Sojojin Rundunar 6 ta Nijeriya, ƙarƙashin Operation Lafiya Nakowa, sun ceto wani mutum da aka sace mai suna Alhaji Ali Adamu a ƙaramar hukumar Lau ta Jihar Taraba.
A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar sojin, Laftanar Umar Muhammad, ya fitar, an ceto mutumin ne a ranar 29 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun kiran gaggawa cewa an sace shi a gidansa.
- Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II
- Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU
“Sojoji sun hanzarta bi bayan masu garkuwa da mutanen, kuma da suka fahimci cewa sojojin suna gab da kama su, sai suka bar wanda suka sace suka tsere zuwa cikin daji,” in ji sanarwar.
Rundunar ta tabbatar da cewa an dawo da wanda aka sace cikin ƙoshin lafiya ba tare da an biya kuɗin fansa ba.
A wani lamari kuma, ‘yan sa-kai da mafarauta sun kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne, mai suna Mista Lalau Adamu, mai shekaru 30, a yankin Maraban Kunini da safiyar ranar Laraba.
Ana zargin mutumin da hannu wajen sace Alhaji Adamu.
Wanda ake zargin ya samu raunuka bayan jama’a sun yi masa duka kafin isowar sojoji, kuma an garzaya da shi asibiti, yayin da ake ci gaba da bincike.
Brigedi Janar Kingsley Chidiebere Uwa, kwamandan Rundunar 6, ya yaba da yadda sojoji, ‘yan sa-kai da mafarauta suka haɗa kai, yana mai cewa wannan haɗin kai ya taimaka wajen samun nasarar ceto wanda aka sace.
Ya kuma buƙaci jama’ar Taraba su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai da wuri domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.














