Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya naɗa babban yayansa, Alhaji Adamu Mohammed, a matsayin sabon Sarkin masarautar Duguri.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Aminu Hammayo ne, ya miƙa takardar naɗin sarautar ga sabon sarkin a wani biki da aka gudanar a fadar masarautar Duguri da ke ƙaramar hukumar Alkaleri.
- Gombe Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Rano Air Don Fara Jigila Tsakanin Abuja Zuwa Gombe
- Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi
Hammayo, ya buƙaci sabon sarkin da ya ci gaba da mara wa manufofi da shirye-shiryen gwamnati baya, tare da tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’umma.
A nasa jawabin, sabon Sarkin Duguri ya gode wa Gwamna Bala Mohammed bisa wannan karramawa, inda ya yi alƙawarin zama mai biyayya ga gwamnatin jihar da kuma masarautar Bauchi.
Haka kuma, an naɗa Alhaji Jibrin D. Hassan a matsayin sabon Sarkin masarautar Bununu, inda shi ma ya karɓi takardar naɗin daga hannun Sakataren Gwamnatin Jihar.
Hammayo ya shawarce shi da ya gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci tare da haɗa kan ƙabilu don tabbatar da zaman lafiya.
A baya-bayan nan ne Gwamna Bala Mohammed ya rattaba hannu kan dokar kafa sabbin masarautu 13 a jihar.












