar hukumar Shendam ta jefa mazauna yankin cikin halin ƙunci. Gadar, wadda aka gina shekaru fiye da talatin da suka gabata, tana da muhimmanci ga matafiya da masu safarar kaya daga Plateau zuwa jihohin Nasarawa da Taraba, da ma direbobin manyan motoci dake kai kayan abinci zuwa Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
- Sojoji Sun Tarwatsa Wata Haramtacciyar Masana’antar Ƙera Makamai A Filato
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato
Gadar ta fara rushewa a shekarar 2022, sannan aka yi mata ɗan gyaran wucin-gadi a bana. Amma ruwan sama mai ƙarfi ya sake wanke ta a watan Agusta.
Mazauna yankin sun koka cewa gwamnati ta manta da su.
“Rushewar wannan gada na haifar mana da matsala sosai. Gwamnati ta taimaka ta gyara,” in ji Wayu Bamga, mazaunin yankin.
Nanlong Nyas ya ƙara da cewa, “Gyaran da aka yi bai daɗe ba kafin ruwa ya sake lalata gadar.”
Wasu direbobi kamar Umar Sa’adu da Abubakar Haruna sun ce duk lokacin da suka isa wurin gadar, sai sun biya ma’aikata su tura motarsu kafin su iya tsallaka rafi kana su ci gaba da tafiya.
Rushewar Gadar Namne Ta Taraba Ta Tsayar Da Zirga-Zirga
A Jihar Taraba kuwa, Gadar Namne dake kan hanyar Jalingo–Wukari ta rushe a watan Agustan 2024 bayan ruwan sama mai yawa, kuma har yanzu shekara guda bayan haka, babu wani gyara da gwamnatin tarayya ko ta jiha ta fara.
Gadar tana da muhimmanci sosai saboda tana haɗa Arewa maso Gabas da Kudu maso Gabas, Kudu maso Yamma da kuma babban birnin Tarayya (Abuja). Duk da alƙawarin da Gwamna Agbu Kefas, da gwamnatin tarayya da hukumar ci gaban Arewa Maso Gabas (North-East Development Commission (NEDC) suka yi, babu wani aikin gyara da aka fara har yanzu.
A yanzu, matafiya suna amfani da kwale-kwale wajen tsallaka kogin, yayin da ƙananan motoci da babura ne kawai ke iya bin hanyar. Ana kuma cajin matafiya kuɗi don tsallaka kogin.
“Farashin sufuri da kayan masarufi sun tashi saboda doguwar hanya da direbobi ke bi,” in ji wani mazaunin yankin. “Tsallaka rafi da kwale-kwalen kuma na da hatsari, musamman ga waɗanda ba su saba ba.”
Tasirin A ƙasa baki ɗaya
A wasu jihohi kamar Kebbi, da Kogi da Neja, irin wannan ambaliya ta lalata gadoji da hanyoyi, ta katse alaƙa tsakanin ƙauyuka da birane, ta kuma jawo cikas ga harkokin kasuwanci da tattalin arziƙi.
Masana harkokin gine-gine da muhalli sun yi gargaɗi cewa, sai an samar da tsarin ƙasa baki ɗaya na magance ambaliya da kuma yin gadaje da hanyoyi masu jure ruwa, idan ba haka ba, za a ci gaba da fuskantar irin wannan ɓarnar kowace shekara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp