Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta samu nasarar gano wata mota kirar Toyota Hilux da aka sace tare da cafke wata mata da ta yi yunkurin fitar da motar ta kan iyaka zuwa jamhuriyar Nijar.
Kakakin rundunar ‘yansandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce kamen ya biyo bayan wani hadin gwiwa ne da jami’an tsaro na musamman na SIS suka jagoranta.
- Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza
- Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar
Ya ce, “rundunar ‘yansandan ta samu rahoto ne a ranar 29 ga Satumba, 2025, dangane da sace motar kirar Hilux mai lamba GWA 998 AR, wacce aka sace a kan hanyar Ikeja a karamar hukumar Fagge a jihar Kano.
“Jami’an ‘yansanda na SIS, suka fara bincike kan rahoton, ta hanyar amfani da kaifin basira da fasaha, a hanyar filin jirgin sama, karamar hukumar Nassarawa, jihar Kano, jami’an sun kama wata mata mai suna Adama Hassan, ‘yar shekara 35 da ke da zama a karamar hukumar Deba, jihar Gombe, a ranar 6 ga Oktoba, 2025, yayin da take tuka motar da aka sace a kan hanyarta ta zuwa Jamhuriyar Nijar.
Rahotanni sun bayyana cewa, wacce ake zargin ta amsa laifin karbar motar ne daga hannun wani mutumi da ke karamar hukumar Lafiyan Lamurde, jihar Adamawa, wanda a yanzu ake nema ruwa a jallo.