• English
  • Business News
Saturday, October 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani and Sulaiman
1 day ago
Manzon Allah

Alhamdu Lillah. Masu karatu har yanzu dai muna nan a darasinmu da muke bayani abubuwan da wani masanin falsafa ya fada game da Manzon Allah (S.A.W.).

 

Kamar yadda muka fara bayni a makon da ya gabata, Manzon Allah (SAW) ne ya kafa wa duniya tushen wayewar kai. Shi ne wanda ya juya halitta ya kawo mata kyakkyawan canji. Masanin falsafan ya ce Manzon Allah ya kawo canji a cikin addini, ya kawo canji cikin siyasa, da tsarin rayuwa, da tsarin kasa, da tsarin jama’a. Manzon Allah (S.A.W.) Annabi ne, ma’aiki ne daga Allah, Annabi ne, ma’ana malami ne wanda ya yi karatu a Hadarar Allah. Wannan ya sa duk yadda mutum yake takama da ilimi, idan ya yi nazarin na Manzon Allah (SAW) sai ya ga inda aka wuce tunaninsa.

  • Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma
  • Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura

Akwai wani bawan Allah, ya yi littafi ya kai wa Shehul Abul Fat’hi ya sa hannu, mutumin kasar Sudan ne ko Chadi (abin ya dan shige min), da Shehu ya karanta tun daga farko har karshe sai Shehu ya sa hannu ya soke littafin ya ce bai yi ba, mutumin ya ce yanzu wannan littafi bai yi ba? Shehu ya ce eh bai yi ba, ya ce duk wannan tarin ilimi da ke ciki? Shehu ya ce kwarai kuwa an sa ilimi amma bai yi ba saboda har ka yi ka gama ban ji ka ce kur’ani ya ce kaza ba, ban ji ka ce Manzon Allah ya ce kaza ba, saboda duk wata nukuda da ka sani sai da kur’ani ya zo da shi, ma’ana kai iliminka ba ya cikin Alkur’ani kenan? To wannan shi ne gaskiya.

 

LABARAI MASU NASABA

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

Saboda haka mu saki ilimi, mu ba ilimi hanya kar mu ji tsoro, mu je mu nemo shi duk inda yake kayanmu ne. Manzon Allah ya ce “ilimi hikima ce kayan mumini ne, saboda haka kar ka ji tsoro, ba wanda ya fi karfin Allah, ba wanda ya fi karfin Manzon Allah (S.A.W.). saboda haka ba wanda zai je ya shiga halwa ko ya shiga wani tunani ko ya shiga kaza har ya zo “summa dana fatadalla”, ba wanda zai zo nan sai dai Manzon Allah (S.A.W.). Dan haka Sufaye ba sa jin tsoron ko waye zai yi maganar ilimi, ba sa jin tsoron ko wane littafi bare damuwa, haka kuma ba a iya kada su, saboda duk abin da aka fada a gabansu ka ke suna kallonka, saboda suna da ilimi babba shi ne Manzon Allah (S.A.W.).

Wannan masani na falsafa ya ci gaba da cewa, Manzon Allah Ya canza halitta duka ta wajen addini, ta wajen siyasa, ya ce manzon Allah ma’aiki ne, annabi ne amma ya tsinci kanshi kuma a matsayin shugaban kasa, kuma dole a tafi a haka, tunda ya yi hijira ya zo Madina, akwai Sarkin Madina, akwai Shugaban Madina (wasu suna cewa Abdullahi bin Ubayyu bin Salul), tun da Manzon Allah suka zo Madina suka watsar da zancen sarautarsu, duk almajiran Manzon Allah suka zamanto a wajensa suke karbar addini kuma yanzu wajensa suke karbar dukkan siyasar duniya.

Shehu Ibrahim, ya ce manzon Allah ya rike mukamai tara a zamaninsa, ko wane mukami idan aka ba mutum a wannan zamani ya ishe shi, Annabi shi ne ministan tsaro na zamaninsa, shi ne kwamandan yaki a zamaninsa, shi ne ministan lafiya na zamaninsa shi ne ministan kasuwanci na zamaninsa, shi ne ministan shirya gari, da zana gidaje, da tsara gari, shi ne ministan tsaro na zamaninsa, haka yake rangadi yana kewaya gari, yana tsaron gari duka ibada ce.

Wata rana an ji wani ihu a Madinah, Sahabbai suka rufe kunnuwansu suna zaton ko an kawo masu hari ne, suka fito suna cewa a bi a hankali kada su tashi Annabi, suka tafi a hanya sai suka tarar Manzon Allah har ya dawo a kan dokin [alha (Manzon Allah ya ga dokin [alha a daure ya kwance ya hau), shi har ya je ya dawo daga wajen da suka ji ihun shi shi kadai, da Manzon Allah ya gan su sai ya ce kada ku ji tsoro, har yake ce wa Dalha wannan doki naka akwai gudu, ka ga dai an yi tafiya mai nisa kenan ko ina ya je? Babu wanda ya sani. Kewayen gari da tsaron gari duk ibada ce, manzon Allah yake yi shi kadai.

Sayyidina Umar, (A.S) sai da ya hau sarauta yake cewa mutum in ba Manzon Allah ba wa zai iya rike wadannan mukamai, Sayyidina Umar ya kakkafa ministoci daban-daban, ministan shari`a daban, ministan waye daban, kuma ya kyauta wanda duk tsarin duniya a kan shi ake yanzu, a da kuma a jikin Manzon Allah yake shi kadai (S.A.W).

