Mutanen Kirawa da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno sun koka kan yadda ƴan Boko Haram ke ci gaba da kai musu hare-hare da ke jawo mutuwa da lalata gidaje da shaguna. A harin da aka kai ranar Litinin da ta gabata, mutane biyu sun rasu, inda aka ƙone fadar dagacin Kirawa da gidaje da shaguna fiye da 50.
Rahotanni sun ce hare-haren sun ƙaru tun bayan da Sojojin Kamaru na rundunar haɗin gwuiwa ta MNJTF suka bar sansaninsu a yankin watanni da suka wuce. Wasu mazauna sun bayyana cewa suna yin barci a Kamaru saboda tsoron kai musu hari, yayin da suke dogaro da tallafin abinci daga gwamnatin Babagana Zulum.
- Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu
- Zulum Ya Tabbatar Da Harin Boko Haram Ya Ci Rayukan Mutane 63
Wani mazauni, Mohammed Abubakar, ya roƙi gwamnati da ta tura Sojoji don dawo da tsaro yakin. Shi ma Baba Kyari Shettima ya gode wa gwamnan bisa tura CJTF da masu farauta, amma ya ce zaman lafiya na dindindin ba zai samu ba sai da Sojoji.
Yayin ziyarar da ya kai Kirawa a ranar Juma’a, Gwamna Zulum ya yi Allah-wadai da sabon harin tare da alƙawarin sake gina asibitin da aka ƙone, zai mayar da shi babban asibiti, da gyaran gidajen da suka lalace, da kuma haƙa rijiyoyi. Ya kuma sake kira ga gwamnatin tarayya da ta tura Sojoji zuwa garuruwan iyaka kamar Kirawa, da Wulgo, da Baga, da Damasak da Malam Fatori.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp