Wannan Jaridar a watan Yunin wannan shekarar muka wallafa sharhi na daga Teburin Edita kan bukatar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, da ya bibiyi batun shari’ar ‘yan yankin Ogoni su hudu.
A nan za mu iya cewa, Shugaba Tinubu, ya saurari kiran namu kuma muna gode masa kan yadda ya yi amfani da karfin ikon da kudin tsarin mulkin kasar ya bashi na yiwa ‘yan Ogonin hudu, afuwa.
A nan za mu iya cewa, jin kiran namu da Shugaban ya yi, wani abu ne, da ke nuna cewa, Shugaban mai sauraron kira ne.
Kazalika, matsin lambar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya fuskanta daga bangaren kungiyoyin kare rajin ‘yan Adam kan batun lafiyar, hakan ya bude wani sabon babi, kan iftila’in da ya aukawa ‘yan yankin na Ogoni, shekaeru 30 da suka gaba wato a shakarar 1994.
A jawabin da ya yiwa ‘yan kasa na zagoyowar ranar ci gaba da dorewar mulkin Dimokiradiyya da aka mayar zuwa June 12, Tinubu ya bayyana yin yafiya ga ‘yan Ogoni su tara, wadanda suka hada da, ‘yan gwagwarmaya na yankin da kuma jagoran kungiyar dorewar alummar yankin Ogoni, MOSOP, Ken Saro-Wiwa, tare da kuma sauran mutane takwas, da suka hada da, Saturday Dobee, Nordu Eawo, Daniel Gbooko, Paul Lebera, Felid Nuate, Baribor Bera, Barinem Kiobel, da kuma John Kpuine.
Baya ga yi masu afuwa, Shuagaba Tinubu, ya kuma karama su da lambar yabo ta kasa.
‘Yan Ogonin su tara, sun dai fuskanci shari’a ne, bisa zarginsu da kitsa kisan sarakunan Ogoni Albert Badey, Edward Kobani, Theophilus Orage da kuma Samuel Orage.
Kotu ta tuhumi ‘yan Ogonin su tara, ta kuma yanke masu hukuncin rataya a ranar 10 ga watan Numambar 1995.
Hukucin na Kotun, a wancan lokacin, ya haifar da hatsaniya tare da yin suka daga bangaren manyan shugabannin kasasshen duniya, daidaikun mutane da sauran kungiyoyi, musaman duba da cewa, an yanke masu hukuncin ne, a lokacin da ‘yan kasar ke nuna tsanar mulkin soji, biyo bayan soke zaben shugaban kasa, da ake da yakinin an yi sahihin zabe ne.
Sai dai, masu sharhi a fagaen siyasa na ganin Tinubu ya yi masu wannan afuwar ce, da wata manufa, musamman ganin yadda afuwar ta kasance, tare da karrama su da lambar yabo ta kasa.
Amma idan aka yi dubi da yunkurin da Tinubu ke ci gaba da yi na tabbatar da sasanci a daukacin mazauna yankunan kasar komai kankancin da yanki yake dashi, musamman wadanda suka ganin, an mayar da shu, Saniyar ware, ko kuma an manta da su, wannan kokarin na sa na son hada kan kasar, hakan ya zama wajibi, suma ‘yan Oginin hudu, hakan ya sa Tinubu, ya sanya ‘yan Ogoni hudu, a cikin jeren wadanda aka yiwa afuwar
Domin idan har ba sanya su cikin jeren wadanda suka suka ci wannan gajiyar ta afuwar ba, hakan zai zama tamkar an yi tuya ne, an manta da Albasa, inda yin wannan afuwar, za ta kara tabbatar da zaman lafiya mai dorewa, a yankin.
Wannan Jaridar na goyon bayan duk wani abu, da ya shafi yin adalci da kuma bai wa, kowanne bangaren na kasar hakkainsa.
A saboda hakan, muna jinjinawa Shugaba Tinubu kan yin wannan afuwar ga ‘yan Oginin su hud, wanda wannan matakin ya bude wani sabon babain tarihi ga turbar makomar mulkin Dimokiradiyyar kasar.
Alal misali, a lokacin tsohuwar gwamnatin mulkin soji ta Janar Yakubu Gowon mai murabus, bayan karshen yakin basa na shekarar 1970, ya yi wadanda suka taka muhimmiyar raywa a yakin afuwa.
Bugu da kari, a lokacin tshowar gwamnatin farar hula ta marigayi tsohon Shugaban kasa Shehu Shagari, ya yiwa Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, afuwa ya kuma rufe kundinsa na aikata jan ragamar yakin basasan, wanda hakan ya sa samu damar dawo cikin kasar bayan barin kasar domin neman mafakar siyasa.
Batun na Ogoni wani abu ne da za a iya cewa, cike yake da nuna karfin kwanji a tsakanin wasu manyan masu fada aji, a yankin, inda matsalar ta kuma haifar kusan kawo karshen rayuwar manyan jiga-jigan da ke a yankin, musamman ganin yadda wasu mayan yankin, a wancan lokacin, suka rinka karkatar da dimbin arzikin, da ya kamata mazauna yankin, su mafana da su, musamman wajen magance dagwalon danyen mai da ke lalata muhalli a yankin.
Tataburzar wadda ta auku a lokacin tsohuwar gwamnatin mulkin siji ta marigayi Janar Sani Abacha, ta samu nasarar cin lagon ‘yan yankin da suka yi uwa suka kuma yi makarbiya wajen siyasantar da batun.
Wasu masu kare muradun siyasa a wancan lokacin, sun alakanta kisan da gwamnatin Abacha ta yiwa ‘yan Ogoni su tara, a matsayin abinda ya sabawa mulkin Dimokiradiyya.
Koma dai menene, daukacin batun ya bayyana a zahiri, irin kalubalen da yankin ke fuskanta a wancan lokacin, na gurbacewar muhalli a yankin.
Sharhin wannan Jaridar kan batun, ba wai wata manufa ce, ta dora laifin kan wani bangare ba, domin kuwa an yi rubuce-rubuce da dama na goyon baya da kuma na yin suka, domin a yanzu, duk wani yunkuri na nuna jayya hakan zai iya zama, tamkar fama wani Gyambo ne.
A nan, muna kira ga Shugaba Tinubu da kai daukin tallafawa rayuwar wadanan ‘yan Ogonin hudu, domin kuwa afuwar da kuma bayar da lambar karramar ga ‘yan Ogonin tara, ba su wadatar ba, ganin cewa, sauran hudu da ba a sanya su a cikin ba, hakan zai iya ci gaba da jefa tamtama.
Suma ‘yan Oginin hudu, ‘yan Nijeriya ne, kamar kowa duba da yadda suka sadaukar da rayukansu, domin dorewar yankinsu
Har dai zuwa yau, ba a iya gano gawarwakin ‘yan Ogonin tar aba, inda su kuma ‘yan Ognin hudu suka rasa na su rayukan a cikin wani irin yanayi.
A bisa wadannan dalilan, muna sake nanata kiran mu da tattausar murya ga Shugaba Tinubu da sake yin bibiya kan batun na ‘yan Ogoni hudu, musamman domin tabbatarda zaman lafiya mai dorewa a yankin.