ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Boko Haram Sun Kashe Masunta A Tafkin Chadi

by Muhammad
3 years ago
'Yan

‘Yan ta’addar Boko Haram sun kai hari kan masuntan Nijar, inda suka yi awon gaba da wasu tare da kashe wasu a yankin tafkin Chadi da ke Jamhuriyar Nijar, kamar yadda wata majiya ta bayyana.

‘Yan ta’addar sun yi nasarar kashe masunta da dama daga tsibirin Kwatar Kaoulaha da ke yankin Diffa a ranar Lahadi zuwa Litinin, inda suka yi wa wasu yankan rago tare da yin garkuwa da wasu saboda rashin bin umarnin da aka ba su na barin yankin, kamar yadda masunta suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

  • An Kashe ‘Yan Boko Haram 49 A Sansaninsu 3 Yayin Luguden Wuta Ta Sama
  • Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 6, Sun Kama Wasu A Borno

“An kashe masunta da yawa tare da yin garkuwa da wasu da mayakan Boko Haram masu biyayya ga Baakura Buduma suka yi garkuwa da su saboda sun gaza ficewa daga yankin kamar yadda aka umarce su,” in ji wani masunta, Kallah Sani, yayin da yake magana kan wani shugaban kungiyar Boko Haram na yankin.

ADVERTISEMENT

Sani bai iya bayar da takamaiman adadin wadanda suka mutu ba amma ya ce wadanda suka tsere ba, sun shaida masa masunta da dama suna tsibirin a lokacin da aka kai harin.

Sani yana cikin masunta kimanin 300 da suka yi biyayya ga sanarwar barin aiki na awa daya, inda suka hakura da kama su da sauran dukiyoyinsu ga ‘yan ta’addar.

LABARAI MASU NASABA

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

“Sun gaya mana cewa za su kwashe duk abin da muka mallaka a matsayin ganima tun lokacin da gwamnatinmu ta kama kudadensu,” kamar yadda ya shaida wa AFP.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne kungiyar Boko Haram ta umarci masuntan wadanda galibinsu ‘yan Arewa maso Yammacin Nijeriya ne da su bar yankin su bar dukiyoyinsu a matsayin ganima ga mayakan, in ji wani masunci, Anas Ibrahim.

“Su (Boko Haram) sun zo ne da kwale-kwale masu gudu guda biyu, suka umarce mu da mu bar tsibirin, kada mu dauki komai sai kayan da muke da su,” Ibrahim ya shaida wa AFP.

“Masu tayar da kayar bayan sun dawo ne a ranar Lahadi inda suka kashe wadanda suka samu, tare da lalata kwale-kwalen su na kamun kifi da hana su tserewa,” in ji shi.

Wata majiyar tsaron Nijeriyar ta kuma tabbatar da faruwar lamarin da kuma kashe-kashen, inda ta ce ‘yan ta’addar sun ji haushin yadda Nijar ta kama masu sayar musu da abinci da wani mai safarar kudi.

Gwamnatin Nijar ba ta amsa kiraye-kirayen neman tabbaci ba.

Sai dai wani jami’in yankin Nijar daga yankin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa ‘yan jihadin sun umarci mazauna yankin da su fice daga tsibirin tare da kashe wadanda ba su yi ba.

“Na ga gawawwaki 11 da suka hada da na masunta kuma a cikinsu akwai ‘yan Nijeriya uku, sauran ‘yan Nijar ne,” inji majiyar.

“Sun ce akwai wasu mace-mace a tsibirin.”

Fadin tafkin Chadi mai fadin fadama ya ratsa kan iyakokin Nijeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, kuma masu jihadi sun yi amfani da kananan tsibiran da suke da su a matsayin mafaka.

A shekarar 2014 ne kungiyar Boko Haram ta kwace tsibiran da ke tafkin Chadi bayan munanan hare-hare, lamarin da ya tilastawa masunta tserewa daga gidajensu. Har yanzu dai kungiyar Boko Haram na rike da tsibiran da ke gefen tafkin na Nijar.

A shekarar 2020, kungiyar Islamic State West Africa Province, wacce ta balle daga Boko Haram, ta kwace mafi yawan yankunan da Boko Haram ke iko da su, tare da barin masunta su komen.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Next Post
Nasarar Tsarin CBN Na Samar Da Kudaden Habaka Tattalin Arzikin Nijeriya

Nasarar Tsarin CBN Na Samar Da Kudaden Habaka Tattalin Arzikin Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.