Manzon Allah (S.A.W.) ya kawo canji a siyasa, saboda me? saboda shi ne ya kawo ‘yanci, da ‘yancin fadar ra’ayi, da zaman tare, da ‘yancin karbar juna. Sannan Manzon Allah ya kawo ‘yancin zaman jama’a ba tare da zalunci ba, ba mai karfi ya cuci mara karfi, ba namiji ya cuci mace ko ya wulakanta ta kowa wajen hakki dai-dai yake da kowa. Manzon Allah duk ya kawo canji a wannan. Ya jefar da bauta, ya kawo yadda za a ‘yanta bayi.

Shi wannan Bafalsafe da ya fadi wannan ya san abin da ya fadi ya san me ya fada kwarai da gaske, Manzon Allah ya canza duniya, ya kawo canji a cikin addini ya kawo canji a wajen siyasa ya kuma kawo canji a wajen zaman tare, ya kara da cewa Manzon Allah ya canza tarihin halitta. Daga zamanin Manzon Allaha tarihi ya soma ci gaba, ya rika budawa har ya zo wannan zamani da muke ciki,.

Manzon Allah ya shirya (kyakkyawan tsari) ma wannan zamani gabadaya, kuma gaskiya ne, tunda manzon Allah (S.A.W.) shi ya fara kafa birni da duk abin da birni yake nema, kuma Allah ya nuna masa duk wanda ya mayar da kansa kauye ko ya mai da garinsa kauye Manzon Allah ya yi maganinsa. A nan ba ana nufin kauye mai gida daya ba, ana nufin wayewa ta birnintaka. Duk wanda zai tsaya ma wani radayin rikau, wand ba ra’ayin ci gaba ba ne ya ce muna nan ba wanda ya isa ya ya canza mu, wannan ya zama dan kauye kenan. Su (‘yan kauye ne) kan ce ba wanda ya isa ya canza su.

Gari daya Allah ya yarda ya yi ta zama kauye har abada, shi ne Makka, ita kadai ce Allah Ya yarda mata, Allah Ya sanya mata suna Ummul-Kura, (Uwar kauyuka), it akadai ce Allah ya yadda ta zama a haka, saboda dakin Allah ya yi ta zama haka har tashin kiyama ba wanda ya isa ya canza wannan. In ka lura ita ma da aka yadda a yi haka idan za mu shiga sai mun cire kayanmu mun sa harami, nan ne kadai Allah ya yadda ya zama kauye da ba zamu shiga da kowane kaya ba sai mun cire, shi ne iykokin da mikati, idan an zo sai an yi niyyar shiga wajen. Manzon Allah (S.A.W.) ya canza rayuwar dan Adam ya kafa rayuwa, ya kafa harsashin duk wani birni, ya kafa harsashin wayewa, ya kafa harsashin ilimi da karatu, shi ne ya kafa harsashin komai, a kan wannan harsashi ake ci gaba da tafiya har yanzu a duniya.

Manzon Allah (S.A.W.) ya samar da wasikatul Madina ,wanda mu muke cewa (constitution), Manzon Allah ne ya fara samar da shi, duk da cewa ga Alkur’ani ga komai, amma kuma ai wannan kur’ani na Annabi ne da mabiyansa kadai, to ya za a yi da sauran jama’ar gari da a cikinsu akwai Yahudawa da ba ruwan su da Alkur`ani suna da tasu Attaura, akwai Nasara da ba ruwan su da Alkur’ani suna da tasu Injila, haka nan akwai wadanda ba da kowane littafi suke aiki ba, akwai kuma wadanda sun nuna suna tare da Annabi a sarari amma a boye ba sa tare da shi. Manzon Allah sai ya ce a yi zaman kasa mana, a zauna lafiya kowa ya zauna da ra’ayinsa, amma dan mu kare kasarmu duk abin da ya taso wa Madina duk dan Madina (yana da hakkin kasa a matsayin) dan Madina, kowa yana da ra’ayin addini da ra’ayin kasuwanci, yana da ra’ayin komai.

Manzon Allah (S.A.W.) ya tabbatar da batutuwa wajen guda tara, kowace kasa ta tabbatar da wadanna babu shakka za ta zauna lafiya. Amma yanzu da za mu dage mu ce mu maganar addini za mu bi, za mu bi maganar shari’a a aiwatar da ita a kan wadanda ba mu ba, kuma duk wanda ba na addininmu a halaka shi (a uzu billahi) wannan ya saba da ka’idar zaman tare da Manzon Allah ya kafa. Kuma ko a addinin namu ma, wani sashe yana ce wa wani sashe kai ba firkatun najiya ba ne, kai ba ka cikin jama’a da za su tsira, kana daga cikin guda saba’in da biyu (72) da ba su tsira ba, ‘yan wuta ne. Amma idan aka samu wani abin da ya kare mu, wanda ya tsare mu, wanda yake rike da mu to sai kowa ya yi addininsa a saukake. Duk wanna magana tana nan a cikin Alkur’ani, amma wanda ya karanta shi a baibai, ko ya ki yin amfani da shi a baibai, shi kuma dole “Constitution” ya yi maganinsa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)
Dausayin Musulunci

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)

October 10, 2025
Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi
Dausayin Musulunci

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

October 3, 2025
Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)
Dausayin Musulunci

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

September 26, 2025
Next Post
Shettima

‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci - Shettima 

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

October 18, 2025
Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

October 18, 2025
Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

October 18, 2025
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

October 18, 2025
Radda

Gwamnan Katsina Ya Bukaci Al’umma Su Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro

October 18, 2025
Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi

Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi

October 18, 2025
IMF

Fitar Da Kudi Ta Haramtacciyar Hanya Na Kara Dagula Matsalar Tattalin Arziki – IMF

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.