Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Remi Tinubu, ta ƙaddamar da ɗakin karatu na zamani na E-learning a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Uwargidan gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ce, ta wakilci Sanata Remi Tinubu a wajen taron.
- An Kammala Taron JKS Inda Aka Amince Da Shawarwari Kan Shirin Ci Gaban Kasar Sin Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 15
- Gwamna Abba Ya Jaddada Mubaya’arsa Ga Kwankwaso
Ta yaba da wannan shiri na ilimin zamani da Gwamnatin Tarayya ta kawo, inda ta ce zai taimaka wajen bunƙasa ci gaban ƙasa baki ɗaya.
Hajiya Huriyya ta ce wannan ɗakin karatu na zamani na E-learning na daga cikin waɗanda aka kafa a jihohi 10 a ƙasar nan, ƙarƙashin shirin Renewed Hope Initiative tare da haɗin gwiwar Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA).
Ta bayyana cewa, shirin ba wai game da fasaha kawai ba ne, yana nufin ƙarfafa matasa da buɗe musu sabbin hanyoyin ilimi da ƙirƙire-ƙirƙire a Jihar Zamfara da ƙasar baki ɗaya.
Ta ce, ta hanyar wannan E-library, ɗalibai, malamai da masu bincike za su samu damar amfani da bayanai da ilimin zamani cikin sauƙi.
A cewarta, Renewed Hope Initiative wanda Sanata Oluremi Tinubu ke jagoranta, na da manufar tallafa wa ilimi, ƙirƙire-ƙirƙire da ci gaban al’umma.
Wannan ɗakin karatu, in ji ta, alamar hangen nesan uwargidan shugaban ƙasa ne wajen inganta ilimi a Nijeriya.
Ta gode wa ma’aikatar sadarwa, ƙirƙire-ƙirƙire da tattalin arziƙin zamani, da kuma NITDA, saboda yadda suka aiwatar da aikin cikin nasara.
Ta kuma yaba wa mijinta, Gwamna Dauda Lawal, bisa jajircewarsa wajen kawo ci gaba a ɓangaren ilimi a Zamfara.
A nasa jawabin, Daraktan NITDA, Kashifu Inuwa, ya buƙaci ɗalibai da malamai a Zamfara da su yi amfani da wannan ɗakin karatu yadda ya kamata domin amfaninsu.
Shi ma Kwamishinan Ilimi na Kimiyya da Fasaha, Mallam Wadatau Madawaki, wanda Sakatariyar Dindindin Maryam Shantali ta wakilta, ya ce aikin ya yi daidai da manufofin Gwamna Dauda Lawal wanda tun zuwansa mulki ya bai wa ilimi fifiko.
Ta ƙara da cewa, a madadin ma’aikatar ilimi da al’ummar Zamfara, suna godiya ga Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, saboda kawo wannan shiri mai amfani.
Ta tabbatar da cewa ɗalibai, malamai, da masu bincike za su yi amfani da wannan ɗakin karatu yadda ya dace domin amfanin ilimi a jihar.













