Majalisar Dokokin Jihar Kano ta zargi Hukumar Kwastam ta Ƙasa (NCS) da nuna son kai ga jihohin Kudu a sabon tsarin ɗaukar ma’aikata.
A zaman majalisar da aka yi ranar Laraba, Jagoran Majalisa, Hon. Lawan Hussaini Dala, ya ce tsarin ɗaukar ma’aikatan ya karya ƙa’idar ɗaukar aiki ta Gwamnatin Tarayya wadda aka kafa domin tabbatar da adalci da daidaito a Nijeriya.
- Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik
- Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump
“Wannan tsarin ɗaukar ma’aikata bai da adalci. Ƙa’idar da aka tsara domin raba damarmaki daidai ba a bi ta ba,” in ji Dala.
Ya bayyana cewa daga cikin mutum 1,785 da aka ɗauka, jihohin Kudu maso Yamma sun fi kowa samun gurabe, inda Legas ta samu mutum 207, yayin da dukkanin yankin Arewa maso Yamma gaba ɗaya ya samu kusan kashi 7 kacal.
Dala ya gargaɗi cewa irin wannan rashin daidaito zai iya sa Hukumar Kwastam ta zama mallakin yanki ɗaya idan ba a gyara ba.
“Muna kira ga hukumar da sauran hukumomi su tabbatar da adalci da daidaito a lokacin ɗaukar ma’aikata na gwamnatin tarayya,” in ji shi.
Shugaban Majalisar ya yaba wa Dala bisa kishin ƙasa da ya nuna, sannan ya umarci kwamitin majalisar da ya binciki lamarin tare da gabatar da rahoto domin ɗaukar mataki.














