• English
  • Business News
Saturday, October 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari

by El-Zaharadeen Umar and Sulaiman
22 hours ago
masari

Shugaban kwamitin gudanarwa na hukumar tallafa wa manyan makarantun gaba Sakandire TETFUND, kuma tsohon gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello ya jagoranci wani taro na masu ruwa da tsaki akan sha’anin harkokin ilimin a Nijeriya.

Taron dai na da nufin gayyato masana da masu ruwa da tsaki akan sha’anin manyan makarantun gaba sakandire domin su fahimci ayyukan hukumar Sannan su bada gudunmawa da shawara ta yadda za a kara inganta ayyukan hukumar

An gudanar da taron a karo na farko inda masana da kungiyoyin farar hula da ‘yan jaridu da kungiyoyin Malaman jami’o’i da jami’an gwamnati da ‘yan majalisa suka halarta, wanda kuma ya gudanar A Class and Ebent Center, Ibrahim Ibrahim Way, Wuse II, Abuja

Bayan kammala taron wakilanmu El-Zaharadeen Umar ya tattauna da shugaban hukumar gudanarwa na asusun tallafawa manyan makarantun gaba da Sakandire TETFUND tsohon gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari domin Dalili shirya irin wannan taro da kuma manufar da ake san cimmawa.

Ga yadda tattaunawar ta kasance.

LABARAI MASU NASABA

Abba Ya Dace Ya Zama Gwamnan Kano Na Har Abada Ba Shekaru 8 Kaɗai Ba – Arch Ali Hassan

Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida – Yahaya Yakubu

 

Shin menene makasudin shirya irin wannan taro na masu ruwa da tsaki akan sha’anin ilimi da aka gudanar a yau?

Makasudin wannan taro shi ne a fadakar da mutane ayyukan wannan hukuma ta TETFUND da take yi, sannan kuma a yi magana da wadanda suka fi amfana da shi wannan tsari na TETFUND. Kamar jami’ai da makarantu da kuma dalibai sannan kuma a karbi shawarwari ga jama’a akan yadda za a bunkasa wannan aikin na hukumar tallafawa manyan makarantu na gaba da Sakandire a Nijeriya.

Wannan shi ne makasudi kuma na farko da ake san a jawo al’umma a ciki su dan abinda ake yi da yadda ake kashe kudaden da kuma yadda ake tarawa da makasudin tara su da makarantun da ake ba kudaden da kuma su makarantu yadda suke amfani da kudin

 

Shin kamar bangarori nawa ne suka halarci wannan taro na masu ruwa da tsaki a wannan hukuma ta asusun TETFUND?

Aminu Bello Masari: Na farko akwai bangarorin makarantu da Dalibai da ‘yan jarida da masu bukata ta musamman da kungiyoyin Malaman jami’o’i wata ASUU da da COUSU da duk masu ruwa da tsaki akan harkar ilmin gaba da Sakandire da kungiyoyin farar hula duk sun halarci wannan taro, bayan jami’an gwamnati wadanda suka zo daga fanni-fanni da tsofaffin shugabanni da majalisar tarayya da suke da hakkin kudaden da ake kashewa baki daya.

 

Jama’a da dama sun yi magana akan zama wasu sun mika kokon barar su akan ilmin gaba da Sakandire wani mataki zaku dauka a kan haka?

Daman ma’anar wancan zama shi ne domin a samu karin shawarwari daga al’umma da masana ta yadda za a cigaba da lissafin kasafin kudi na shekarar 2026, samun wadannan shawarwari za mu zauna mu kalle su, mu duba wadanda za su iya yiyuwa bana, wasu kuma sai an tura gaba, amma dai za a yi wani abu akan shawarwarin da aka samu insha’Allahu.

 

Masu bukata ta musamman sun samu wakilci kuma har sun mika bukatun su, me zaka ce game da haka?

To, na farko dai su masu bukata ta musamman darkatan da ke kula da gine-gine ya ce to yanzu dole ne duk ginin da za a yi dai an tabbatar da yana da tsari na kula da masu bukata ta musamman. Kuma sun kawo bukatar suna san a yi masu wani gurbi a ofishin shi sakatare na hukumar tallafawa manyan makarantun gaba da Sakandire, wannan kuma wani abu ne da sai mun zauna wajen taro zamu kalli abubuwan sannan abinda ke yiyuwa kuma shi za a yi.

 

A takaice me kake son cimmawa na ganin an ciyar da wannan hukuma ta TETFUND gaba?

Ai babban al’amari shi ne, a sanya mutane a cikin hidimar su san abinda ake yi, kuma su ba da shawarwari yadda za a kara bunkasa abin da ita wannan ma’aikata take yi, kudi ake amsa masu yawa kuma wajibi ne a gayawa jama’a yadda ake sarrafa wadannan kudaden a dukkan jami’o’in gwamnatin tarayya kusan 250 banda kwalejojin da sauran su ba wanda bai amfana da wadannan kudadai duk shekara.

 

Zuwa yanzu an kashe nawa a wannan hukuma mai tallafa wa manyan makarantun gaba da Sakandire a Nijeriya?

Yanzu abin da za mu iya cewa shi ne mun yi kasafin kudi, wanda zuwa yanzu an baiwa su makarantun daunin su na kaso hamsin (%50) bisa dari wanda yanzu lissafin da aka yi ya wuce biliyan 500 wanda aka ba su Makarantun a hannun su, to kuma za su kawo yadda za su kashe kudaden, sannan sauran an yi aikin lafiya da su wanda yanzu haka an fada a wajen taron da kuma aikin wuta da aikin tsaro duk wadannan wurare ne da aka sanya kudi da ayyuka na musamman.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnan Abba Kabir Yusuf tare da Arch. Ali Hassan
Tattaunawa

Abba Ya Dace Ya Zama Gwamnan Kano Na Har Abada Ba Shekaru 8 Kaɗai Ba – Arch Ali Hassan

June 23, 2025
Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida – Yahaya Yakubu
Tattaunawa

Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida – Yahaya Yakubu

May 24, 2025
Ma’aikatar Kasuwanci Da Zuba Jari Ta Gudanar Da Bikin Makon Abokan Cinikayya
Tattaunawa

Ma’aikatar Kasuwanci Da Zuba Jari Ta Gudanar Da Bikin Makon Abokan Cinikayya

October 18, 2024
Next Post
Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

October 18, 2025
Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025
Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka

October 18, 2025
JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i

JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

October 18, 2025
Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

October 18, 2025
Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.