Sojojin Operation Haɗin Kai sun daƙile wasu hare-haren ‘yan ta’adda a jihohin Borno da Yobe da safiyar Alhamis, 23 ga watan Oktoba, 2025.
Mai magana da yawun rundunar, Kanal Sani Uba, ya ce ‘yan ta’addan sun kai hare-hare kan sansanonin sojoji a Dikwa, Mafa, Gajibo, da Katarko tsakanin ƙarfe 12 na dare zuwa 4 na safe.
- Me Ake Fatan Gani A Shirin Sin Na Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar Na Gaba
- Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara
Ya bayyana cewa sojojin sun yi ƙwazo, tare da taimakon sojin sama, sun kashe sama da ‘yan ta’adda 50, inda sauran suka tsere.
Sojojin sun kuma ƙwato bindigogi AK-47 guda 38, manyan bindigogi guda bakwai, RPG guda biyar, da harsasai masu yawa.
Aƙalla ‘yan ta’adda 70 ne suka ji rauni.
Wasu daga cikin sojojin sun ji rauni amma suna cikin ƙoshin lafiya.
Haka kuma, wasu gine-gine da motocin da ke kusa sansaninin sun lalace yayin artabun.
Rundunar sojin ta yaba da jarumtar dakarunta, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare ƙasar daga duk wata barazana.













